1

Wasu Sanannun Zumɓutan Doron ƙasa 8 da Muhimman Bayanai Game da Su


Zumɓutan Doron ƙasa, wanda aka fi sani da Peninsula, wani sashe ne na nahiyoyin da muke rayuwa a kan su amma yana da wata siffa ta daban ba kamar yadda sauran ƙasashe suke ba.

Wasu sukan ƙira shi da tsibiri, wato wani yanki ne da yake kusan kewaye da babban ruwa da ake ƙira teku amma ba duka ba, saboda yana ɗan liƙe ne da wata babbar nahiya saboda haka ne ma masana yanayi na binciken na ƙarƙashin kasa suke ƙiran sa “rabin tsibiri” wato half island.

Karanta: Bayani A Kan Farantan Duniya – ‘Tectonic Plates’

Sannan shi wannan rabin tsibirin ba wai ainihin tsibiri ba ne kamar yadda muka ambata a baya, shi wannan yana ɗan haɗe ne da uwar nahiya. Ke nan yana da bambanci da asalin tsibiri da yake cikin teku tsamo-tsamo

Taswirar tsibirin Iberia

Saboda kasantuwar ruwa da tekuna a duniyar Earth ne tsibiri ya kasantu, amma a wasu duniyoyin da babu ruwa, kawai tsaunuka ake iya samu. A wannan rubutun za a iya ganin wasu sananun tsibirai kamar haka:

1. Arabian Peninsula –wanda shi wannan sashi ake kira da gabas ta tsakiya ya kuma had’a kasashe a qalla guda goma.

2. Indian Subcontinent –ya ƙunshi ilahirin ƙasar India ne a yanzun, sannan sashinsa yana cikin teku na uku mafi girma a duniya wato tekun India. Daga kudancinsa ya yi iyaka da tsibirin kasar Sri Lanka wanda wani mashigar ruwa ya raba su.

3. Iberian Peninsula –shi kuma wannan ya ƙunshi tsohuwarr daular Al-Andalus ne wacce yanzu ake ƙira ƙasar Spain da Portuga. Shi wannan zumɓutun yana cikin tekun Atlantic ne kuma ya yi iyaka da nahiyar Afrika daga kudancinsa.

4. Scandinavian Peninsula –wanda yake zaune a mafi maƙurar arewacin duniya wato –Northern Hemisphere, kuma sashi ne na nahiyar Europe wanda ya haɗa ƙasashe da dama kamar su; Norway, da Sweden da Denmark. Tsibirin Scandinavian yana kewaye da wasu dashi na tekunan Norwegian, da Baltic da North Sea waɗanda suke arewacin nahiyar Europe.

5. Yucatan Peninsula –yana arewacin nahiyar America wanda a yanzu ƙasar Mexico take zaune a wajen. Sannan shi kuma wannan tsibirin ya kasance dashi na yankin Caribbean ne.

6. Indochinese Peninsula –yana nahiyar Asia ta kudu maso gabas da ya ƙunshi ƙasashen Vietnam, da Burma, da Thailand, da Cambodia da sauransu.

7. Lizard Peninsula –wanda yake zaune a jikin tsibirin Great Britain wanda ya zamo wani dashi na ƙasar England yanzu.

8. Monte Argentario –wannan shi kuma yana ɓangaren ƙasar Italy ne a yanzu a cikin jelar tekun Atlantic da ake ƙira Mediterranean Sea

Wadannan suna kaɗan daga cikin zunɓutan doron ƙasa wadanda aka fi sani da tsibirai –peninsulas da suke a duniyar Earth.

Madogara

[1] Wikipedia.org

[2] Encyclopedia of Geography

[3] National Geographic

Abdullahi Abubakar

Abdullahi Abubakar

I'm Abdullahi Abubakar from bajoga, gombe state. A former student in geography dept from fce,kano

One Comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *