1

Jerin Nau’ukan Dabbobi 8 Da Suka Halaka Dubunnan Shekaru Da Suka Gabata

Dabbar dinosaur

Dabbobi da dama sun halaka dubunnai ko miliyoyin shekaru da suka gabata a baya, wasu sanadiyyar samun canje-canjen yanayi ko kuma yanayin canjin zubin halitta.

Daga cikin waɗannan dabbobin akwai dinosaurs, waɗansu irin dabbobi masu kama da ƙadangare da suka rayu shekaru miliyan 65 da suka gabata.  Masana suka ce iftila’in dutsen asteroid ne ya afka musu, wanda hakan ne yayi sanadiyyar halakarsu.

1. Dinosaurs

Masana suka ce waɗannan dabbobi sun shafe aƙalla shekaru miliyan 245 suna rayuwa kafin wannan iftila’i ya yi sanadiyyar halakar yawancin nau’ukansu, sannan daga lokacin halakar ta su zuwa yanzu kuma ya kai shekaru miliyan 66.

Wasu Abubuwa Dangane Da Su:

  • Sun rayu tsawon shekaru miliyan 245 a duniyar Earth
  • A shekarar 1842 wani masanin kimiyyar halittu da ake ƙira Sir Richard Owen ya samar da wannan suna daga lalmar Greek deinos wacce ke nufin “tsoro” da kuma sauros wacce ke nufin “ƙadangare”
  • Akwai aƙalla nau’ukan waɗannan dabbobi 700, amma ba duka ba ne suka halaka
  • An samu ƙwarangwal ɗin waɗannan dabbobin ne a kowacce nahiya da ke duniyar Earth, kuma saboda girman ƙwarangwal ɗin hakan ya tabbatar lallai waɗannan dabbobi ba ƙaramin girma gare su ba.
  • A manyan gidajen tarihi akwai ƙwarangwal ɗinsu, masana ne suka kai bayan sun gama wasu ‘yan bincike-bincikensu a kai.

2. Woolly Mammoth

Irin waɗannan dabbobin sun rayu tsawon wasu dubunnai shekaru da suka gabata a gabashin nahiyar Asia. Masana suka ce halakarsu za ta iya kai wa aƙalla shekaru dubu 800,000 da suka shuɗe.

A tsarin siffa da girma, waɗannan dabbobin suna matuƙar kama da giwa sai dai sun fi ta girma. Suna da manyan ƙaho a ka da hannu mai kama da na giwa.

3. Sabre-toothed Cat

A zubin halitta wannan dabba tana kama da damisa, wasu masanan ma suka ce takan iya faruwa ta kasance daga cikin nau’ukan damisa da suka halaka a shekarun baya.

Wasu nau’ukan dabbobin da ke jadawalin dabbar Sabre-toothed Cat sun haɗa da Smilodon, Pogonodon, Adelphailurus, Proailurus da sauransu waɗanda yawanci suka rayu a nahiyar North America.

4. Dunkleosteus

Duk da suna da dogon tarihi da nau’uka da dama, dabbobin Dunkleosteus sun rayu aƙalla shekaru miliyan 360 da suka gababa. An samu ƙwarangwal ɗinsu a yankunan ƙasashen Poland, da Belgium da kuma wasu sassa na nahiyar North America.

Zuwa yau masana sun gano nau’ukan waɗannan dabbobi aƙalla guda 10, ta hanyar binciken ƙwarangwal ɗinsu a sassan wurare a faɗin duniya.

5. Megatherium

Irin waɗannan dabbobin masu kama da dila ta fuskar halitta sun halaka dubunnan shekaru (aƙalla 12) da suka shuɗe. Ana gano wasu sassa na jikinsu wanda tuni ya zama ƙwarangwal, wanda aka fara ganowa a shekarar 1788.

6. Komodo dragon

Komodo dragon na ɗaya daga cikin dabbobin da ke nau’ukan ƙadangaru sannan masu matuƙar kama da kada, sai dai suna da hatsari sosai. A yanayin girma, tsayinsu yana kai wa kamar mita 3, sannan nauyinsu kuma kilogram 70. Masana suka ce su kan rayu har na tsawon shekaru 30 ko fiye da haka.

Sai dai ba duka nau’ukan waɗannan dabbobin ba ne suka halaka, kaɗan ne daga ciki, kuma har yanzu ana samun wasun su a nahiyoyi daban-daban.

7. Argentavis

Wannan kuma wasu nau’in tsuntsu ne da suka kasantu a baya, amma daga bisani su ma suka halaka. Kasancewarsu tsuntsaye da ke tashi, har wasu daga cikinsu ma kan iya tafiyar kilomita 40 a sa’a guda. Suna yin ƙwai guda biyu ko ɗaya duk bayan shekaru biyu

8. Megalodon 

Waɗannan irin nau’i na kifayen shark masu manyan haƙora da ake ƙira megalodon sun rayu aƙalla shekaru miliyan 10 da suka shuɗe. Masana suka ce tsayinsu zai iya kai wa mita 15. Sannan suna da matuƙar nauyi, a inda haƙoran nasu shi ne ya kasance mai wannan nauyin sosai.

Madogara

[1] Encyclopedia of Zoology

[2] Wikipedia.org

[3] Encyclopedia Britannica

Mohiddeen Ahmad

Mohiddeen Ahmad

I am Muhammad Auwal Ahmad, an inquisitive student, tech aficionado, science enthusiast and a writer. I am the founder and CEO of Flowdiary.

One Comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *