5

Yanar Gizo: Bayani da Bambanci Tsakanin Surface Web, Deep Web da Dark Web

Haƙiƙa yanar gizo tana da girma gaske, girman da mutum ba zai iya haƙaitowa kai tsaye ba. Kamar dai girman ƙaunu; duk inda Ɗan-Adam ya sani bai wuce ƙwayar zarra idan aka kwatanta shi da girman ƙaunun gaba ɗaya ba. Haka nan yadda muka san yanar gizo da ake ƙira web, wasu ɓoyayyun lunguna a cikinta sun kasance na daban.

Wasu lokuta mu kan ci karo da waɗannan kalmomi Surface Web, Deep Web da Dark Web, amma ba mu san ma’anoninsu ba. don haka wasu suke ɗauka kawai suna ne na wasu abubuwa waɗanda ba su kai sun kawo ba. Amma sai dai lamarin ya girmi haka.

Yadda yanar gizo –web ya kasance kundin shafuka da aka ɗaura a yanar gizo, haka nan yana da wasu fannoni da suka kasance ire-irenshi, kamar haka:

1. Surface Web

Wannan fanni na yanar gizo shi ne inda kowa yake shiga –wato shafukan yanar gizo ba tare da sanya lambobin tsaro don sirri ba. Waɗannan shafukan da ake shiga da suke rukunin Surface Web sun haɗa da Flowdiary, Google, BBC, ArewaBlog da sauransu don karanta bayanai ko sauƙe wasu abubuwa ba tare da sanya wasu lambobin tsaro ba. Ke nan waɗannan shafukan sun kasantu ne a zaure na farko a yanar gizo.

Irin waɗannan shafukan ana iya ƙirƙirarsu da yarukan na’ura kamar HTML da CSS zalla ko wasu daban, don sun kasance a bayyane wato shafukan da aka ba wa kowa damar shigarsu.

2. Deep Web

Wannan zauren kuma ya kasance ɗaki ne mai mukulli da dole ana buƙatar mukullin kafin a iya shiga ciki. Wato wannan fanni na shafukan da suke buƙatar matakan shiga cikinsu kamar yin rajista da sanya lambobin tsaro –misalin irinsu sun haɗa da Facebook, Paystack, PayPal Luno –ma’ajiyar kuɗaɗen lantarki, da makamantansu. Ke nan waɗannan shafukan suna adana bayanansu ne a rumbun bayanai don kula da tsare bayanan mutane da suka karɓa. Kamar bayanan mutum na banki ko kasuwanci dole za a tsare su don madatsa da makamantansu.

3. Dark Web

Shi kuma wannan fanni ne da ya ƙunshi duk wani sirri na yanar gizo kuma nan de fadar da ake aikata duk wata ɓarna. Wannan fanni na yanar gizo ya kasance baƙin ɗaki da ake ajiye duk wasu abubuwan da ba a so mutane su sani. A nan ake ajiye duk wasu bayanan sirri na leƙen asiri, ake yin dillacin makamai da haramtattun magunguna da makamantansu.

Sannan fanni ne da shu’uman duniya suke haɗuwa don tattauna batutuwansu wanda ya kasance babban sirri. A kan yi cinikin duk wasu abubuwa da suka kasance haramtattu a duniya kamar ƙwayoyi, bayanan sirri, dillacin kisa da makamantansu. Haka nan a nan ake cinikin makamai da adana bayanan sirri na leƙen asiri da duk wasu sha’anonin sirri na duniya.

Kasancewar ɗakin yana da matuƙar girma ga kuma mummunan duhu ya sa ba a iya shigarsa kai tsaye kamar yadda ake shiga shafukan da kowa ya sani. Sannan ba za a iya kama mutum ko gano wani abu dangane da shi a Dark Web ba.

Me ya sa?

A shekarun 1990s wata runduna ta jami’an tsaro a ƙasar America suka samar da Dark Web saboda adana bayanan sirri da leƙen asiri, da harƙallar wasu abubuwansu da ba sa so duniya ta sani. Don haka sai ya zama wuri ne na sirri da ba kowa ba ne yake iya shigarsa. Hatta manhajojin wayoyinmu ma ba za su iya shiga wurin ba don yanayin tsarinsa duk ya sha bamban da yanar gizon da muka sani.

A Dark Web ba a amfani da irin waɗannan sunaye na shafukan yanar gizo irinsu Flowdiary.com.ng, sai dai wani suna mai wahala kamar fl0wd1ar33yyi.onion wato wannan .onion ɗin ya kasance laƙabin shafi. Sannan shi ma ya samo asali ne daga sunan The Onion Router (TOR) –a inda shiga shafukan ya kasance sai da wasu irin manhajoji da aka ƙirƙira musamman don su kamar TOR Browser ko I2P

Ke nan Dark Web baƙin ɗaki ne na yanar gizo da ko injinan binciken yanar gizo kamar Google ko Bing da suke amfani da manhajar binciken ƙwaƙwaf wato crawler ba za ta iya nemo shafin Dark Web ba, ballantana shiga da manhajojin da ake amfani da su wajen shiga shafukan yanar gizo irinsu Chrome, Opera, Mozilla da makamantansu.

Bambanci a Jadawali

BambanciSurface WebDeep WebDark Web
RukuniZauren kowaƊakin tattaunawaBaƙin ɗaki
TsariKowa zai iya shigaAna buƙatar yin rajista kafin shigaBa kowa ba ne zai iya shiga
MisaliFlowdiary.com.ng, Google.com Wikipedia.comLinkedIn.com, Payant.ng, Twitter.comfl0wd1ar33yyi.onion
Manhajar shigaChrome, Mozilla, IE…Chrome, Mozilla, IE…TOR Browser
AikiKaratu kyauta, bincike, samun labaraiAjiye bayanai, sada zumunci, karatu…Dillacin haramtattun kaya, ajiye manyan bayanan sirri…
GirmaƘaramiBabbaMafi girma
Injinan bincikeZa su iya nemowaBa sa iya nemowaBa za su iya nemowa ba
Bayanin bambaci a jadawali

Madogara

[1]     Service Care

[1]     Encyclopedia Britannica

[2]     Kristin, Finklea: ‘Dark Web’ (2017), Congressional Research Service

Mohiddeen Ahmad

Mohiddeen Ahmad

I am Muhammad Auwal Ahmad, an inquisitive student, tech aficionado, science enthusiast and a writer. I am the founder and CEO of Flowdiary.

5 Comments

  1. Wanna ilmantar damu kake, wannan shafi flowdiary ai makaranta ne a gurin mu. Babu abun da zamu saka madashi sai muce dai muce ALLAH kara basira da hazakha sako daga AUWAL MAMU YOLA

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *