1

Ire-iren Fasaha 16 da Za Ka Iya Sani Waɗanda Suka Taimaka a Ɓangarori da Dama

fasaha

Fasaha ta rabu kashi-kashi kamar yadda kimiyya take, wato akwai wasu fannoni da aka samar a  ƙarkashinta sakamakon bunƙasarta a zamanance.

Waɗannan fannoni na fasaha sune suke gudanar da wannan zamani ta fuskar cigaba. Sannan sun samo asali tun daga ƙarnukan baya a tsohuwar duniya har zuwa yau.

Waɗanda za a iya sani daga cikinsu sun haɗa da:

1. Communication Technology

Wannan fanni na fasaha da ake ƙira communication technology shi ne fasahar sadarwa waɗanda tun a ƙarnin baya ake amfani da su. Misalan wannan fasaha sun haɗa da rediyo, da talabijin, da waya, da kuma yanar gizo. Waɗannan fasahohin sadarwa da su muke amfani a kullum wajen isar da saƙonni a faɗin duniya.

2. Medical Technology

A fannin lafiya, sarrafa magani da likitanci, medical technology ya kawo muhimmin sauyi wajen zamanantar da duk wani sashe a fannonin. Ƙasashen da suka ci gaba suna amfani da waɗannan fasahohi da aka samar don gudanar da gwaji, fiɗa, sarrafa magunguna da sauran muhimman ɓangarori na harkokin lafiya da likitanci. Misali, kamfanin IBM ya ƙirƙiri wani saƙago da ke taimakawa likitoci wajen gudanar da fiɗa.

3. Construction Technology

Duk wata gada, hanya, gini da makamantansu da ake gani yau sun danganta da fasahar gini da ƙira. Duk da ta kasance tun tala-taini, amma an samu damar bunƙasa ta ta yadda a yau ta kasance mai matuƙar taimako ga kowa.

4. Information Technology

Fasahar bayanai kuwa ba ƙaramin taimako na canji ta kawo ba a wannan duniyar. Duk wani lamari da ya shafi rumbun bayanai, na’ura, yanar gizo, fasahohin sadarwa duk sun ta’allaka ne a wannan rukuni kuma sune suka gina shi. Wannan fasaha ta zama ruwan dare a wannan zamani, don mafi yawancin manyan kamfanonin duniya a ɓangarenta suke. Misali kamfanin Google, Apple, Facebook da makamantansu.

5. Space Technology

Fasahar sararin samaniya ta taimaka matuƙa a yunƙurin tafiya sararin samaniya. An haɗa da fannonin kimiyya da dama kamar ɓangaren physics da astronomy, da wasu fannonin fasaha don dacewa da abun da ake son ginawa. Ta dalilin wannan fasaha a yau ana iya kallon talabijin ta hanyar ƙirƙirar tauraron Ɗan-Adam a ko ina a faɗin duniya.

6. Artificial Intelligence

Fasahar fiƙira da ake ƙira Artificial Intelligence ta zama ruwan dare a wannan zamani duk da ba ta jima da kasantuwa ba. Wato fasaha ce da ake kokarin sanya wa na’ura, ta yadda na’urar za ta kasace mai basira da tunani da fiƙira kamar Ɗan-Adam. A yau tasirin wannan fasaha ya yi sanadiyyar samar da babban cigaba a faɗin duniya, duk da ita ma tana da nata muƙarraban.

7. Operational Technology

A yau, wannan fasaha kuma ita ta zama ruwan dare kusan fiye da sauran. Tana taka muhimmiyar rawa a fannoni da dama. Misalanta sun haɗa da yadda ake ƙirƙirar abubuwan zamani don sauƙaƙa wasu abubuwa da ake amfani da su, musamman waɗanda suka kasance na gudanarwa a harkokin yau da kullum.

8. Entertaimanent Technology

A ɓangaren nishaɗantarwa, fasaha ta yi kaka-ni-kaka don kuwa ta kawo sauyi sosai. Don haka wannan fannin ya kasance na ta sukutum saboda ƙirƙirar fasahohi da ake yi da suke ƙayatar da ita kuma suke ƙara bunƙasata ta. Misali ƙirƙirar na’urori da manhajojin shirya bidiyoyi, wasanni, har da tsere ko gasa da makamantansu.

9. Robotics Technology

Fasahar saƙago kuwa ta ginu ne don gina saƙagai da muƙarrabansu. Ana ƙirƙira saƙagai da dama da suke taimakawa duk wasu lunguna da saƙo don kawo muhimman sauyi a rayuwar yau da kullum.

10. Superintelligence

Tun daga wannan lokaci zuwa nan gaba ana hasashen wannan rukunin na fasaha zai kasance mai tsananin fiƙira da basira da ya fi na Ɗan-Adam. Misalin wannan rukuni sun haɗa da Artificial Superintelligence da transhumanism.

11. Business Technology

A fannin kasuwanci ma fasaha ta yi kane-kane saboda zamanantar da tsarin kasuwanci. Ana ƙirƙirar manhajoji da suke matuƙar taimakawa wajen gudanar da lamuran kasuwanci da cinikayya gida da waje.

12. Educational Technology

A ɓangaren ilimi kuwa, tasirin fasaha ya wuce duk inda mutum zai iya yin tunani. Miliyoyin shafukan yanar gizo da suke taimakawa ɗalibai da malamai wajen ɗaukar darussa ma kaɗai sun isa su ba da kyakkyawar shaidar fasahar a wannan fanni. Ga manhajoji da fasahohi kala-kala da ake ƙirƙira a kullum.

13. Architectural Technology

Gini da ƙayatarwa yau ya yi matuƙar faɗaɗa ta hanyar rukunin wannan fasaha. Yau mutum ya kan iya buɗe na’urarsa ya tsara duk yadda yake buƙatar tsarin gininsa ya kasance. A kan yi zane da ko ƙirƙirar na’urori masu alaƙa da fannin da makamantanu.

14. Assistive Technology

Misalan fasahohin da ake ƙirƙira musamman don taimakawa gajiyayyu da agaza musu sun haɗa da na’urar ƙara sauti, da na’urar ƙara gani, da na’urar fito da sauti irin wacce masani Stephen Hawking yake amfani da ita ƙafin mutuwarsa. Wannan fanni ya kasantu ne musamman don agaza wa miskinai.

15. Aerospace Technology

Wannan ɓangaren kuma ya haɗa da ƙirƙirar jirgi da sauran ababen tashi sama kamar na’urar drones da makamantansu. Har yanzu ana nan ana ƙirƙiro fasahohi da za su ƙara taimaka wa duniya wajen tafiye-tafiyen da suka shafi keta hazo.

16. Military Technology

Ɓangaren jami’an tsaro sun samu babban cigaba, wanda shi yayi sanadiyyar ƙirƙirar yanar gizo don adana bayanai da haƙakayya tsakanin na’urori. Har yanzu kuwa akwai manya-manyan na’urori da fasahohi da suke ƙara taimaka musu wajen gudanar da muhimman ayyukansu.

Mohiddeen Ahmad

Mohiddeen Ahmad

I am Muhammad Auwal Ahmad, an inquisitive student, tech aficionado, science enthusiast and a writer. I am the founder and CEO of Flowdiary.

One Comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *