11

Bambancin ‘Web’ da ‘Internet’: Bayani kan Ma’anonin PAN, LAN, MAN da WAN

Sau tari mutane da dama suna tunanin internet da web ko yanar gizo ma’anarsu guda saboda yadda ake amfani da su a wurare daban-daban ba tare da bambancewa ba, amma dai a zahirance suna da bambanci. A wannan rubutu za a iya fahimtar mene ne ma’anonin gajarcin kalmomin PAN, LAN, MAN da WAN, sannan kuma a iya fahimtar bambancin web da internet tare da misalansu.

PAN

PAN gajarcin kalmar Personal Area Network ne da ke nufin sashin sadarwa mafi kusa da mutum, wanda kowa zai iya mallakar shi kuma yayi yawo da shi ko da a tafin hannunsa ne. Misalin irin waɗannan irin sashin sadarwan sun haɗa da Bluetooth ko Wi-Fi; duk suna ba da damar sada na’urori a wuri guda matukar na’urorin sun kasance a kusa. A irin wannan yanayi waɗannan na’urori za su iya musayar fayil.

LAN

LAN ma gajarcin kalmar Local Area Network ne wanda ya kasance sashin sadarwa da ya fi PAN ƙarfi, wato za a iya yin ɗan nesa da na’urorin kuma su kasance suna sada juna. Misalin irin waɗannan sashinan sadarwan su ne waɗanda ake yi a wata ma’aikata, ko wani gini, ko asibiti ko gida ko kamfani da makamantansu. Mutum zai iya sada na’urarsa a wannan sashen sadarwan matukar bai wuce kilomita guda tsakaninsa da magudanarta ba. Ana iya haɗa irin wannan sashin sadarwan a wurare da dama sannan a saita duk wasu lamura na gudanar da ita a wannan wuri ta yadda za ta kasance a wurin sai da mutane su zo su sada na’urorinsu da ita.

MAN

Gajarcin kalmar Metropolitan Area Network, shi kuma ci gaba ne kuma babban LAN wanda ya kasance za a iya saita shi a babban birni ko wani yanki, wato za a iya sada wannan sashin sadarwan ko da mutum zai yi nisan kilomita 50 ko fiye da haka tsakaninsa da ita. Ke nan an samu ci gaba na sashin sadarwan LAN, ta yadda wannan sashin sadarwan yake iya sada na’urori da ke gari guda ko wani yanki baki ɗaya. Misalan irin wannan sashin sadarwan sun haɗa da gidan rediyo ko ko talabijin waɗanda ake gudanar da su a gari guda, ko wani yanki.

WAN

Kamar yadda PAN ya kasance na mutum guda zuwa biyu, LAN ya kasance na wuri guda na ma’aikata, MAN ya kasance nan a birni ko ƙasa baki ɗaya, hakanan shi kuma WAN ya kasance cigabansu ne duka. Cikakkiyar kalmar Wide Area Network da ke nufin sashin sadarwa wanda zai mamaye kuma yayi aiki a dukkanin nahiya ko ƙasa guda. Misalin irin wannan sashin sadarwan shi ne yanar gizo wato Internet, wanda ita ma ta samo asali daga International Networking.

Internet da Web

Gundarin kalmar internet na nufin haɗakayyar na’urori a sashinan sadarwa daban-daban don su sadu da juna a layi guda, a inda wannan ya kasance matakin da internet ya ke. Wato yana ba da damar sada sashinan sadarwa da dama, ko kuma waɗanda ba su da iyaka daga sassan wurare a faɗin duniya.

A duk lokacin da mutum ya buɗe na’urarsa ya shiga yanar gizo, hakan na nufin ya sada sashin sadarwarsa da miliyoyin sashinan sadarwa da ke wurare daban-daban a faɗn duniya.

Amma abunda ake ƙira web kuma shi ne shafukan da aka ɗaura su a yanar gizo, misali Flowdiary.com.ng, Google.com, DailyTrust.com da sauransu, dukkansu shafuka ne da ke gudanar da lamuransu a internet.

Kalmar Yanar Gizo

Fassarar kalmar yanar gizo kai tsaye zuwa turanci ita ce internet, domin ita ce haɗakayya ta miliyoyin sashinan sadarwa daga mabambantan wurare a faɗin duniya. Kalmar yanar gizo ta samo asali ne saboda fahimtar da da bahaushe yayi wa internet cewa haɗakayya ce ta sashinan sadarwa, saboda ganin yadda gizo yake haɗa kowane lungu da saƙo na yanarsa.

Amma web kuma shafuka ne da aka ɗaura su a wannan haɗakayya ta sashinan sadarwa, ta yadda mutum zai iya sada sashin sadarwarsa da wannan haɗakayya kuma ya iya shiga wani shafi don karanta abunda aka rubuta ta hanyar shiga shafukan da aka ɗaura.

Sanin cewa a shekarar 1969 aka ƙirƙiri internet kuma tun daga wannan lokaci ya kasance sashin sadarwa mafi girma kuma mafi ƙarfi, amma web kuma sai a shekarar 1989 aka samar da wannan fasaha ta ɗaura shafuka a kan internet.

Bambanci a Jadawali

BambanciWebInternet
Shekarar ƙirƙira19891969
Cikakken sunaWorld Wide WebInternational Networking
Ma’ana a taƙaiceGundarin shafukan yanar gizoHaɗakayyar sashinan sadarwa
Misalihttps://flowdiary.com.ng   Yanar gizo
Bayani na IAkwai shafuka biliyan 1 da miliyan 800 a yanar gizoMutanen da ke hawa yanar gizo sun kai biliyan 4 da miliyan 700 a yanar gizo
Bayani na IIAna shiga shafuka ta hanyar amfani da manhaja da ake ƙira web browser, misali Chrome, Opera, Mozilla, Internet ExplorerKowace na’ura tana da iko na karan kanta a yanar gizo
Bayani na IIIWeb wani fanni ne na yanar gizoYanar gizo ya kasantu a karan kansa
Bayani na IVTim Berners-Lee ne ya ƙirƙiro fasahar world wide webCibiyar bincike ta America mai suna Advanced Research Projects Agency ce gundarin samuwar yanar gizo
Bayani na VKullum ana samun sababbin shafuka aƙalla 54,7200Kullum ana ɗaura na’urori sama da biliyan 3 a yanar gizo
Bayani na VIƘirƙirar wannan fasaha ya kawo babban canji ga fahimta da moriyar yanar gizoƘirƙirar yanar gizo ya canja duniya ta hanyar zamanantar da ita

Danna nan don sanya sunanka da adireshinka imel ɗinka ta yadda za ka rinɗa samun rubuce-rubucenmu kai tsaye da zaran mun yi.  

Madogara

[1] InternetLiveStats.com

[2] An Introduction to Computer Networks by Peter Dordal

[3] Introduction to Fundamentals of Computer and its Application by Kayode Adeleke

Mohiddeen Ahmad

Mohiddeen Ahmad

I am Muhammad Auwal Ahmad, an inquisitive student, tech aficionado, science enthusiast and writer. I am the founder of Flowdiary.

11 Comments

  1. Muna godiya kana da bada goyon baya a gareku wurin kokari da kukeyi wajen ganin kunviliman tar damu.Allah ya saka da alkairy.

  2. Muna godiya kana da bada goyon baya a gareku wurin kokari da kukeyi wajen ganin kun iliman tar damu.Allah ya saka da alkairy.

  3. Mashaallah gaskiya #Iron_man bansan irin abinda zance ba sai daucgaskiya kana qoqari Allah ya biyaka d mafiyin hakan

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *