3

Bayani kan Quantum Computer: Tsari, Amfani da Tasirinta a Duniyar Zamani

Engadget

Wasu na’urori da suka yi ƙaurin suna a ƙarni na 21 da ake ƙira Quantum Computer a yanzu suna janyo hankalin mutane sosai ta yadda ake son jin labarinsu da kuma abubuwan da suka ƙunsa da komai game da su. Wasu su kan tambaya, shin mene ne amfanin waɗannan na’urori kuma ta yaya za su kawo canji na cigaba a duniyar zamani?

Mece ce Quantum Computer?

Sakamakon bayyanar kimiyyar ƙananan ƙwayoyi da ake ƙira Quantum Mechanics, waɗannan na’urori da ake kan ƙirƙira waɗanda aka daidaita tsarin gudanarwarsu kan kimiyyar quantum mechanics, ana hasashen za su taka muhimmiyar rawa wajen kawo cigaba a yanayin tsarin na’urorin da ake amfani da su a duniya, musamman yadda suke da sauri da kuma manyan sashinan sadarwa da gudanarwarsu. A taƙaice, waɗannna na’urori da ake ƙira quantum computers daban suke da na’urorinmu na yau da kullum ta fuskar tsari, tasiri, amfani da cigaban da za su kawo a yanzu da kuma nan gaba.

A jadawalin ginin na’ura da cigabanta wanda ya fara tun daga tsarin gini na farko da ake ƙira 1st Generation a shekarar 1946 har zuwa yanzu da ake amfani da 4th Generation da kuma 5th Generation –wanda ya kasance a kan tsarin fasahar Artificial Intelligence, masana da dama a duniya sun alaƙanta quantum computer da zama tsarin ginin na’ura na shida wato 6th Generation, saboda babu wani lamari na cigaba da waɗannan na’urori ba za su iya ɗauka ba.

Tsarin Quantum Computer

Na’urorinmu na yanzu suna amfani da lambobin 0’s da 1’s don adana bayanai, sarrafa su da kuma fitar da su. Amma a tsarin waɗannan sabbin na’urori na quantum babu tsarin amfani da 0 ko 1 don adana bayanai ko sarrrafa su, babu tsarin amfani da haruffan A ko B wajen sarrafa bayanai zuwa ga gundarin tsarin masarrafar bayanan na’ura. Tsarin masarrafar bayanan quantum computer zai tafi ne kan yadda za a yi amfani da ziri don fuskantar bayanai kai tsaye ba tare da juya su zuwa wani nau’i na lambobi ba kamar yadda ake yi a na’urorin yanzu –classical computers.

Ke nan quantum computer za ta daidaitu ne tsakanin 1 ko 0 don ƙirƙirar irin nata tsarin sarrafa bayanai da ake ƙira quantum bit –qubit.

Ko haka:

Tasirin Quantum Computer

Abu na farko da ya sa quantum computer yin tasiri shi ne don “third option” da take da, wato wata dama ta faɗaɗa shigar da bayanai ba tare da an yi musu iyaka ba. A na’urorin yanzu kawai tsarin 0 da 1 ne, amma a na’urorin quantum kuma lamarin ya faɗaɗa.

A na’urorin yanzu 1 ko 0 na nufin ‘e’ ko ‘a`a’, ‘za a yi’ ko ‘ba za a yi ba’; amma a quantum computer kuma ba a amfani da su ɗaya-bayan-ɗaya, sai dai a kai-ɗaya don haka ne ta fiye sauri da kuma samun damar warware wata matsala cikin gaggawa kuma cikin sauƙi.

Ke nan quantum computers sun kasance masu matuƙar sauri da suka fi waɗannan na’urorin yanzu sauri sau sama da dubu, kamar yadda wani farfesa a Amherst University ya faɗa. A yanzu haka dai kamfanin IBM shi ne ya yi nasarar ƙirƙirar quantum computer da duniya ta shaida.

Don wannan saurin, kamfanin Google ya ce ya cim ma wani ɓangare na tasirin quantum computer na warware matsaloli cikin sauri, inda na’urar ta warware wata matsala cikin gaggawa, wacce za ta iya ɗaukan na’urar yanzu shekaru masu yawa kafin ta gama. Haka nan kamfanin ya ce na’urar tasu ta fi na’urarion yanzu sauri sau sama da miliyan ɗari.

Amfanin Quantum Computer

Haƙiƙa quantum computers suna da matuƙar amfani a wanan zamanin saboda za su kawo canji sosai game da tafiyar da fasaha da na’ura.

1. Fasahar Artificial Intelligence

Ɓangare na farko da quantum computer za ta yi aiki kuma ta taka muhimmiyar rawa shi ne ɓangaren fasahar Artificial Intelligence –wacce ta kasance fiƙira ce ta ba wa na’ura tsarin gudanarwa kamar na Dan-Adam; kamar basira, tsarin fiƙirori, tunani, hankali da makamantansu.

A wannan tsarin, quantum computer za ta ba wa wanan fasaha tare da muƙarrabanta kamar Machine Learning; wanda ya kasance tsarin fiƙira ne da ke ƙoƙarin ba wa na’ura damar tsarin koyon abubuwa kamar mutum –damar gudanar da ayyukan fasaha cikin sauƙi kuma yadda ya kamata. Hakanan kamfanin IBM ya ce na’urarsa ta quantum za ta taimaka sosai a bangaren fasahar Machine Learning da tsarin fiƙirorinsa.

2. Tsarin Tsaro da Ɓoye Bayanai

Duk da na’urorin yanzu suna da tsaruka na ɓoye bayanai, amma quantum computer za ta ba wa tsaro muhimmancin gaske ta yadda madatsa ba za su iya fahimtar wannan bayanin da aka ɓoye ba ballantana iya sarrafa shi. Masana suka ce za ta yi muhimmin aiki a ɓangarorin cinikayya da banki da kuma sashinan adana muhimman bayanai da makamantansu.

3. Aiki a Masana’antu

Manyan masana’antu musamman na sarrafa magunguna da sauran waɗanda ke buƙatar sauri da gano wasu abubuwa wajen gudanar da aiki suna buƙatar quantum computer don sauƙaƙa musu lamura. Masana suka ce za a kawo canji a ɗakunan binciken kimiyya da sauran manyan masana’antu da wuraren bincike, musamman idan aka yi duba da yadda quantum computer za ta rinka gudanar da lamarunta cikin ƙwarewa, sauri da kuma faɗaɗa wasu sashinan gudanarwanta.

4. Sashin Fasahar Sadarwa

Dalili na farko da ya sa fasahar sadarwar 5G ta kasantu don taimakawa quantum computer wajen gudanar da ayyukanta, ta yadda saurin nata zai bunƙasa matuƙa. Ko da a manyan na’urorin yanzu amfani da fasahohin sadarwa waɗanda ke ƙasa da 5G abu ne wanda masana suka ce kamar koma-baya ne. don haka a wannan mataki quantum computer za ta yi aiki da ne wannan sabuwar fasahar sadarwa.

5. Warware Duk Wani Hasashen Kimiyya ko Fasaha

Quantum Computer za ta zama wani magani na warware duk wanu hasashen kimiyya ko fasaha. Misali, a hasashen kimiyya akwai cigaban fasahar Artificial Intelligence da ake ƙira Superartificial Intelligence wacce ke ƙoƙarin fin mutum duk wani surkellensa, basira da kuma nazari da ilimi.

Hasashen da aka yi cewa a idan aka zo wannan lokaci za a iya sauƙe bayanan ƙwaƙwalwar mutum don ɗaurawa a na’ura, wannan lamari da ake ƙira technological singularity. Amma na’urorin yanzu ba za su iya wannan aiki ba, quantum computer ce kawai za ta iya adana bayanan ƙwaƙwalwar mutum. Don haka wannan ya kasance wani yunƙuri ne na tabbatar da wannan hasashe da ma sauran.

Madogara

[1] IBM.com

[2] Forbes.com

[3] Encyclopedia Britannica

Mohiddeen Ahmad

Mohiddeen Ahmad

I am Muhammad Auwal Ahmad, an inquisitive student, tech aficionado, science enthusiast and a writer. I am the founder and CEO of Flowdiary.

3 Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *