3

Wasu Nau’ukan Dabbobin Dinosaurs 30 Da Za Ka So Sani

Akwai nau’ukan dabbobin dinosaurs 700 a duniya

Dinosaur wasu nau’ukan dabbobi ne da suka rayu miliyoyin shekaru da suka gabata, kuma mafi yawacin nau’ukan dabbobin sun halaka ne sakamakon wani iftila’i na dutsen asteroid da ya faɗa musu.

Masana suka ce waɗannan dabbobi sun shafe aƙalla shekaru miliyan 245 suna rayuwa kafin wannan iftila’i ya yi sanadiyyar halakar yawancin nau’ukansu, sannan daga lokacin halakar ta su zuwa yanzu kuma ya kai shekaru miliyan 66.

Wasu Abubuwa Dangane Da Su:

  • Sun rayu tsawon shekaru miliyan 245 a duniyar Earth
  • A shekarar 1842 wani masanin kimiyyar halittu da ake ƙira Sir Richard Owen ya samar da wannan suna daga lalmar Greek deinos wacce ke nufin “tsoro” da kuma sauros wacce ke nufin “ƙadangare”
  • Akwai aƙalla nau’ukan waɗannan dabbobi 700, amma ba duka ba ne suka halaka
  • An samu ƙwarangwal ɗin waɗannan dabbobin ne a kowacce nahiya da ke duniyar Earth, kuma saboda girman ƙwarangwal ɗin hakan ya tabbatar lallai waɗannan dabbobi ba ƙaramin girma gare su ba.
  • A manyan gidajen tarihi akwai ƙwarangwal ɗinsu, masana ne suka kai bayan sun gama wasu ‘yan bincike-bincikensu a kai.

Rukunin Nau’uka

  • Saurischia – irin waɗannan dinosaurs ɗin su ne masu kama da ƙadangaru, a sashinan rukunin kuma akwai theropods; waɗannan dinosaurs ɗin su ne masu cin nama zalla, sannan yawancin tsuntsaye daga cikinsu suka samu kuma su ne masu tafiya da ƙafa biyu –irinsu spinosaurus, allosaurus ko carnotaurus; na biyu kuma sauropods; waɗanda suke tafiya da ƙafa huɗu sannan su ne masu girma sosai kuma su ciyawa kawai suke ci –daga cikin misalansu akwai diplodocus da brachiosaurus.
  • Ornithiscia –wannan rukunin kuma su ne masu kama da tsuntsaye, a sashinansu akwai thyreophora; misalan irin waɗannan akwai stegosaurus su ma suna matuƙar girma; sannnan sashe na biyu kuma sai cerapods; misali irin su iguanodon.

Jerin Nau’uka

Ba dukkanin nau’ukan dabbobin dinosaur guda 700 ne suka halaka lokaci guda ba, amma dai mafi yawancin sun halaka ne a wancen lokacin.

1. Stegosaurus

Dabbobin stegosaurus sun ɓace a duniyar Earth ne kimanin shekaru miliyan 155 da suka gabata, sannan an samu ƙwarangwal ɗinsu ne a wasu yankunan Canada da America, wato a nahiyar North America. Waɗannan halittu masu zubin ƙadangare suna da matuƙar girma da ban tsoro. Tsayinsu (daga kai zuwa wutsiya) yana kai wa mita 9, sannan tsayinsu (daga ƙafa zuwa baya) ya kai mita 4. Wannan ya nuna cewa lallai waɗannan dabbobi ba karami girma gare su ba.

2. Apatosaurus 

Kamar dai stegosaurus, apatosaurus ma na ɗaya daga cikin mafiya girman dabbobin dinosaurs da suka rayu a baya. Suna da doguwar wutsiya da wuya, sannan da gajerun ƙafa. Su ma dai sun rayu shekaru miliyan 150 da suka gabata, kuma an samu ƙwarangwal ɗinsu a nahiyar North America. Tsayinsu (daga kai zuwa wutsiya) ya kai mita 23, sannan daga kafa zuwa baya kuma ya kai mita 5. Ke nan shi apatosaurus sun ninka stegosaurus a tsayi da girma sau biyu ko fiye da haka kenan.

3. Tyrannosaurus

Haka nan tyrannosaurus ma sun kasance mafiya girma da suka rayu a North America shekaru miliyan 65 da suka gabata. Tsayinsu (daga kai zuwa wutsiya) ya kai mita 13, sannan daga kaƙa zuwa baya kuma ya kai mita 7. Suna da matuƙar girma da nauyi. Masana suka ce a suka yi loma ɗaya da naman da ya kai nauyin kilogram 200.

4. Allosaurus 

Allosaurus ya kasance daya daga cikin nau’ukan dinosaurs wanda ke rukunin theropods wato waɗanda suka kasance a tsarin halittar ƙadangare, amma suna da ƙafa biyu manya a baya, sannan sai hannu biyu a gaba kamar ƙafa. Sun rayu shekaru miliyan 155 da suka gabata. An samu ƙwarangwal ɗinsu a yankin Portugal da Tanzania tun lokacin da masana suka fara bincike a kansu. Masana suka ce ƙwaƙwalwarsu babba ce sai dai suna da gajeren wuya ba kamar su stegosaurus ba.

5. Coelophysis 

Coelophysis ba su kasance masu girma sosai ba kamar sauran, sun rayu aƙalla shekaru miliyan 200 da suka gabata a wasu yankunan Zimbabwe, South Africa da America. Masana suka ce nama ne ya kasance abincinsu, sannan suna tafiya da ƙafa biyu da hannuwa biyu a gaba kamar dai allosaurus, sai daishi tsayinsu (daga kai zuwa wutsiya) gaba ɗaya ba ya wuce daga mita 3-4

6. Carnotaurus 

Haka nan Carnotaurus kuma sun rayu shekaru miliyan 72 da suka gabata, kuma an samu ƙwarangwal ɗinsu a South America. Suna matuƙar kamanceceniya da coelophysis kusan duk wani yanayi da tsarin zubin halittarsu ɗaya ne. Tsayinsu (daga kai zuwa wutsiya) yana kai wa daga mita 5-9, haka nan daga ƙafa zuwa baya kuma yana kai wa mita 3.

7. Deinonychus 

Deinonychus ma nau’i ne na dinosaurs da suka rayu shekaru miliyan 115 da suka gabata. Yawancin ƙwarangwal ɗinsu da ake samu daga yankunan America ne. Suna tafiya da ƙafa biyu sannan tsayinsu (daga kai zuwa wutsiya) ya kai mita 3.

8. Diplodocus 

A shekarar 1877 aka fara gano ƙwarangwal ɗin diplodocus. Sun rayu a yamma ta tsakiyan yankin North America shekaru aƙalla miliyan 154 da suka gabata. Suna da girma da dogon wuya kuma suna tafiya da ƙafa huɗu. Tsayinsu (daga kai zuwa wutsiya) ya kai mita 26. Wannan ya nuna suna da matuƙar girma, don sune a sahun farko wajen tantance girman dabbobin dinosaurs.

9. Hypsilophodon 

Waɗannan kuma su ne ƙanana a rukunin girman dabbobin dinosaurs. Tsayinsu (daga kai zuwa wutsiya) ba ya wuce mita 2-2.3. Sun rayu shekaru miliyan 125 da suka gabata a yankunan England, da Spain da United Kingdom.

10. Iguanodon 

Iguanodon suna iya tafiya da ƙafa biyu ko huɗu, suna da matuƙar girma da nauyi. Sun rayu aƙalla shekaru miliyan 140 da suka gabata a yankunan England, da Belgium da United Kingdom. Tsayinsu (daga kai zuwa wutsiya) ya kai mita 10.

11. Maisaura 

Waɗannan nau’in dinosaurs ɗin sun rayu shekaru miliyan 76 da suka gabata a yankin America. Suna da girma, tsayinsu (daga kai zuwa wutsiya) ya kai mita 9. Suna yin ƙwai kamar yadda tsuntsaye ke yi sannan su ƙyanƙyashe su.

12. Plateosaurus 

Plateosaurus sun rayu shekaru aƙalla miliyan 210 da suka gabata a yankin North America, tsakiya da kudancin nahiyar turai da Greenland. Masana bincike kan kayan tarihi suka ce an samu wasu dinosaurs masu kama da plateosaurus da suka rayu a wajajen South Africa da China, haka nan a France, da Switzerland da Germany. Sukan iya tafiya da ƙafa biyu ko huɗu, tsayinsu (daga kai zuwa wutsiya) ya kai mita 7.

13. Spinosaurus 

Waɗannan dinosaurs ɗin da ke da ƙusumbi ko doro a gadon baya da ya kai tsayin (a kwance) mita 1.5, suna da girma kuma sun rayu shekaru miliyan 99 da suka gabata. Masana suka ce girmansu ya fi na giganotosaurus da tyrannosaurus. Tsayinsu (daga kai zuwa wutsiya) yana kai wa daga mita 12-18, sannan daga ƙafa zuwa baya yana kai wa mita 2.5

14. Tuojiangosaurus

Tuojiangosaurus na cikin manyan dinosaurs da suka rayu a gabashin nahiyar Asia shekaru miliyan 155 da suka shuɗe. Suna da girma da doguwar wutsiya, sannan tsayinsu (daga kai zuwa wutsiya) ya kai mita 7, sannan daga ƙafa zuwa baya kuma mita 2.  Masana suka ce tuojiangosaurus suna da dangantakar nau’in halitta da kamanceceniya da dinosaurs ɗin stegosaurus da kuma kentrosaurus.

15. Velociraptor 

Velociraptor sun rayu shekaru miliyan 71 da suka gabata. Masana suka ce waannan dinosaurs ɗin suna matuƙar kama da tsuntsaye, har wasu ma suka tafi kan cewa daga su ne manyan tsuntsaye suka samu. Da yake ba su da girma, tsayinsu (daga kai zuwa wutsiya) ba ya wuce mita 1.8-2. Masana suka ce an fara samun ƙwarangwal ɗin kansu ne a wajajen Mongolia. Abu guda da ya ƙara wa masana haske kan hasashensu na velociraptor a kasantuwar tsuntsaye shi ne irin fiffiken da suke da shi yana matuƙar kama da na tsuntsayen yanzu.

16. Styracosaurus 

Waɗannan na’ukan ma sun rayu shekaru miliyan 75 da suka shuɗe. Irin waɗannan su ne masu matuƙar girma. Sun rayu a nahiyar North America, tsayinsu (daga kai zuwa wutsiya) ya kai mita 8, sannan daga ƙafa zuwa baya ya kai mita 4.

17. Silvisaurus 

Silvisaurus sun rayu shekaru aƙalla miliyan 121 da suka shuɗe a wajajen America. Tsayinsu (daga kafa zuwa wutsiya) ya kai mita 4. Tsarin zubin halittarsu yana matuƙar kama da na kunkure

18. Parasaurolophus 

Sun rayu shekaru miliyan 76 da suka shuɗe a nahiyar North America. Tsayinsu (daga kai zuwa wutsiya) ya kai mita 11 sannan suna da girma da nauyi.

19. Ornithomimus 

Irin waɗannan dinosaurs ɗin dake nau’in Ornithomimus sun rayu shekaru miliyan 120 da suka shuɗe a yankunan North America, Europe da kuma Mongolia. Tsayinsu (daka kai zuwa wutsiya) ya kai mita 3.5.

20. Albertosaurus

Albertosaurus sun kasance kamar wasu ‘yan’uwa ne ga tyrannosaurus saboda kamanceceniyarsu, sai dai nau’insu ba daya ba ne a rukunin nau’ukan dinosaurs. Sun rayu shekaru aƙalla miliyan 70 da suka shuɗe a yammacin North America. Tsayinsu (daga kai zuwa wutsiya) yana kai wa daga mita 9-10.

Sauran waɗanda masana suka gano kuma suka karance su sun haɗa da:

21. Microraptor 

22. Mamenchisaurus 

23. Cetiosaurus 

24. Scelidosaurus

25. Brachiosaurus

26. Giganotosaurus

27. Kentrosaurus

28. Shunosaurus

29. Supersaurus

30. Ultrasaurus

…da suransu. Masana suka ce akwai nau’ukan dinosaurs aƙalla 700 waɗanda suka gano da wadanda ba su gama ganowa ba.

Madogara

[1] Wikipedia.org

[2] Britannica Encyclopedia

[3] National History Museum

[4] DinosaurPictures.org

[5] National Geographic

Mohiddeen Ahmad

Mohiddeen Ahmad

I am Muhammad Auwal Ahmad, an inquisitive student, tech aficionado, science enthusiast and a writer. I am the founder and CEO of Flowdiary.

3 Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *