0

Hasashen Kimiyya 8 Da Suka Faru a Zahiri

Akwai dubunnai hasashen kimiyya da suka faru a rayuwa ta zahiri, waɗanda yawancinsu sun samo asali ne daga ƙirƙirarrun labaran kimiyya da marubuta suka yi ta yin hange a kai a matsayin tatsuniya. Amma a yau waɗannan hasashe na ƙirƙirarrun labaran sun tabbata a rayuwa ta zahiri, kaɗan daga cikin waɗanda za a iya sani a wannan rubutun sun haɗa da:

1. Saƙago

Da abu ne mai wuya a wayi gari wani yayi tunanin kasantuwar saƙagai a rayuwa ta zahiri, amma a yau sun zama ruwan dare a ko’ina a faɗin duniya. Saƙagai suna taimaka wa mutane a wurare da dama, kuma suna da hatsari a wurare da dama. Haƙiƙa rayuwar saƙago da mutane abu ne da ke buƙatar nazari da kula da kuma sanin yadda za a kafa kyakkyawar mu’amala a tsakani.

2. Saƙa-Mutum

Saƙa-mutum shi ne mutumin da aka sabunta ko maye gurbin wasu sassan jikinsa da na saƙago, sannan sai/ko kuma sabunta mutumin sukutum zuwa mataki na gaba. Babu wanda yayi tunanin za a iya yin wannan a zamanin da ya wuce, amma a yau ya faru a rayuwa ta zahiri. Farfesa Warwick yana yi wa kansa kirari da kasancewa saƙa-mutum na farko a tarihin duniya.

3. Kimiyyar Adana Gawa

Duk da a can tsohuwar duniya (a ƙaunin tarihi BCE) ana amfani da ƙanƙara wajen adana gawar mutum don kada ta lalace, amma a wannan zamanin lamarin ya bunƙasa ta yadda ake ajiye gawarwaki da niyyar tada su nan gaba, wato a tada su su dawo suna rayuwa. A duniyar zamani an fara gudanar da wannan kimiyyar ne a shekarar 1967, kuma wani likita da ake ƙira Dr. James Bedford shi aka fara yi wa a wannan shekarar.

4. Kimiyyar Canja/Juya Ƙwayoyin Halitta

Wata kimiyya da ake amfani da ita don canja ƙwayoyin halittar halittu ita ce Genetic Engineering, wacce ta fara aiki tun a gabannin ƙarni na 21. Da taimakon wannan kimiyyar ana iya haɗe ƙwayoyin halittar wasu mabambantan halittu don ƙyanƙyasar wata halitta mafi rinjaye daga cikinsu, ko kuma a samu raba-daidai. Haka nan ana amfani da wannan kimiyyar wajen juya ƙwayoyin halittar ɗan da ke ciki zuwa wani jinsi daban, ko kuma canja wasu sashe a jikinsa ta hanyar daƙile ko canja akalar cells ɗinsa.

5. Ɗan Tafintan Kai-Tsaye

A da can da zaran mutane sun je taro wanda ke haɗa ƙasashe suna shan wahala wajen fahimtar yarukansu, musamman idan taron ya kasance ana gabatar da shi ne da harshen turanci ko kuma larabci a ƙasashen gabas, ko kuma harshen Swahili a nahiyar Africa. Ke nan, wanda ke jin Hausa zalla ba zai iya fahimtar harshen Swahili ko larabci a wurin taro ba, haka nan ba kowa ba ne yake jin harshen turanci ba; musamman ƙasashen da ba su ginu da harshen ba. don haka lamarin taro a ƙasashen waje da musayar harshe yana wahala, amma a yau zuwan fasahar Real-Time Voice Translator tana iya fassara wa mahalarta harshen da wani ke yi a kan dandamali a wurin taro. Zuwan wannan fasaha ya taimaka wa shuwagabanni wajen fahimtar yaren da ba nasu ba a wuraren taro a ƙasashen waje.

6. Tafiya Sararin Samaniya

Tafiya sararin samaniya abu ne da ke da matuƙar wuya, hatsari da fargaba, don haka ta kasance kamar labarin ƙanzon kurege a wajen waɗanda ba su san ta ba ko suke jin labarinta. Amma tun a ƙarni na 20 da lamarin ya tabbata a rayuwa ta zahiri labarin ya canja. A yau matafiya sararin samaniya suna zuwa wasu duniyoyi da ke maƙwabtaka da mu, duniyar wata da sauransu.

7. Ababen Zirga-Zirga Masu Tuka Kansu

Abu ne mai matuƙar wuya a iya ganin mota ko jirgi suna tuƙa kansu, don haka ya kasance kamar wani almara ne a tsohuwar duniya. Amma a duniyar zamani kuma a wannan zamanin, ababen tafiye-tafiye masu tuƙa kansu suna matuƙar ɗaukar hankalin mutane musamman idan aka yi duba da yadda suke kula da kansu a manyan biranen duniya da ke da cunkoso da wuraren da ko mutum ne ke tuƙi sai yayi shakkun shiga. A yanzu haka a biranen duniya kamar America akwai motoci masu tuƙa kansu inda yawanci suke jiran lasisi daga hukuma don fara gudanar da ayyukansu yadda da dace. Ba ma wannan ba, na’urorin drones da suke yawo gida-gida don isar da saƙonni da makamantansu.

8. Fasahar Artificial Intelligence

A shekarar 1950 wani babban masanin lissafi da kuma na’ura mai suna Alan Turing ya gabatar da wani kundinsa, a inda wata jimla take cewa, “shin na’ura za ta iya tunani?” wanda ya janyo hankulan masanan duniya har zuwa wannan lokaci. A fahimtar da aka yi masa na nuna cewa yana hasashen zuwa nan gaba za a iya samun fiƙirar da za a iya sanya wa na’ura don ta yi tunani kamar yadda Ɗan-Adam yake yi. A yau, saboda wannan jimla, an iya ƙirƙirar fasahar Artificial Intelligence da danginsa wacce ta kasance wata fiƙira ce wa na’ura da take ba ta damar yin abu da kanta, tunani, basira da kuma yin wasu abubuwa da mutum ne kawai ke da damar yinsu da makamantansu.

Danna nan don shigar da sunanka ta yadda za ka rinƙa samun rubutunmu a duk lokacin da muka yi sabo.

Mohiddeen Ahmad

Mohiddeen Ahmad

I am Muhammad Auwal Ahmad, an inquisitive student, tech aficionado, science enthusiast and a writer. I am the founder and CEO of Flowdiary.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *