4

Wasu Abubuwa da Za Ka So Sani Game Da Saƙago –‘Robot’

Abunda duniya ta sani game da saƙago a yau shi ne an fara tunanin ƙirƙirarsu a wannan duniyar tun a ƙarni na 19, kamar yadda mutanen da suka rayu a wancen ƙarnin suka yi tunanin saƙagai za su zama ruwan dare a ƙarni na 20. Amma duk da haka, sabon samfurin saƙagai masu tunani da kansu bai ɗauko hanya ba sai a ƙarni na 21.

A duniyar zamani saƙago ya zama ruwan dare ba kamar yadda aka yi tunanin kasantuwarsa a tsohuwar duniya ba. A yanzu har cikin wayoyinmu akwai saƙagai. Akwai su a masana’antu, bankuna, kamfanoni, mahukunta da sauransu. Saƙagai suna taimaka mana a muhimman wurare da muke buƙatarsu.

Shin Me Ka Sani Game Da Su?

1. Al-Jazari Ne Uban Kimiyyar Saƙago

Al-Jazari

Shahararren masanin da ya rayu a ƙarni na 12 mai suna Ismail al-Jazari mutumin ƙasar Turkey shi ake yi wa laƙabi da “The Father of Robotics” saboda muhimman fiƙirorinsa da suka gina fasahar yi-da-kanka wacce a yau ta yi sanadiyyar samar da na’urar saƙago.

3. Saƙago Yana Taimako Kuma Yana Da Hatsari

Babu wanda zai iya hasashen yadda za su iya kasancewa nan gaba

A wurare da dama ana samun iftila’in saƙago, sannan mafi yawancinsu a masana’antu ne, kamar yadda wani saƙago ya kashe ma’aikaci a wata masarrafa a shekarar 1981. Dalili na farko da ya janyo ƙirƙirar saƙagai da fiƙirar na’urar yi-da-kanka shi ne don taimakawa masana’antu wajen gudanar da ayyukansu na musamman. A wannan zamanin kuwa wata kwalejin kimiyya da fasaha a ƙasar Korea ta ƙirƙiri wani saƙago ta sanya masa suna Raptor, wanda yake da tsananin gudu fiye da mutum. Masanan suka ce yana gudun kilomita 46 a sa’a guda. Wannan ya nuna yadda saƙago zai iya zama barazana ga rayuwar Ɗan-Adam.

4.  Asalin kalmar ‘robot’ kalmar Czech ce

Czech yare ne a nahiyar Turai

Kalmar “robot” ta samo asali ne daga “robota” kalmar Czech wacce ke nufin “aikin wahala”. An samar da kalmar ne a shekarar 1920, shekarar da aka fara ƙirƙira wani saƙagon aikin masarrafa kuma a ƙarnin da saƙago ya fara tashe.

5. Akwai Abunda Ake Ƙira Saƙa-Mutum –‘Cyborg’

Transhumanism kuma wata fasaha ce wacce ake tunanin faruwarta zuwa nan gaba

A sashen ƙirƙirarrun labarai, marubutan sun yi hasashe kan yadda saƙago da mutum za su haɗe su zama abu guda, wanda a cikinsu a yau yayi sanadiyyar kasantuwar cyborg. A yanzu kuma ana amfani da sassan saƙago a maye gurbinsa da sassan jikin mutum. Haka nan a yanzu ana kan bincike kan yadda za a iya haɗe ƙwaƙwalwar mutum da ta saƙago, sannan sai wanda kuma zuwa nan gaba za a iya sabunta mutum zuwa mataki na gaba duk ta hanyar amfani da sassan saƙagai. Wani shahararren farfesa da ake ƙira Kevin Warwick ya ce shi ne mutum na farko da ya zama saƙa-mutum da ake kira Cyborg.

6. Hasashen Masana Kan Saƙagai

Akwai hasashen ya iya juyewa zuwa wani abu nan gaba

Masana da dama suna hasashen cewa zuwa gaba saƙagai za su iya mallake duniyar nan ta hanyar yin tunanin kafa tasu ƙasa da daula, da siyasa da sha’anonin rayuwa kamar yadda mutane suka kasance suna yi. Wani masani wanda ya samar da masarrafar saƙago Carnegie Mellon’s Robotics Institute, da ake ƙira Hans Moravec ya ce zuwa nan da shekarar 2040 saƙagai za su samar da nasu nau’in sukutum.

7. Elektro ne Farkon Saƙago A Duniya

Saƙagon Elektro

Da yake akwai saƙagai da dama kuma suna da nau’uka kala-kala, amma saƙagon da aka fara ƙirƙira wanda ya kasance kwaikwayon halittar mutum ne shi ne Elektro, wanda kamfanin Westinghouse ya ƙirƙira a shekarar 1939. Wannan saƙago an shigar masa kalmomi 700 ta yadda yake iya haɗa su yayi magana amma ba mai yawa ba.

8. Akwai Saƙagai Mata

Saƙaguwa Sophia

Mafi yawancin lokuta da mutum ya ji an ce saƙago kawai samfurin maza yake tunawa, amma a yanzu haka a wannan duniyar akwai saƙagai mata da aka ƙirƙira kuma ake kan ƙirƙirarsu. A shekarar 2016 kamfanin ƙirƙirar saƙago na Hanson Robotics ya ƙirƙiri wata saƙaguwa da ake ƙira Sophia, wacce ta kasance mai hazaƙa kuma saƙaguwa ta farko a tarihin duniya da ta taba mallakar katin shaidar zama ‘yar ƙasa. A shekarar 2017 ƙasar Saudi Arabia ta ba wa Sophia katin shaidar zama ‘yar ƙasarta a wani taro da aka gudanar a birnin Riyadh.  Haka nan akwai kamfanoni da suke ƙirƙirar saƙagai mata don wasu manufofi daban, ciki har da ɗebe wa mutane kewa da makamantansu.

9. Ana Amfani Da Saƙagai Wajen Yaƙi

Wani saƙagon yaƙi

Daga cikin hatsarin saƙagai a wannan zamanin shi ne farmakar abokan gaba da yaƙi da su. Ƙasar America kaɗai tana da saƙagai 4,000 da take amfani da su wajen samame da ayyukan sirri don jami’an tsaro da taimaka musu wajen gudanar da bincike da yaƙi. A wani rahoto aka ce tana amfani da su don ƙasashen gabas ta tsakiya da bincike kan tarko da farmaki a akansu musamman inda ayyukan ta’addanci ya yi tsamari. Haka nan ƙasar China, da Japan, da Russia da sauransu.

10. Unimation ne Farkon Kamfanin Saƙago

Unimation

A shekarar 1956 aka samar da farkon kamfanin saƙago da aka sanya wa suna Unimation. A yau akwai ɗaruruwan kamfanonin saƙago a faɗin duniya. Wani rahoto ya ce a shekarar 1990 kuma aka samar da wani kamfanin saƙago mai suna iRobot a ƙ asar America wanda yayi sunan da ya sayar da saƙagai sama da miliyan 20 a faɗin duniya.

11. Dokokin Saƙagai

Dokar Asimov ta farko ita ce kada saƙago ya kashe mutum

Wani marubucin ƙagaggun labarum kimiyya mai suna Isaac Asimov ya gabatar da dokoki kan saƙagai a shekarar 1942, yake cewa:

Dokar saƙago ta farko ita ce ba zai cutar da Ɗan-Adam ba; na biyu dole ya bi umarnin Ɗan-Adam; sannan na uku kuma dole ya kare kansa kuma ya kare mutane matuƙar hakan ba zai saɓa doka ta farko da ta biyu ba.

Madogara

[1] Discovermagazine

[2] Fascinate.com

[3] Mentalfloss.com

Mohiddeen Ahmad

Mohiddeen Ahmad

I am Muhammad Auwal Ahmad, an inquisitive student, tech aficionado, science enthusiast and a writer. I am the founder and CEO of Flowdiary.

4 Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *