
Wasu mutane da suke neman sanin yadda fasahar sadarwan 5G take aiki sun koka kan yadda 5GE yake shige musu duhu, musamman waɗanda suke cin karo da kalmar a yanar gizo.
Mene ne 5G?
5G fasahar sadarwa ce mai tsananin ƙarfi wacce a yanzu haka a duniya ƙasashe kaɗan ne suka yi nasarar ƙirƙira da fara amfani da ita. A shekarar 2010 bayan samuwar fasahar sadarwar 4G aka yi hasashen fara aiki da 5G a shekarar 2020, amma saboda naci ƙasar China da Korea sun ƙirƙire ta kuma sun fara amfani da ita tun a ƙarshen shekarar 2019.
Ko Za Ka Karanta?
Mene ne 5GE?
5GE kuma na nufin “5G Evolution”, kalma ce da kamfanin AT&T ya fara ƙirƙirowa wacce take nufin bunƙasuwar fasahar sadarwar 4G. Wato dai 5GE ba fin 5G yayi ba, shi wani sashin cigaba ne na fasahar sadarwar 4G kawai, kamar yadda ya kasance akwai 3.5G, 2.5G haka nan shi ma 5GE za a iya ɗaukarsa a matsayin cigaban 4G wato 4G LTE.
‘Yan Bambance-bambance
Bambanci | 5G | 5GE |
Sauri | Ya kai 35 Gmps | Ya kai 100 Mpbs |
Jinkiri | milliseconds 1 | milliseconds 5 |
5G | 5GE |
Ya ninka 4G a ƙarfi sau sama da 30 | Ya fi 4G kaɗan |
Yana buƙatar sabbin ƙira, manyan wayoyin zamani | Yana aiki da wayoyin hannu na zamani |
Ƙasashe kaɗan ne suka mallake shi | Akwai shi a kusan ko’ina a duniya |
Bugu da ƙari an ƙirƙiri fasahar sadarwan 5G ne don fasahohin zamani irin su Artificial Intelligence, Machine Learning, Quantum Computers, Robotics, Virtual Reality, Augmented Reality, Internet of Things da sauransu.
Madogara
[1] Forbes.com
[2] Lifewire.com
[3] Wikipedia.com
CSS Dinka da home page ta dauke
Na gode ranka shi dade har na gyara ma