36

Bayani Kan Kasuwancin Kuɗin Lantarki –‘Cryptocurrency’ Da Yadda Ake Yinsa

Mutane da dama suna yawan tambayar ko yaya wannan harkar ta cryptocurrency take kuma yaya ake yinta kasancewar ba ta jima da shigowa wannan zamanin ba. Wannan rubutu zai yi bayani game da ita da yadda za a fara ta.

Menene Cryptocurrency?

Cryptobusiness ko Cryptocurrency a taƙaice kasuwanci ne na canjin kuɗaɗe a yanar gizo ba tare da shigowar wata hukuma ko banki ciki ba, wato canjin kuɗaɗe ne da ake yi tsakanin mai sayarwa da mai saya.

Misali yadda ake canja kuɗaɗen Dala (Dollar, $) zuwa Naira ko zuwa wani kuɗin wata ƙasa daban, haka ake canja waɗannan kuɗaɗe na lantarki zuwa wani kuɗi.

Saboda yawaitar hatsaniya da sauran dalilai, a yanzu ba a buƙatar sai mutum ya je banki kafin ya iya biyan kuɗi a yanar gizo ko ya tura zuwa wata ƙasa, cikin hanyoyin da ake bi na zamani akwai wannan hanyar wacce ta zama ruwan dare a wannan zamanin. Kuɗaɗen lantarki za su ba wa mutum damar musayar kuɗaɗe a yanar gizo ba tare da shigowar wata hukuma cikin lamarin ba.

Rashin shigowar hukuma cikin lamarin ba shi ke nuna cewa ba ingantacce ba ne, haƙiƙa an jima ana wannan harkar kuma yawan damfara yana raguwa ta dalilinta.

Yaya Abun Yake?

Ana sayen waɗannan kuɗaɗe na lantarki don a sayar da su ga wasu duk lokacin da buƙatar hakan ta tashi. Saboda yadda waɗannan kuɗaɗe suke tashi, misali yadda Dala (Dollar, $) take tashi a yanzu, sayenta zai iya zama riba ga mutum – ta yadda za a saya kashegari kuma a sayar musamman idan ta ƙara kuɗi. Haka nan ita ma wannan harkar take.

Ta Yaya Za a Fara?

Kuɗaɗen lantarki na wannan harkar ta cryptobusiness suna da dama, a cikin mafiya shahara sun hada da:

KuɗaɗeAdadin Kuɗin LantarkiFarashin Kuɗi a Naira
BitcoinBTC 0.00005383₦1,000
LitecoinLTC 0.012274₦1,000
EthereumETH 0.001682₦1,000
Bitcoin CashBCH 0.00459₦1,000
RippleXRP 6.10₦1,000

…da sauransu.

Abun ake fara yi da farko shi ne, a matsayin mutum na ɗan-koyo sai ya dubi wanne ya kamata ya fara saya a cikinsu? Sannan kowane akwai tsarukan yadda ake amfani da shi da yadda ake kasuwancinsa. Idan aka ɗauki Bitcoin musamman yadda yake ruruwa kullum a kasuwa, zai fi sauƙin harkar sai dai yana da tsada. A yanzu haka Bitcoin 1 ya kai N18,670,562. Ana lissafinsa da 0.1 zuwa sama. Sannan ana buɗe masa asusu da ake ƙira wallet a shafukan da ake harkar. Haka nan su ma sauran kuɗaɗen lantarkin kamar su Ethereum, Litecoin da sauransu.

Yaya Ake Fara ‘Bitcoin Trading’/‘Cryptobusiness’

Wasu lokutan mutane suna ruɗuwa daga jin sunan Bitcoin Mining, Bitcoin, CMDX, Bitcoin Trading, Cryptocurrency da sauransu. Bari in kore shakkun: duk harkar ɗaya ce, dukkaninsu kasuwancin lantarki ne da ake ƙira Cryptocurrency ko Cryptobusiness sai dai bambancin tsari kawai.

Bitcoin sunan kuɗin lantarki ne. Bitcoin Trading kuma shi ne kasuwancin Bitcoin, yadda ake juya Bitcoin ɗin ya koma riba. Misali idan aka sayi na ₦1,000 yadda za a mayar da shi na N1,500.

To a kullum ina bada shawarar cewa duk abunda za a yi to a yi bincike a kanshi kada a fada kai-tsaye. A nan nake cewa abu na farko da ya kamata a yi tunda an fahimci mene ne Bitcoin kuma mene kasuwancin lantarki wato cryptocurrency, to a ƙara faɗaɗa bincike ta yadda za a ƙara sanin wasu muhimman abubuwa game da lamarin a wurin wasu.

Abu na biyu kuma shi ne buɗe asusu wato wallet, wanda za a rinƙa amfani da shi wajen karɓar kuɗi da tura shi. A Nigeria idan za a yi harkar nan zan bada shawarar ayi amfani da asusun Luno, wanda mutum zai iya sayen kuɗin lantarki kuma ya sayar ko yana kwance a ɗakinsa. Yadda tsarinsu yake shi ne, mutum zai iya neman sayen Bitcoin (ko wani nau’in kuɗin lantarki daban) ta hanyar sayensu da kuɗaɗensa na banki kuma ya biya da katin cirar kuɗinsa. Akwai hanyoyin biyan kuɗi da suka haɗa da biya da Paystack; wanda ya kasance dama ne da ke shiga tsakanin kamfanin da za biya kuɗi da bankin mutum.

GARGAƊI: babu yadda za a iya yi wa mutum sata a asusunsa ba tare da ya ba da haɗin kai ba. Kada wani ya ɗauki lambobin asusunsa ya bayar ga wani face sahihan kamfanoni. A tabbatar wani bai ƙira mutum yace ya faɗa masa lambobin sirrinsa, kuma ya ɗauka ya bayar ba.

Idan ba a gida Nigeria ba ne, ko kuma wani dalili daban akan iya amfani da asusan Coinbase ko na Binance.

Yadda Za a yi Rajista da Asusun Luno.

Kamar yadda na ce asusun Luno yana da sauƙi musamman idan mutum yana son kasuwancin gida Nigeria, sannan yana da wasu alfanu da yake ba wa mutumin da ke amfani da shi. Abunda za a yi shi ne rajista da wannan asusun ta hanyar ziyartar shafinsu na yanar gizo https://www.luno.com wanda daga nan za a shigar da adireshin imel da lambobin sirri, sannan sai su tura saƙo zuwa adirenshin imel ɗin don tabbatarwa.

Bayan an yi rajista da Luno kuma an tabbatar da shaida, abu na gaba shi ne jarraba sayen kuɗin lantarki domin komai sai an jarraba shi a kan dace. Za a iya sayen kuɗaɗen Bitcoin, Litecoin, Ethereum, Bitcoin Cash da Ripple a wajensu kuma a biya kai tsaye cikin sauki.

Sannan kamar yadda wannan hoto na ƙasa ya nuna yadda na buɗe akawunt da asusun Luno, kuma na buɗe asusun Bitcoin (za a iya gani a BTC 0. 000000 a ƙarƙashin kalmar Cryptocurrency)

Bayan an bude akawunt da Luno

Wato duk kuɗin lantarki da za a yi musayarsa (kasuwancinsa) sai ya kasance yana da asusu wato an buɗe masa wallet kamar su Litecoin ko Ripple kamar yadda yake a hoto na sama Add a new wallet (a ƙarƙashin kalmar Cryptocurrency) A hoto na ƙasa kuma an nuna waɗanne kuɗaɗen lantarki ne za a iya buɗe musu asusu wato wallet da Luno:

Bayan an buɗe asusu za a iya shigar sa a inda za a ga babu komai a cikinsa, kamar yadda wannan asusun Bitcoin ɗin yake:

Sannan idan aka danna BUY BTC a hoton da ke sama za a shigo nan inda za a iya saya ta hanyar biyan kuɗi kai-tsaye:

Kamar yadda ake gani a sama, za a iya saya da kuɗaɗen Nigeria (kuɗaɗen mutum na banki) ta hanyar danna NGN Wallet. Sannan a ƙara dannan Top up Wallet kamar yadda ake gani a hoto na ƙasa:

Sannan a nan kuma za a ga yadda za a iya biya ta hanyar amfani da Paystack da katin cirar kuɗin mutum na ATM:

Idan aka shiga sai a shigar da adadin kuɗaɗen da ake so a saya, misali ₦2,000 ko sama da haka. Za a iya sayen na N10 zuwa ₦100,000 a lokaci guda.

Abu na gaba shi ne amfani da code din mutum domin tara kuɗaɗe. Kamar yadda yake a hoton da ke ƙasa, za a iya ganin yadda idan an shiga Rewards inda aka ajiye waɗannan lambobi 9CT93N, kuma a ɗaya gefen akwai Enter a Code, wanda nan ne inda za a sanya code ɗin:

Idan aka sanya waɗannan code ɗin, shi mai asusun (wato wani abokinka da ya gayyace ka) zai samu ₦250 a asusunsa kuma kai ma ka samu.

Don haka idan ka ji daɗin wannan rubutun ka sanya wannan code ɗin nawa a wannan sashe na ENTER A CODE.

Rubutu na gaba zai yi bayani kan yadda za a iya sayar da kuɗaɗen lantarki ga wasu kuma a samu riba sannan a iya amfani da kuɗaɗen. Ci gaba da bibiyarmu a shafim Flowdiary. Shigar da adireshin imel ɗinka a nan don tura maka rubuce-rubucenmu masu zafi a duk lokacin da muka yi.

Mohiddeen Ahmad

Mohiddeen Ahmad

I am Muhammad Auwal Ahmad, an inquisitive student, tech aficionado, science enthusiast and a writer. I am the founder and CEO of Flowdiary.

36 Comments

 1. Alhamdulillah, ngd sosai dama inason na fara cryptocurrency amma dik wadda na tinkara ya koyamin business din sai yana nunamin Bai da lokaci wani ma fadamin dole sai nayi xaman 5-8 months tukunna na iya. Matsala yadda Zanyi business da crypto na iya saya na iya sayarwa.

 2. Masha Allah a gsky naji ddin bayanin nan kuma na gamsu, Kuma insha Allah zanyi registere.saide idan ba damuwa inason numbanka saboda tambaya

  • Slm,nakanta wannan rubutu naka Allah ya saka da alkairi,inason nasiyi Bitcoin kamar yadda kayi bayani anan toh Amma tayaya zan sai dashi idan naci riba kuma Taya zansan naci ribar?

 3. Hakika na dade inason koyan wannan harkar amma rashin sanin ya akeyi ya hanani da kuma rashin sanin wazai koyamin.
  Muna fatan Allah yasaka da alkhairi

 4. MashaAllah laquwata illah billah Allah ya saka ni abin dake hanani shiga irin wannan harka rashin sanin makama da tabbas sannan rashin kudi kamar yadda kudin yake da yasa shiyassa

 5. ALHAMDULILLAH, DAMA IRE-IRENKU MUKE BUKATA A AREWA, SABODA WE ARE LEFT BEHIND MANY THINGS.
  MUNA GODIYA, AMMA INASON INSAN RISK DINDA YAKE CIKIN WANNAN HARKAR DAKUMA YANDA ZA’A IYA KAUCE MASA.
  Thank you.

 6. Masha Allah muna godiya
  Amma ni ATM card dina verve ne to kuma sunce min sai dai visa card kokuma master card
  To tambaya ta itace babu wata hanya da mutum zai iya siya sai ta wannan hanyar.

 7. A gaskiya muna jindadi sosai ALLAH ya kara basira da fasaha da hikima.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *