
Dabbobi sun kasance a nau’uka kala-kala, haka nan kowanne nau’i yana da wasu muhimman abubuwa masu ban mamaki ko ƙayatarwa.
A rukunin dabbobi akwai ƙanana da manya, a inda manya suka kasance mutane; na biyu madaidaitan dabbobi kamar su akuya, shanu, tunkiya giwa da sauransu; sai na uku ƙanana kamar su mage, zomo, da sauransu; sannan kuma mafiya ƙanana daga cikinsu irinsu ƙadangare, kifi da sauransu, sai ƙwari, sannan na karshe kuma su ne tsuntsaye.
Don haka wannan rubutu zai yi magana ne kan wasu abubuwa dangane da dukkanin rukunin dabbobi tun daga ƙanana, madaidaita, mafiya ƙanana, tsuntsaye, ƙwari da sauransu.
1. Ɓera yana dariya idan aka masa cakulkuli
2. Biri yana son shan abunda zai bugar da shi
3. Mage tana yi wa mutane magana da yarenta
4. Giwa tana daidaita kanta duk lokacin da ta totsi ƙahonta
5. Ƙaguwa tana da zuciyoyi 3, ƙwaƙwalai 9, kuma jininta launin bula ne
6. Tsuntsun penguin sun iya soyayya, har kyautar zobe suna yi
7. Dodon Koɗi zai iya bacci har na tsawon shekaru 3
8. Mujiya ta fi kowacce dabba gani da dare
9. Jemage zai iya cin ƙwari 1000 a cikin sa’a guda
10. Kare yana jin ƙamshi/warin abu sau 100 sama da mutane
11. Ƙudan Zuma zai iya fifita fiffikensa sau 200 a daƙiƙa guda
12. Maciji yana haihuwar nau’ukan dabbobi da dama
13. Saniya ta kan iya yin bacci bacci a tsaye, amma mafarki ne sai a kwance
14. Ɗigon dafin baƙin maciji zai iya kashe mutane sama da 100 a lokaci guda
15. Idan sha’awar dabbar ferret ta motsa za ta iya mutuwa don ƙishi idan ba ta samu abokin tarayya ba
16. Dabbobin koalas suna da al’aura biyu-biyu
17. Hawainiya tana iya canja launi a duk lokacin da take so
18. Tsayin harshen hawainiya ya ninka ta sau 2 a tsayi
19. Mage ba ta da ɗanɗanon zaƙi
20. Doki yana iya yin bacci a tsaye
21. Maciji yana iya gani ko ya rufe idanuwansa
22. Wasu nau’in karnuka su kan sumbaci juna
23. Zakanya ta fi fita farauto abinci, ba zaki ba
24. Tattabara ta kan iya yin lissafi
25. Kwaɗo ya kan iya ɗauke wuta ba tare da ya mutu ba
26. Doki yana da hakora 40-42, goɗiya tana da 36-40 kacal
27. Dabbobin koalas suna baccin sa’o’i aƙalla 20 kullum
28. Ƙaguwa ta kan iya jin ɗanɗano da ƙafafuwanta
29. Aku tana da shauƙi kamar mutum; ta kan iya jin farin ciki da saɓaninsa
30. Kada ta kan iya rayuwa har na tsawon shekaru 100
31. Matsatstsaku na da ƙwaƙwalai 32, ciki 10, da marena 18
32. Abu mai zaƙi yana kashe jaki
33. Kare ya ba son abu mai zaƙi
34. Nau’in damisar jaguar ya ninka mutum gani sau 6 musamman a duhu
35. Mage tana tuna sunan da aka sanya mata, amma ba ta son amsawa da shi
36. Malam-Buɗe-Littafi yana iya gane yanayin abinci fiye da mutane
37. Ƙwaƙwalwar maciji ita ce maganin dafinsa
38. Kare gwanin linƙaya ne
39. A kan iya jin kukan zaki ko da tazarar ta kai kilomita 5
40. Ƙwayoyin halittar mutum da na biri nau’in chimpanzee suna kama da kaso 98.8%
41. Damisa ta kan iya yin gudun kilomita 65 a sa’a guda wurin farauta
42. Don tsoro, kare ya kan iya suma idan ya ga kura
43. Raƙumi yana da sufiyan ciki na ajiye ruwa
44. Aku ta kan iya rayuwa har na tsawon shekaru 60
45. Idon maciji yana iya ganin zirin haske da idon mutum ba ya iya gani
46. Idon jimina ya fi ƙwaƙwalwarsa girma
47. Kwaɗo ba ya hararwa, idan kuma ta kama dole sai yayi yana amar da duk kayan cikinsa
48. Jimina da raƙumi sun fi doki gudu
49. Gizo ya kan iya ganin abunda mutane ba sa gani
50. Macen gizo ta kan cinye ‘yan uwanta idan ta ji yunwa, har samarinta ba ta bari
51. Cinnaka ba ya bacci
52. Jinjirin doki zai iya gudu har da tsere bayan sa’o’i kaɗan da haihuwa
53. Cizon gizon-turai ya kan sa gaban namiji ya miƙe
54. Dafin baƙar bazawarar gizo ya fi na na mugun maciji illa sau 15
55. Ko da an fille kan kyankyaso, ya kan iya rayuwa har na tsawon mako guda
56. Kyankyaso ya kan iya tsaida numfashinsa har na tsawon mintuna 40
57. Kyankyaso ya kan iya rayuwa har na tsawon wata guda ba tare da abinci ba
58. Namijin sauro ba ya cizo, macen ce kawai ke yi
59. Mujiya ta na juya kanta ta ko ina
60. Agwagwar swan tana da fiffeke 25,000
61. Mikiya ta kan rayu na tsawon shekaru 70
62. Kifi yana cinye ƙananan kiyaye da ke ruwa
63. Cutar cancer ba ta kama kifin sharks
64. Kadar maɗaura ba ta iya tafiya ta baya
65. Ƙuda ba ya wuce mako 2 a duniya
66. Giwa ta kan ji ƙamshin ruwa ko da tazarar ta kai mil 3
67. Giwa ba ta son ihu ko hayaniya
68. Jimina tana cin ƙarfe
69. Ana amfani da kare don isar da saƙo
70. Macijiyar mesa tana haɗiye mutum
71. A kan samu buhun gero a ramin tururuwa
72. Aku yana fahimtar damuwar iyayen gidansa
73. Wasu lokutan zafin cizon kunama yana ɗaukewa bayan sa’o’i 24
74. Giwa tana shiga damuwa idan ‘yar uwarta ta mutu
75. Don tsananin faɗa, ko walkiya aka yi sai macijiyar tandara ta kai sara
76. Idan jemage ya taɓa ƙasa ba ya iya tashi
77. Ana amfani da tattabara wajen isar da saƙo
78. Kwaɗo ba ya shan ruwa, ya kan tsatso shi daga fatarsa
79. Kada ta na cin dutse
80. Doki ba ya iya hararwa
81. Tattabara ba ta manta inda take duk nisan inda ta je
82. Ko da an cire ko yanke idon dodon koɗi, wani yana iya tsirowa
83. Tsaka ta kan iya yin kowacce irin ƙara
84. Tsaka ta kan iya rayuwa har na tsawon shekaru 20
85. Wasu nau’ukan tsaka ba su da kafa, kamar maciji suke
86. Dorinar ruwa ta kan iya rayuwa har na tsawon shakaru 50
87. Kaza ba ta fitsari
88. Rakumi yana tsoron kunama
89. Jaki yana da matuƙar gardama da izza
90. Wasu matan mikiyoyi su kan fi mazajensu girma da kaso 25%
91. Gizo yana da ido 6
92. Macen aku tana yin kwai 2 – 3 a lokaci guda
93. Jimina ce mafi girman tsuntsuwa
94. Doki ya kan yi gudun kilomita 44 a sa’a guda
95. Raƙumi ya kan yi wata guda bai sha ruwa ba
96. Kowacce hawainiya marainiya ce
97. Saniya kwanar linƙaya ce
98. Kusan kowacce nutsatstsiyar dabba ta na fahimtar maganar mutane
99. Maciji yana tsoron mutum, mutum ma yana tsoronsa
100. Kare yana da juriyar yunwa
101. Don wayo da tsoro, dila ba ta shan ruwa a sunkuye, sai da ta rinƙa tsoma wutsiyarta tana tsotsewa
Madogara
[1] Lovelyplanet.com
[3] Mentalfloss.com
[4] Motherjones.com
[5] Livescience.com
[6] Thefactsite.com
[7] Thedodo.com
[12] Comprehensive Zoology
Kai! Gaskiyar magana Mohiddeen ka cancanci a maka sharhi a wannan rubutu na ka mai matukar alfanu.
Ka yi namijin kokari kwarai da gaske, Allah dai ya taimaka.
In haka ne gaskiya to Allah shi raba mutanenmu da cizon gizon-turai😂. Ga kuma bazawarar macen gizo wacce ba ta da amana sam.
Ameen ya rabbi na gode Malam Abba. Ameen Allah ya raba mu da ciwon bazawarar macen gizo-turai (laugh)
Gaskiya yy kyau muna godiya, Allah y qara basira Aameen.
Ameen na gode Malam Sadiq
Kudos to you.
Godiya muke