2

Annobar Na’ura: Mene ne Worm, Rootkit da Trojan Horse?

Credit: Avast

Lokuta da dama na’urori suna faɗawa tarkon annobar na’ura kamar Malware, Spyware, Ransomware da makamantansu ba tare da sanin mai na’ura ba, haka nan waɗannan ire-iren annobar na’ura kan iya lahanta na’ura ba tare da an lura ba.

Abu mafi kyau da za a yi shi ne fahimtar su da ɗaukan matakan gaggawa kan yadda za a shawo kan su kafin su yi wa na’ura illa, domin rashin yin hakan a karon farko shi ke jefa na’ura da mai ita a halin ha’ula’i.

Ko Za Ka Karanta?

Mene ne Worm?

Worm, wacce aka fi sani da Computer Worm ɗaya ce daga cikin ire-iren Malware da ke shafar wasu na’urori a duk lokacin da ta kasance a wasu na’urori – wato tana ƙoƙarin shiga wasu na’urori ta hanyar yaɗuwa a tsakaninsu. Don wannan dalilin, shiyasa ya kasance abu mafi illa a nuna halin ko-in-kula ga na’ura a lokacin da annobar na’ura ta shafe ta, domin ta waɗannan hanyoyi na Computer Worm da sauram annobar ke shigar su.

Computer Worm tana yaɗuwa ne ta hanyar mu’amala da na’urorin da ba su kamu ba, wato na’urar da ta kamu da wannan annoba tayi mu’amala da wata na’ura da ba ta kamu ba. Hanyoyin mu’amalar su kan iya kasancewa ta hanyar sadarwar yanar gizo, ko Bluetooth, ko Wi-Fi, ko kuma amfani da igiyar caji don musayar fayil. Ke nan ita wannan annoba ita da kanta take ƙoƙarin yaɗuwa zuwa wata na’ura ba tare da sanin su masu na’urorin ba.

Hanya mafi inganci don kare kai daga yaɗuwar irin waɗannan annobar na’ura shi ne ta hanyar amfani da manhajojin rigakafi da ake ƙira Antivirus Software, da manhajojin garun-dole – Firewalls, sannan sai na gaba kuma kulle duk wani fayil da ke ɗauke da bayanai masu muhimmanci.

Ko Za Ka Karanta?

Mene ne Trojan Horse?

A lamarin na’ura mai ƙwaƙwalwa, Trojan Horse na ɗaya daga cikin mafi illolin annobar na’ura a wannan zamanin. Irin wannan annobar na’ura kan iya zuwa a siga da dama, amma babbar manufar maƙirƙiranta bai wuce cutar da na’urar ba. Yadda take shi ne, mutum zai iya amfani da ita ba tare da sanin ita mai cutarwa ba ce, wato tana sajewa ta zo da fuskar wasu manhajojin daban.

A lokuta da dama mutane suna sauƙe manhajoji a na’urorinsu ba tare da sanin sahihancinsu ba, to a irin wannan lokacin Trojan Horse kan iya kasance a ɗaya daga cikin manhajojin da aka yarda da su, sai a sauƙe su a cikin na’ura ba a sani ba. Ita kuma da zaran ta sauƙa a cikin na’ura mutum zai ci gaba da amfani da ita yana tunanin ita ce asalin manhajar da yake so, saboda duk wani tsare-tsare na waccen manhajar akwai su a wannan.

Daga cikin manufofin Trojan Horse akwai leken asiri; za ta iya bin diddigin mutum don satar muhimman bayanansa na sirri musamman lambobin cire kudi a duk sanda yake ciniki a yanar gizo, ko kuma ta shiga cikin na’urar mutum ta nemi duk hanyar da za ta yi don ta cutar da na’urar, ko kuma goge wasu bayanai ko sabunta su, ya dai danganta da manufar maƙirƙiranta.

Don haka yana da kyau a rinƙa samun asalin shafin manhaja da lasisi a kamfaninta kafin a sanya ta a cikin na’ura.

Ko Za Ka Karanta?

Mene ne Rootkit?

Su kuma irin waɗannan annobar na’ura masu kama da Trojan Horse, za su iya kasantuwa a cikin na’ura ba tare da an san suna nan ba, a inda babban burinsu shi ne gurbata duk wani sashe na tsaro a cikin na’ura ta yadda madatsa za su iya shiga wuraren cikin sauƙi. Wato dai Rootkit kan iya zama munafukar manhajar na’ura wacce take rukunin annobar na’ura Malware. Ta kan iya zama a sashina da dama kamar ma’ajiyar fayil da makamantansu.

Madatsan da ke shirin kai hari a cikin na’ura suna amfani da wadannan tsarukan ne ta hanyar turawa mutum su, shi kuma sai ya dauka ingantattu ne ya sanya su a cikin na’urarsa. Saboda yadda zamani ya ci gaba su kan zuwa a siffofi da dama kamar fayil, manhaja da sauransu.

Abu mafi kyau da za a yi don kare kai daga irin wannan lamura na cutar shi ne a rinƙa kula da duk wani sashen sadarwa na na’ura da sanin sahihancin manhaja kafin sanya ta a cikin na’ura. Sannan a kula da sashen sadarwar musayar fayil, kamar ta hanyar sanya igiyar caji da makamantansu. 

Ko Za Ka Karanta?

Madogara

[1] Avast

[2] AVG

Mohiddeen Ahmad

Mohiddeen Ahmad

I am Muhammad Auwal Ahmad, an inquisitive student, tech aficionado, science enthusiast and a writer. I am the founder and CEO of Flowdiary.

2 Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *