1

Ƙoƙarin Masana Kimiyya na Dakatar da Mutuwa da Dawo da Mamaci

Credit: Getty Images

Mutuwa ta kasance wani tashin hankali da mutum yake fuskanta a ƙarshen rayuwarsa. Haka nan mutuwa ta kasance mai yanke zumunci da ƙauna a tsakanin masoya. Don haka halittu sun kasance masu matuƙar ƙinta, saboda ita ke shiga ƙarshen jindadin mutum a duniya.

Duk da haka, duk da cigaban da duniyar kimiyya da fasaha ta samu, mutuwa ta kasance ba ta da magani. Babu wani yunƙuri da ake yi don dakatar da mutuwa ko jinkirta lokacinta. Sannan halittu suna mutuwa ta dalilin cututtuka ba tare da sanadin tsufa ko sai hatsari ba.

A kimiyyance, da zaran numfashin mutum ya tsaya kuma zuciyarsa ta daina bugawa shikenan ya mutu. Babu wani lamari da zai ƙara biyowa, shikenan rayuwarsa ta zo ƙarshe. Haka rayuwa ta fara miliyoyin shekaru da suka gabata, kuma a wannan matakin ake ciki har yanzu. Babu yadda mutum zai yi, yana ji yana gani haka zai mutu.

Ko Za Ka Karanta?

Amma yadda mutane suke mutuwa, sai wasu masana kimiyya suke tunanin hanyar da za su bi don dakatar da mutuwar ko kuma dawo da mutum bayan ya mutu.

Wannan ƙudiri na masana kimiyya ya sa mutane da dama a faɗin duniya ɗaukar wasu lamuran kimiyya, ba ma wannan kaɗai ba, a matsyain tatsuniya ko labarun ƙanzon kurege kawai. Mutane sun yarda cewa babu yadda za a yi a dakatar da mutuwa ko kuma dawo da wanda ya mutu, musamman waɗanda suka kasance suna da addinai.

Mene ne ya faru a ƙarni na 19?

Amma masana kimiyya tun a ƙarni na 19 suke ta yunƙuri kan yadda wannan ƙudiri nasu zai tabbata, kuma ba su duba ƙalubalen da za su fuskanta a cikin ƙudirin ba.

Masana tarihi suka ce, tun a ƙarni na 19 wani masanin kimiyya da ake ƙira Giovanni Aldini yayi amfani da wutar lantarki mai tsananin ƙarfi don zaburar da gawar mutane da ta dabbobi. Yin wannan abun sai ya fahimci yadda mamatan nan suke zabura kamar waɗanda suke raye, amma duk da ya san ba sa raye sai ya sa a ransa cewa akwai wani lokaci da zai zo da masana kimiyya za su iya yin wani ƙoƙari don dawo da mamaci.

A wannan yunƙuri na masanin kimiyya Aldini, an fahimci yadda yayi amfani da wutar lantarki mai tsananin ƙarfi don zaburar da waɗannan mamata. Sai dai abunda wasu masana suka buƙaci sani shi ne, shin wutar lantarki ba za ta iya zaburar da wani abu da ya taɓa rayuwa ba ne ba tare da yin la’akari da kasantuwar rai a jikinsa ko babu ba?

Mene ne ya faru a ƙarni na 20?

Bayan wannan sai a shekarun 1930s lokacin da masanin kimiyyar halittu Robert Cornish ya ce ya yi nasarar tada karnuka biyu da suka mutu, kuma ya shirya don gudanar da wannan aikin a kan mutane. Da jin haka wani mutum a ƙasar ta America ya sadaukar da gangar jikinsa don tabbatar da wannan bincike, amma bayan ya mutu hukumomin jiha suka hana.

Amma yaya lamarin dawo da karnuka biyu da masani Cornish ya yi? Shin mene ne sahihancin bincikensa kuma zuwa nan gaba zai tabbata?

Daga wannan lokaci masan kimiyya da dama a faɗin duniya suka shiga bincike kan wannan lamari da yadda za su tabbatar da shi a zahiri.

Ko Za Ka Karanta?

A game da ƙudirin jinkirta mutuwa, wata kimiyya da ake ƙira Cryonics da ta fara aiki a shekarar 1967 na ƙoƙarin sanya mutum a cikin ƙanƙara ta yadda babu wani abu da zai same shi, zuwa nan gaba kuma a tada shi. Wato lamarin ya tafi ne kan cewa za a sanya mutum cikin ƙanƙara a ɗauke masa numfashi da zai kasance kamar a mace, zuwa nan gaba kuma a iya tada shi.

Dangane da shekarar da kimiyyar ta fara aiki kuwa (1967), shi ne kasancewa shekarar da aka fara gudanar da wannan lamari inda wani likita da ake ƙira Dr. James Bedford ya kasance mutum da farko da aka fara sanyawa a cikin ƙanƙara.

Masana kimiyyar suka ce wannan yunƙuri zai yi aiki ne musamman ga mutanen da suke gangaren mutuwa saboda wata cuta da ba a gano maganinta yanzu ba, zuwa nan gaba idan aka gano maganin sai a tashi mutumin a yi masa magani ya warke.

Suka ƙara da cewa, haka nan zuwa nan gaba idan aka samu ilimin da za a iya tada mamaci zai kasance lokaci na musamman don gudanar da aikin tadarwan, saboda mutuwa ba ita ba ce ƙarshe.

Mene ne ya faru a ƙarni na 21?

Amma a ƙarni na 21 masana sun ƙara faɗaɗa bincikensu wajen cim ma wannan manufa ta musamman. Sannan sun yi ƙoƙarin danganta lamarin da fasaha ta yadda za ta iya ba wa kimiyyar gudummawa ta musamman wajen cim ma ƙudirin.

A game da kimiyyar Cryonics, a yanzu haka a ƙasar America, akwai mutane aƙalla 200 da aka sanya a cikin ƙanƙara waɗanda ake tunanin zuwa nan gaba za a dawo da su raye, sannan sama da 1000 kuma an yi yarjejeniya da su cewa bayan sun mutu su ma a sanya su.

Wani kamfani da ke gudanar da wannan lamari mai suna Alcor Life Extension Foundation ya ce, “mutuwa ba ita ba ce ƙarshe, mutuwa ba ta nuna cewa mutum ba zai ci gaba da rayuwa ba. Tabbas akwai buƙatar dawo da mutum bayan ya mutu, ilimin nan gaba ne zai tabbatar da haka”

Shin wannan sanya mutum da ake a cikin ƙanƙara don a tashe shi zuwa nan gaba zai tabbata gaskiya kuwa? Masanan suka ce ba su cire rai zuwa nan gaba su iya tada mutanen da suka mutu ta wannan hanyar ba, kamar yadda wanann kamfani shi ma ya yi bayani.

Ko Za Ka Karanta?

Sannan a shekarar da ta gabata ta 2020 cikin watan April, na yi wani rubutu a dandalin sada zumunta na Facebook kan wani matashi da ake ƙira Josh Bocanegra, wanda ƙudirinsa shi ne dawo da mamaci da kuma dakatar da mutuwa. A nan na kawo wasu muhimman bayanai game da ƙudurin wannan matashi da yadda zai kasance.

“Bocanegra ya ƙirƙiri kamfanin bincike ya sanya masa suna Humai, sannan ya zuba masana kimiyya daga fannoni da dama don gudanar da bincike kan wannan ƙudirin nasa. A bayaninsa ya ce yana so ne lamarin ya kasance yadda za a iya sauƙe bayanan ƙwaƙwalwar mutum a zuba a na’ura ta yadda za a ƙara ɗaukar bayanan a zuba a ƙwaƙwalwar saƙago.”

Daga ƙarshe dai aka gano gaba ɗaya ƙudirin wannan matashi ya tafi ne kan yadda za a iya amfani da ƙwaƙwalwar mamacin don sarrafa bayananta a cikin na’ura; wanda wannan shi ne ƙudirin Elon Musk na Neuralink, a inda gaba ɗaya abun ya ta’allaka ga hasashen fasaha na Technological Singularity, wanda ake tunanin faruwarsa nan da shekaru 25 zuwa 30.

Ko Za Ka Karanta?

Me ke shirin faruwa nan gaba?

Wannan ƙudiri na matashi Josh Bocanegra wanda ya ta’allaka ga yin amfani da bayanan ƙwaƙwalwar mutum don a ɗaura wa na’ura ta yadda wannan na’urar za ta maye gurbin mamacin, shi ne abunda yake shirin faruwa nan gaba.

Masana kimiyya da fasaha ta kowanne ɓangare a halin yanzu suna ƙoƙari kan wannan ƙudiri saboda an jingina shi da fasaha wanda ake tunanin zai iya zama a rayuwa ta zahiri.

Shin hakan mai yiwuwa kuwa?

Ko Za Ka Karanta?

Madogara

[1] Live Science

[2] BBC News

[3] Alcor Life Extension Foundation

Mohiddeen Ahmad

Mohiddeen Ahmad

I am Muhammad Auwal Ahmad, an inquisitive student, tech aficionado, science enthusiast and a writer. I am the founder and CEO of Flowdiary.

One Comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *