4

Yadda Wani Matafiyin Sararin Samaniya Ya Yi ‘Time Travel’

Credit: New Atlas

Har yanzu mutane da dama suna ɗaukar hasashen kimiyya na time travel a matsayin tatsuniya, amma abunda masana ke ƙoƙarin tabbatarwa shi ne sanin waɗanne matakai ake bi domin gudanar da time travel da kuma irin abubuwan da za a fuskanta.

Duk da ya kasance hasashe, amma hakan bai hana shi faruwa a rayuwa ta zahiri ba kuma a wannan zamanin na sabuwar duniya.

Shin Mene ne Time Travel?

Time travel wani hasashen kimiyya ne da ke nuna yadda mutum zai iya yin tafiya domin tsallake wani zamani, kamar gudanar da wata tafiya zuwa sararin samaniya domin a tsallake wani zamani.

Ko Za Ka Karanta?

Me Ya Faru?

A shekarar 2015 wani matafiyin sararin samaniya mai suna Gennady Padalka ya dawo daga sararin samaniya bayan shafe kwanaki 879 a can. Ba a wannan lokacin ne kawai ya taɓa zuwa sararin samaniya ba, amma wannan ya kasance lokaci na shida da ya je sararin samaniya don gudanar da wani muhimman ƙudirinsu na kimiyyar sararin samaniya.

Wani masanin kimiyya a jami’ar Princeton ya ce, “lokacin da matafiyi Padalka ya dawo daga sararin samaniya, ya fahimci yadda duniyar Earth ta canja da kaso 1% cikin 44% na inda yake tunanin za ta riska”

Wato a shekaru biyu da watanni biyar da matafiyin nan ya ɓata a sararin samaniya, ya fahimci wasu canje-canje ‘yan kaɗan a duniyar da ya bari ta Earth.

Abunda za a ƙara fahimta a nan shi ne, yin time travel ya danganta da inda aka je da kuma yanayin tafiyar da aka yi. Masana dai cewa suka yi kafin a iya yin time travel dole sai an samu wani jirgi na musamman da ke da damar yin irin wannan tafiya, ana ƙiranshi time machine.

Yadda tsarin time machine yake shi ne, zai iya yin gudu kamar gudun haske, saboda masani Albert Einstein cewa yayi kafin a iya yin time travel dole sai an samu abunda zai yi gudu kamar gudun haske. Sai dai har yanzu duniyar kimiyya da fasaha ba ta kai wannan mataki na ƙirƙirar irin wannan jirgin ba

Ko Za Ka Karanta?

Ba a nan time travel kawai ya tsaya ba, ɗayan ɓangaren nashi na nuna yadda za a iya komawa zamanin da ya wuce ta yadda mutum zai iya fahimta a zahirance game da wasu abubuwa da suka faru a baya da kuma yin zamani kamar a bayan.

Shin hakan mai yiwuwa ne kuwa?

Ko Za Ka Karanta?

Madogara

[1] Popular Mechanics

Mohiddeen Ahmad

Mohiddeen Ahmad

I am Muhammad Auwal Ahmad, an inquisitive student, tech aficionado, science enthusiast and a writer. I am the founder and CEO of Flowdiary.

4 Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *