0

Yadda Masana Kimiyya a China Suka Ƙirƙiri Kwaikwayon Halittar Rana da Wata

Tun a shekarar 2018 masana kimiyya a ƙasar China suka sanar da ƙudirinsu na ƙirƙirar kwaikwaiyon halittar wata don maye gurbin fitulun da suke haska ƙasarsu da dare. Masanan suka ce ta wannan hanyar za su iya rage yawan kashe kuɗaɗen da ake yi wajen sayen mai da kula da fitilun da ke kan titi. A wancen lokacin sun shirya tsaf kan yadda wannan ƙudirin nasu zai fara aiki a shekarar 2020.

Credit: Live Science

Masanan suka ce a birnin Chengdu kaɗai ana kashe kimanin dala miliyan 170 duk shekara na kuɗin lantarki, idan suka samu nasara kan wannan ƙudirin nasu zai rage yawan wannan kashe-kashe maƙudan kuɗaɗen.

Haka nan a wannan shekarar kuma ƙasar ta China dai take ta yunƙurin ƙirƙirar kwaikwayon halittar rana, wacce za ta iya amfani da ita don maye gurbin rana don amfani da wasu sinadarai da kuzari da makamantansu.

Kasar Korea ma tana kan gaba wajen samar da irin wannan kwaikwayon halittar ranar, inda a yanzu aka kai matakin da take da zafin da zai kai ma’aunin Celsius miliyan 100. Sannan masana kimiyyar suna ƙoƙari ne wajen ƙara ƙarfin da zai wuce haka.

Ta kasar China kuwa HL-2M Tokamak, wanda tuni ta fara aiki tun a ranar 4 ga watan December na shekarar 2020, yanzu haka zafinta ya kai ma’aunin Celsius miliyan 150.

Credit: Getty Images

Wannan kwaikayon halittar rana da suka ƙirƙira za ta yi aiki ne don inganta Nuclear Fusion dinsu, da kuma wasu sassan bangarorin cigaba, wanda ake tunanin zai ƙara haɓɓaka musu tattalin arzikin kasa.

Madogara:

Global News

The Indian Express

Mohiddeen Ahmad

I am Muhammad Auwal Ahmad, an inquisitive student, tech aficionado, science enthusiast and a writer. I am the founder and CEO of Flowdiary.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *