5

Kimiyya Da Fasaha: Wanne ne Mafi Hatsari ko Cigaba?

(c) Shutterstock.com

Kimiyya da fasaha, waɗannan sashinan biyu sun kasance daban tun farkon kasantuwarsu har zuwa duniyar zamani a yau, saboda yadda suke  ƙoƙarin sabunta abubuwa da kuma kawo sabbi a duk wasu lamura na rayuwar yau da kullum. Haƙiƙa waɗannan sashinan sun taka muhimmiyar rawa wajen zamanantar da al’amuranmu a wannan duniyar.

Idan ka dubi yadda duniyar yau ta canja ta hanyar zamanantar da ita da waɗannan sashinan suka yi, za ka fahimci irin rawar da suke takawa wajen kawo cigaba da zai sauƙaƙa wa mutane yadda suke gudanar da al’amuransu na yau da kullum. Daman manufar kimiyya da fasaha a duk wani yanayi shi ne sauƙaƙa wa mutane yanayin gudanar da al’amuransu, da kuma kawo sababbin cigaba wanda wataƙila ba a taɓa ganinshi a rayuwa ta zahiri ba.

A fannin kimiyya, a yau an ci gaba da har ta kai ga an manta wasu wahalhalun da aka sha a baya. Misali fannin likitanci, ko fannin magani, ko bincike da sauransu.  A ɓangaren fasaha kuma za a iya ganin yadda na’ura mai ƙwaƙwalwa take canja rayuwar yau da kullum. Misali yanar gizo, tafiye-tafiye kamar jirage da motoci, sadarwa, kasuwanci da sauransu. Ke nan a duniyar yau duk wani lungu da saƙo na harkokin rayuwa babu inda kimiyya da fasaha ba su shiga ba don kawo sauyi na cigaba da kuma sabunta wani tsari da ake yinshi a da.

Amma duk da haka, wasu suna ganin wadannan sashinan a matsayin masu cutarwa ko hatsari ga rayuwar Ɗan-Adam, musamman idan suka duba hasashen cigaban da ake yi wanda waɗannan sashinan za su kawo. Misali, a ɓangaren manyan fasahohin zamani ana tunanin nan gaba na’ura za ta iya samun ƙarfin mallakar hankali na karan kanta, da za ta iya yi wa mutum juyin mulki. Haka nan wasu suka yi tofin ala-tsine ga masana kimiyyar da suke ƙirƙirar cuta su yaɗa ta a cikin al’umma, sannan sun nuna hakan a matsayin cigaban mai tonon rijiya.  

A ɓangaren zamanantar da duniya zuwa mataki na gaba, waɗannan fannoni na kimiyya da fasaha sune kan gaba wajen gudanar da wannan aiki. Masana suka ce duniya za ta iya zama kamar a tafin hannun mutum da zaran ta shiga mataki na gaba saboda cigaban da zai zo zai sha bamban da wanda ake gani ko tunaninsa a wannan zamanin.

A wannan mataki da muke ciki, wanne ne kake tunanin zai kasance mafi cigaba ko hatsari a duniyar zamani; kimiyya ko fasaha?

Mohiddeen Ahmad

Mohiddeen Ahmad

I am Muhammad Auwal Ahmad, an inquisitive student, tech aficionado, science enthusiast and a writer. I am the founder and CEO of Flowdiary.

5 Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *