1

Hikimar Rumbun Bayanai – ‘Database’ da Amfaninsa a Duniyar Zamani

rumbun bayanai database
‘Database’ -Rumbun Bayanai

Kafin wannan zamanin na na’ura mai ƙwaƙwalwa da fasaha, an kasance ana adana bayanai ne a littatafai –wato a rubuta bayanai a adana su a ɗakin karatu. Idan suka kasance masu matuƙar muhimmanci sai a yi musu kundi sukutum a adana a ciki, a nemi wani ɓoyayyen wuri mai tsaro a ajiye musamman cikin akwatin ƙarfe.  

Cikin waɗanda aka sani da irin wannan ɗabi’a, da kuma karance-karance da rubuce-rubuce, da anada kayan tarihi, da ƙoƙarin neman wayewa akwai tsohon birnin Egypt, da masana falsafar Girka da kuma Babiloniyawa. Waɗannan jerin al’umma ba tsohon tarihi kawai suke da shi ba, amma sun kasance jagorori a tafiyar da duk wani lamari na ƙoƙarin wayewa ta hanyar karatu da rubutu a tsohuwar duniya.

Ko Za Ka Karanta?

Amma kaɗan-kaɗan sai aka fara sabunta tsarin adana bayanai, aka samu tsarin binciko bayani cikin sauƙi a ɗakin karatu ta hanyar bin wasu bayanai. Misali, samun tsarin bibliography ta yadda binciko bayanai a ɗakin karatu zai yi sauƙi ba tare da shan wahala ba, ana ƙiran sa bayanin bayanai.

Bayan duniya ta ci gaba kuma an shigo duniyar zamani ta na’ura mai ƙwaƙwalwa da fasaha, sai aka fara zamanantar da tsarin gudanar da adana bayanai, misali a shekarar 1960 kamfanin IBM ya fara ƙirƙira wa kamfanin Sabre rumbun bayanai, wanda zai taimakawa hukumar zirga-zirar jirage don adana bayanan matafiya. Wannan rumbun bayanai ya kasance na farko da ya shahara a kasuwa.

A shekarar 1970 wani masani E.F. Codd ya gabatar da kundinsa wanda ciki da yake nuna yadda za a zamanantar da rumbun bayanai, wanda hakan ta kai ga samun babban cigaban ƙirƙiro rumbunan bayanai a shekarun 1970s, kamar su SQL a 1974, MS SQL Server a 1989, Oracle a 1979 da sauransu. Sannan a shekarar 1992 kuma aka samu MS Access.

Ko Za Ka Karanta?

Iren-iren Rumbun Bayanai

Sai dai akwai ire-iren rumbun bayanai waɗanda ake amfani da su a wurare da dama. Waɗannan sun haɗa da:

1. Hierarchical Database

Irin wannan rumbun bayanan shi ne yake bin mataki-mataki don dacewa da rukunin da aka ɗaura shi a kai. Wato tsarin wannan rumbun bayanan shi ne wanda ake tsarawa bisa matakin girma; misali a tsarin gwamnati akwai shugaban ƙasa, mataimakin shugaban ƙasa, shugaban majalisar dattawa da sauransu, sannan duk wani ɗan majalisar tarayya yana ƙarƙashin ofishin shugaban majalisar dattawa ne ba shugaban ƙasa ko mataimakinsa ba. Kamar yadda yake a hoton da ke ƙasa, an nuna yadda tsarin jami’a yake:

Photo: GeeksForeeks.org

2. Network Database

A irin wannan rumbun bayanan kuma, yawanci sashinan suna da alaƙa da wasu –wato ace ɗan majalisar tarayya yana da alaƙa da ɗan majalisar jiha da wakilin jiha. Ke nan, ana duba sashi mafi muhimmanci da zai kasance yana da alaƙa mai kusanci da sauran sashinan. Wannan dalilin ya sa sunan rumbun bayanan ya kasance a haka –network, saboda yadda sashina suke da alaƙa da juna. Kamar yadda yake a hoton da ke ƙasa, an nuna yadda sashinan tsangaya da na dalibai  ke da alaƙa da sauran:

Photo: GeeksForeeks.org

3. Object-Oriented Database

Shi kuma wannan rumbun bayanan yana ba da damar yadda za a iya tsara bayanai bisa tsarin da zai yi kama da bayanin, don haka za a iya shiga bayanin ta hanyar tattaro tsarin bayanin da ya ta’allaƙa da bayanin da aka sanya. Misali, a wannan hoton da ke kasa za a iya ganin yadda tsarin bayanin mutane ya nuna gurbin bayanansu kamar sunaye, da lambobin waya da adireshin imel; haka nan wannan sashin mutane ya ƙara raba wasu ƙananan sashina na farfesoshi da ɗalibai, saboda duk bayanin da za a sanya a cikinsu na mutane ne.

Photo: GeeksForeeks.org

4. Relational Database

A yanzu kuma yadda duniya ta ci gaba, kusan duk wani rumbun bayanai da wannan tsarin yake amfani, saboda yadda yake da sauƙin gudanarwa da kuma ba da dama wajen ajiye komai a muhallinsa. A wannan rumbun bayanan duk wani bayani yana da dangantaka da gurbin bayanan, ta yadda da zaran an buƙaci neman wani abu za a iya samun sa cikin sauƙi. Haka nan kamar yadda tsarinshi yake na jadawali ya sa ya kasance mai sauƙin gudanarwa. A hoton da ke ƙasa za a iya ganin yadda gurbin bayanai na lambobin ɗalibai, da sunayensu, da makin ɗin da suka samu suka ta’allaƙa ga gurbin bayanansu.

Photo: GeeksForeeks.org

Duk wani rumbun bayanan da ya shahara kuma ake amfani da shi a duniya yanzu yana a tsarin Relational Database ne. Misali, rumbunan bayanai MS Access da MySQL, za a iya ganin yadda tsarinsu ya kasance a ƙasa:

MS Access:

rumbun bayanan database din Microsoft access
MS Access Database

A wannan rumbun bayanan an nuna yadda aka adana bayanan mutane daki-daki, kuma kowanne bayani ya ta’allaƙa da gurbin bayaninsa –wato Name, Phone, da Date of Birth kamar yadda yake a hoton.

MySQL

MySQL Database

Haka nan a rumbun bayanan MySQL ma an nuna yadda aka adana bayanai daki-daki a ma’adanarsu.

Idan mun fahimci rumbun bayanai za mu san cewa shi ne ma’adanar bayanai da aka zamanantar a cikin na’ura, wanda za a iya shiga a ajiye bayanai kuma a iya sabunta su nan gaba. Duk wani bayani da ke gudana a yanar gizo haƙiƙa ana adana shi a cikin rumbun bayanai ne. Kuma rumbun bayanan da ake amfani da shi wajen adana da sarrafa bayanai a duniyar zamanin nan shi ne Relational Database.

Sannan wasu abubuwa da za a iya sani dangane da rumbun bayanai da tsarinsu sune kamar haka:

1. Database – da farko dole za a ƙirƙiri sabon rumbun bayanai da sanya masa suna don adana bayanan da ake so a cikinsa. Kamar yadda yake a hoton da ke sama na misalin rumbun bayanan MySQL, za a ga yadda sunan rumbun bayanan ya kasance shafinmu.

2. Table – misali, yadda ake adana littatafai a ma’ajiyarsu, ana tsara su ne daki-daki yadda da zaran an zo neman wani littafi na wani fanni za a iya samun sa cikin sauƙi a fanninsa, wato ba a haɗa littatafan da ke mabambantan fannoni a wuri ɗaya. To haka lamarin jadawali yake a rumbun bayanai, kowane bayani yana da nashi ma’ajiyar. Kamar yadda yake a hoton da ke sama a misalin rumbun bayanai MS Access, za a iya ganin yadda sunan jadawalin ya kasance table_bio; wato bayanan mutane ne kawai a cikin wannan jadawalin. Haka nan a hoton da ke sama na misalin rumbun bayanai MySQL, za a iya ganin yadda jadawalin ya kasance blog; shi ma kenan duk bayanan da ke cikinsa na rubutu ne ba na mutane ba.

3. Column – wannan kuma shi ne gurbin bayanai. Duk wani bayani da za a adana a rumbunsu sai sun kasance suna da gurbi a cikin rumbun bayanan nan, domin ta haka ne za a iya sanin bayanin da me ya ta’allaƙa kuma bayanin mene ne. A wannan hoton da ke kasa za a ga yadda bayanai ba su kasance da gurbinsu ba, don haka waɗannan bayanan ba su da ma’ana don ko na’urar ba za ta iya sanin akan me bayanan suka ta’allaƙa ba.

Yanzu za a fahimci cewa domin adana bayanai a rumbunsu dole sai an ƙirƙiri rumbun bayanan, jadawali da kuma gurbin bayanan domin tsara yadda bayanan za su kasance a jere.

Madogara:

GeeksForGeeks.org

Wikipedia.org

QuickeBase.com

Mohiddeen Ahmad

Mohiddeen Ahmad

I am Muhammad Auwal Ahmad, an inquisitive student, tech aficionado, science enthusiast and a writer. I am the founder and CEO of Flowdiary.

One Comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *