4

Hatsarin Tafiya Sararin Samaniya

Tafiya sararin samaniya ta kasance tafiya mafi hatsari da Ɗan-Adam ya taɓa riska a duk yawace-yawacenshi a faɗin ƙaunu. Tafiya ce wacce, ko da an san inda za a tsaya, to ba a san me za a tarar a wurin ba. Haka nan tafiya ce wacce ba a yada zango don hutu, ko kuma a dakata a sayi abinci ko a yi ibada kamar yadda aka saba yi a wannan duniyar. Haƙiƙa tafiya sararin samaniya ba ta kasance tafiya mai sauƙi ko mai dadi ba. tafiya ce wacce ake yin ta da fargaba gami da tsoro don babu wanda zai iya hangen wani abu da zai iya faruwa ga matafiyan.

Ko Za Ka Karanta?

A duk lokacin da aka so tafiya sararin samaniya mutane da dama suna ƙoƙarin sanin waɗanne matakai ne ake bi kafin gudanar da tafiyar, ko kuma ƙoƙarin sanin dalilin tafiyar. Amma wasu lokutan kuma an fi duba hatsarin tafiyar, shiyasa mafi yawan lokuta mutane suke sarewa, wasu ma su ƙaryata tafiyar duba da yadda suke jin labarinta, wasu su kan ɗauki lamarin ne kawai a matsayin labaran ƙanzon kurege.

Tabbas ana tafiya sararin samaniya, amma tafiyar ba ta kasance mai sauƙi ba. Mutane da dama sun rasa rayukansu a wannan tafiya, wasu sun ɓata, wasu kuma sun yi nadamar tafiyar da suka yi. Waɗanda suka tsira kuma a yau su suke ba da labarin abunda suka gano a can.

Amma ko kasan idan aka yi tafiya zuwa sararin samaniya ina ake zuwa?

Mutane da dama sun ɗauka wasu duniyoyi kawai ake zuwa, ko kuma duniyar wata da makamantansu. Amma sai dai ba duniyoyi kaɗai ake zuwa ba, ana zuwa wurare da dama. Abunda kuma mutane da dama ba su sani ba shi ne, lokuta da dama da an yi tafiya zuwa sararin samaniya kawai ana shawagi ne a sararin samaniyan a dawo, musamman idan aka je gudanar da wani bincike.

Ko Za Ka Karanta?

Tafiya sararin samaniya tana da ɗan dogon tarihi kamar yadda masana suka nuna. Sai dai abunda yake a zahiri kuma wanda aka tabbatar a tarihi shi ne an fara zuwa sararin samaniya ne a wani zamani da ake ƙira Space Age, a ƙarni na 20. Zamanin Space Age shi ne zamanin da aka fara zuwa sararin samaniya. Wannan zamani ya fara daga shekarar 1957 har zuwa yau ɗin nan, lokacin da aka harba jirgin Sputnik sararin samaniya.

Ko Za Ka Karanta?

Sararin samaniya ba ta kasance kamar wannan duniyar ba, akwai wasu abubuwa da akwai a nan amma a can babu, haka nan akwai a can amma a nan babu. Waɗannan bambance-bambance suna daga cikin abubuwan da masana suke la’akari da su, sannan suna daga cikin abubuwan da suke da hatsari matuƙar ba a ɗauki matakin da ya dace a kansu ba, kamar:

1. Yanayi – yanayin da ke a sararin samaniya daban ne da wanda ake fuskanta a duniyar Earth. Misali a shekarar 1986 jirgin Challenger ya tarwatse bayan daƙiƙu 73 kacal da tashinsa, sanadiyyar yanayin sanyi da ake ciki da yayi sanadin fashewar wani sashi a jikin jirgin har ya fara fitar da gas mai tsananin zafi.

2. Iska – haka nan iskar da halittu masu rai suke shaƙa daban ce da wacce take a sararin samaniya, hasali ma dai a can babu wata iska makamanciyar wannan. Don haka wannan shi ma ya kasance wani hatsari da mutum zai iya fuskanta domin ba zai iya rayuwa ba tare da shaƙar iska ba. A shekarar 1967 matafiyan Apollo 1, Edward White II, da Roger Chaffee, da Gus Grissom suka rasa rayukansa sanadiyayyar rashin shaƙar iska, saboda wutar da ta mamaye jirginsu.

Ko Za Ka Karanta?

3. Lokaci – yanyin lokacin da ke tafiya a wannan duniyar daban yake a sararin samaniya, kuma hakan ya ta’allaƙa ne ga lokaci-da-wuri da masana suke gina nazariyyoyi a kai, ciki har da shahararriyar nazariyyar dangantaka ta masanin kimiyya Albert Einstein.

Ko Za Ka Karanta?

4. Jirgi – abu na farko da ake yawan samun hatsari da shi a tafiya sararin samaniya shi ne jirgi. Hatsarin jirage a sararin samaniya yayi sanadiyyar halakar rayuka da dama.  

5. Hanya – babu wata hanya a tafiya sararin samaniya face sarari marar iyaka. Babu wani wuri da za a iya fakewa don a yada zango ko makamancin haka. Akwai abubuwa da dama da suke shawagi a sararin samaniya waɗanda suka kasance masu matuƙar cutarwa, amma sai dai babu wani yunƙuri da za a iya yi domin kauce musu.

Ko Za Ka Karanta?

6. Tafiya – a gabannin tafiya sararin samaniya ana shirya manufa da dalilin tafiyar. Sannan ana tsara wane wuri za a je kuma a ina za a dira, kuma yaushe.

7. Dawowa – wasu mutanen ma a hanyar dawowa gida suke rasa rayukansu, kamar yadda matafiya sararin samaniya Vladislav Volkov, da Viktor Patsayev, da Georgi Dobrovolski suka rasa rayukansu a shekarar 1971.

Ko Za Ka Karanta?

8. Ziri – wataƙila wani ziri a can ya kasance mai cutarwa ga lafiyar Ɗan-Adam. Duk da mutanen da ke tafiya sararin samaniya suna rufe jikinsu da kaya masu kauri haɗe da iskar shaƙa da sauran abubuwan buƙata, amma duk da haka wani zirin zai iya kasancewa mai ƙarfin gaske da zai iya tsaga jikin mutum.

9. Maganaɗiso – abu na gaba da masana suke duba a kai shi ne maganaɗiso. Wato kowane wuri a faɗin ƙaunu akwai yanayin yadda maganaɗisoshi yake. Wataƙila wurin da za a je akwai ƙarfin maganaɗiso mai rinjaye sosai, wasu wuraren kuma babu.

Ko Za Ka Karanta?

10. Guzuri – duk wani yunƙuri da mutum zai yi sai ya kasance yana cikin ƙoshin lafiya. Game da abinci ko magani, wataƙila a sararin samaniya wannan guzuri ya iya zama mai guba, don babu tabbacin waɗanne irin guba ne a can kuma yaya suke cutar da halittu masu rai. A shekarar 1955 matafiyan Apollo-Soyuz suka gamu da guba da suka shaƙa ta sinadarin nitrogen tetroxide a sararin samaniya. Amma bayan sun dawo gida suka fara fuskantar shaƙewar numfashi, sai da aka yi musu aiki a asibiti.

Mujallar Astronomy ta ce sama da mutane 20 ne suka rasa rayukansu, da dama kuma suka jikkata sanadiyyar tafiya sararin samaniya. Sai dai da dama da suka mutu suna gamuwa da ajalinsu ne a yayin gwaji.

Ko Za Ka Karanta?

Madogara:

Astronomy.com

FacificPrime.com

Wikipedia.org

BBC Space

Mohiddeen Ahmad

Mohiddeen Ahmad

I am Muhammad Auwal Ahmad, an inquisitive student, tech aficionado, science enthusiast and a writer. I am the founder and CEO of Flowdiary.

4 Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *