1

Muhimman Abubuwa 7 Game da Duniyar ‘Saturn’

duniyar saturn
Duniyar Saturn

Abunda mutane suke fara tunawa a duk lokacin da aka ƙira sunan duniyar Saturn shi ne zobenta. Wato tuna yadda zobe yayi wa duniyar ƙawanya. Duniyar Saturn ta kasance ƙaya daga cikin duniyoyi takwas da suke a tsarin hasken ranarmu –wato Solar System dinmu da ya kasance a gungun taurarinmu Milky Way.

Ko Za Ka Karanta?

Wasu muhimman abubuwa 7 da za mu iya sani dangane da duniyar Saturn sun haɗa da:

1. Zobe – ba duniyar Saturn ba ce kaɗai ta ke da zobe, haƙiƙa akwai wasu duniyoyi da suke da zobe ba Saturn kadai ba, amma dalilin da ya sa aka san na duniyar Saturn din shi ne, ana iya hango shi daga duniyar Earth, ba kamar sauran ba. A ƙalla akwai zubbai sama da 30 kewaye da duniyar Saturn. Masana suka ce nan da shekaru miliyan 100 zubban Saturn za su fara mutuwa.

Ko Za Ka Karanta?

2. Suna – duniyar Saturn ta samo asalin sunanta ne daga sunayen daya daga cikin allolin Romawa, Saturn. Haka nan tana da sunaye kala-kala daga wurin wasu al’umma ko masana, kamar masana karantar taurarin Hindu suna ƙiranta Shani; haka nan Girka ma suke ƙiranta Phainon.

3. Samuwa – duniyar Saturn ta samu shekaru biliyan 4 da suka shuɗe, shekaru miliyan 500 bayan samuwar Solar System. Duniyar ta ginu ne da tiriri da sinadaran gas da hydrogen da helium

Ko Za Ka Karanta?

4. Ziyara – a tarihi sau huɗu aka taɓa aika jirage duniyar Saturn; na farko a shekarar 1979, na biyu a shekarar 1980, na uku a shekara 1981, na huɗu a shekarar 2004. Jirgin da aka tura a shekarar 2004 ya shafe shekar 13 yana bincike a duniyar Saturn kafin halakarsa a shekarar 2017.

5. Lokaci – lokaci a duniyar Saturn daban yake da na sauran duniyoyi. Duniyar tana shafe sa’o’i 10 kacal domin juyawarta na kwana daya, haka nan tana shafe shekaru 29 kafin ta zagaye rana. Daga duniyar Saturn zuwa tamu ta Earth, sa’a daya da mintuna talatin kawai haske yake yi kafin ya karaso gare mu.

6. Girma – duniyar Saturn ita ce duniya mafi girma ta biyu a Solar System baya duniyar Jupiter. 

Ko Za Ka Karanta?

7. Watanni – duniyar Saturn tana da watanni a ƙalla 82, kuma har yanzu ana ƙoƙarin tabbatar da kasantuwar wasu. Babban watan duniyar shi ne Triton, wata mafi girma na biyu a Solar System bayan na duniyar Jupiter, Ganymede.

Madogara

1. Wikipedia.org

2. NASA

Mohiddeen Ahmad

Mohiddeen Ahmad

I am Muhammad Auwal Ahmad, an inquisitive student, tech aficionado, science enthusiast and a writer. I am the founder and CEO of Flowdiary.

One Comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *