2

Ko Yaya Ake Yi Wa Gawar Mutum Binciken Ƙwaƙwaf?

Shin ka san kuwa a yau maƙurar binciken kimiyya ya kai cewa ana iya gane asalin mutum ko sanadin mutuwarsa ko da ya shafe sama da shekaru dari da mutuwa?

A duniyar kimiyya, kuma a cigaban da aka samu tun a ƙarnukan baya, an iya kai matakin da ake yi wa gawar mutum binciken ƙwaƙwaf, don gano sanadin mutuwarsa ko kuma gano wata cuta da ke jikin mutum don samun wasu ilmuka da sauransu.

A irin wannan binciken ƙwaƙwaf da ake ƙira autopsy ana iya gano wasu sirrika a jikin mutum da shi kanshi bai san da su ba har ya mutu, don ba sanadin mutuwa kawai ake iya ganowa ba, har da:

  • binciken gano lokacin da mutum ya mutu
  • bincike akan ƙwayoyin halittar mutum don gano asalinsa
  • bincike don gano yadda cuta (idan ta kasance ita ce sanadin mutuwar) take shiga jikin mutum da sauransu.

Masana tarihi suka ce irin wannan binciken ƙwaƙwaf akan gawar mutum ya samo asali ne shekaru aru-aru da suka gabata; wasu suka ce tun a 3000 BCE a tsohuwar ƙasar Egypt. Sannan daga baya, bayan dubunnan shekaru Romawa ma suka kwaikwayi wannan fiƙira, a inda Julius Caesar ya zama mutum na farko da aka fara yi wa gawarsu binciken ƙwaƙwaf bayan kashe shi da aka yi.

Amma a ƙarni na 11 zuwa na 12 kuma kimiyyar magani da fiɗa suka fara ƙarfi sosai, a inda masani kan likitanci da fiɗa na tsohuwar ƙasar Andalus, Ibn Zuhr, ya gina fiƙirori da nazariyyoyin kan fiɗa da binciken ƙwaƙwaf. Wani muhimmin abu da masanan duniya suka koya daga wajen wannan masani shi ne, da farko yana fara yin gwajin fiƙirarsa ko bincikensa ne akan dabbobi kafin yayi akan mutane.

Daga nan aka ci gaba da amfani da fiƙirorin masanan baya, da wasu na zamani don gudanar da binciken ƙwaƙwaf akan gawar mutum, don wasu dalilai kamar yadda yake a sama a jere. Misali a shekarar 1775 aka kashe wani likita Dr. Joseph Warren a wani gumurzu, don haka sai abokinshi ya gudanar da binciken ƙwaƙwaf a kanshi don tantance sassan jiki waɗanda suka kasance nashi da wanda ba nashi ba.

Ana yin binciken ƙwaƙwaf a dakin binciken kimiyya

A da masana tarihi sun rubuta cewa Napoleon ya mutu ne ta dalilin gubar da aka ba shi a abinci, amma ba a gano makashin nashi kai tsaye ba. Amma bayan shekaru sama da dari da hamsin, masana ilimi na wannan zamanin suka ce ba kashe shi aka yi ba, guba ya shaƙa a labulen ɗakinsa, kuma ba wanda ya kitsa hakan kawai ya faru ne.  Ya shaƙi gubar sinadarin arsenic ne kwatsam a labulen ɗakinsa. Ita kuma wannan guba tana iya yawo a iska, don haka ta manne a jikin labulen ɗakin don ta dace da shi. Sannan ita wannan gubar tana sa matsanancin ciwon ciki, don haka ne a wancen lokacin aka ce cutar daji ta ciki ce ta kashe Napoleon, ashe ba haka ba ne.

Masana sun yi amfani da gashin Napoleon da ke gidan tarihi, da kuma binciken abubuwan da yake amfani da su a lokacin, da yanayin yadda garin da yake da zama yake, da dai sauran abubuwan da ya danganta da shi domin samun gamsashshiyar amsa da kuma bincike mai fa’ida.

Sannan sai binciken ƙwaƙwaf da Dr. Thomas Harvey ya gudanar a kan gawar babban masanin kimiyya Albert Einstein a shekarar 1955, a inda ya gano fifikon ƙwaƙwalwa da masani Einstein ya ke da ita da sauran mutane.

Ko Za Ka Karanta?

Haka nan a shekarar 1991 aka gano gawar wani mutum daskare cikin ƙanƙara a bodar ƙasar Austria da Italy. Bayan masana kimiyya sun gudanar da bincike akansa sai aka gano cewa ya rayu tun a karni na 34 BCE, wato dai yanzu a kalla ya shafe shekaru 5,300 a mace. Masana sun sawa wannan mamacin suna Otzi.

Wannan ƙanƙarar ita ta daskarar da shi ya sa bai rube ba har da gatarinsa da taguwarsa. Masana suka ce akwai yiwuwar ya je ƙetara wannan tudun ƙanƙarar nan ne don zuwa saran icce, ko kuma kewaya a daji amma sai tsantsin ƙanƙarar ya debe shi ya faɗi ya karya ƙashin wuya.

Wannan nazari da bincike yayi matuƙar taimakawa masana kayan tarihi da masana kimiyya da sauransu. A wannan bincike na ƙwaƙwaf da aka gudanar a kan gawar Otzi an iya gano ƙwayoyin halittarsa, wanda haka ya sa aka gano cewa har yanzu akwai tsatsonsa waɗanda suke raye a duniya a ƙalla mutane 19. Sannan an iya gano tarin abubuwa a jikinsa kama daga ƙwaƙwalwarsa, cikinsa da sauransu.

Ko Za Ka Karanta?

Likitocin da ke yi wa gawa binciken ƙwaƙwaf da ake ƙira pathologists, suka ce matakai uku da ake bi wajen gudanar da wannan aikin sun haɗa da:

1. Purpose of the Autopsy

Abu na farko da likitocin suke farawa shi ne sanin dalilin da ya sa za su gudanar da binciken ƙwaƙwaf a kan gawar mutum. Da yake akwai dalilai da dama, wani lokaci ta kan iya faruwa a ce ana son gano lokacin da mutumin ya mutu ne; to a nan inda za su fi mayar da hankali a kai shi ne tattara bayanai da kuma sakamakon binciken da suka samu domin kai wa ga cin nasarar abunda suka sa a gaba. Sannan suna bukatar sa hannun magajin gawar –wato wani wanda ya kasance jigo ga wannan gawa, kamar uba ko ɗa ko ɗan’uwa ko makamancin haka.

2. External Examination

A wannan matakin da ya kasance na biyu, a shi ne ake binciken gano wasu abubuwa na mutum da suka kasance a bayyane; misali, dole za a fara gano jinsi, shekaru, ƙabila da makamantansu na wannan gawa. Sannan a nemi wasu bayanan da za su iya samuwa kamar lokacin mutuwar, inda ya mutu, kalmominsa na magagin mutuwa da sauransu. Da waɗannan bayanan ne likitocin za su samu damar ɗaura akalar bincikensu akan hanyar da ta dace.

3. Internal Examination

A wannan matakin kuma ana bincike ne kan gano wasu abubuwan da suke na mutum, wanda wataƙila shi kadai ne ke da su a duniya –kamar zanen hannu. Sannan kuma sai a shiga gano ƙwayoyin halittarsa, nau’in jininsa da sauransu. A wannan matakin ne kuma da ya kasance mai sarƙaƙiya ake farɗe mutum kamar cikinsa ko ƙwaƙwalwa don gano ko akwai wata cuta a ciki, ko kuma wani abu da ya kasance baƙo ko wanda zai iya cutar da shi. Sannan a nan ake gano wane irin abinci yake ci, yaushe ne cin abinsa na ƙarshe, mene ne a cikin abincin da makamantansu musamman idan ya kasance ana zargin kashe shi aka yi ta hanyar guba, ko kuma ana so a gano lokacin da ya mutu.

Ko Za Ka Karanta?

Madogara

Wikipedia.org

Britannica.com

PopularMechanics.com

Mohiddeen Ahmad (Facebook posts)

Mohiddeen Ahmad

I am Muhammad Auwal Ahmad, an inquisitive student, tech aficionado, science enthusiast and a writer. I am the founder and CEO of Flowdiary.

2 Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *