5

Yin Tunani Don Warware Matsalolin Rayuwa

Kullum sababbin matsaloli suna tunkaro mu kuma muna ƙoƙarin nemo wasu hanyoyi da za mu samu damar warware matsalolinmu, waɗanda suka kasance masu kyau, ko ma dai saɓanin haka. Kuma muna yin hakan ne ta hanyar yin tunani kuma mu ɗauki shawarar da muke ganin za ta iya fishshe mu.

Amma a wasu lokutan mutane suna yanke shawara ne ba tare da sanin me hakan zai haifar ba, wato yanke shawara kai-tsaye ba tare da duba kamata na abunda za mu yi ba. A irin waɗannan lokutan ana samun matsaloli da dama da za su iya biyo baya; ke nan an faɗa abunda Malam Bahaushe yake ƙira “garin nemo ƙiba an samo rama.”

Ko Za Ka Karanta?

Don kaucewa faɗawa wata matsala, ya danganta ga waɗanne matakai ne muka bi da zai iya kai mu ga yanke sahihiyar shawara da za ta iya kai mu ga ci, ta hanyar yin la’akari da waɗansu abubuwa a ilimance.

Sai dai wasu lokutan ba matsalaoli masu girma muke samu ba, kawai dai rashin tadanar waɗannan abubuwa a rayuwarmu yana janyo mana wata matsalar. A takaicen-takaicewa, waɗannan matakai da ke kasa, da ma wasu, su ya kamata mu rinƙa duba a duk wasu harkoki na rayuwarmu ta yau da kullum.

A nan, zan so mai karatu ya fahimci kalmar matsala da yadda ya kamata ya ɗauke ta a wannan maƙalar –wato kan iya zama duk wani lamari na rayuwar yau da kullum, ba wai sai tarzoma ko wata hatsaniya ko wani mummunan lamari ne matsala ba. Don haka ya na da kyau a fahimci wannan a karon farko.

1. Fahimtar Matsalar

A karon farko dole za a fahimci mece ce matsalar? kuma yaya take? shin ta wace hanya za a fara warware ta?

A kimiyyar na’ura da lissafi, a duk lokacin da wata matsala –wato wani al’amari ya taso ana la’akari da yadda yake da kuma yadda za a fara shawo kansa. Misali, idan ana so a koyi wani abu ana ɗaukar matakai da za su iya fishshe da mutum ne kamar; la’akari da yanayin girman abun, abubuwan da ake buƙata, fa’idar abun da za a koya da sauransu. Don haka a kowane irin lokaci ana so a fara fahimtar mece ce matsalar da ake son warwarewa, kuma ta wace hanya ya kamata a ɓullo mata.

2. Amfani Da Fiƙirar Lissafin ‘Algorithm’ Don Shawo Kan Wani Lamari

Kamar yadda yake a kimiyyar na’ura da lissafi, ana amfani da fiƙirar lissafin Algorithm don shawo kan wani al’amari tun daga tushe. Ana bi daki-daki, mataki-mataki, saƙo-saƙo domin warware wannan al’amari.

Abunda ake so a fara yi shi ne da farko bayan an fahimci mece ce matsalar kuma ana so a tunkare ta, sai a sanya wannan fiƙirar lissafin, misali idan lamarin ya kasance ana son yin karatu ne ko sana’a, sai lissafin ya kasance kamar haka:

Na farko: 	karatu, sana’a 
Na biyu:	a ina zan yi karatun? kwaleji 
Na uku:	        a ina zan fara sana’a? garinmu 
Na hudu:	ina da jarin sana’a? a’a
Na biyar:	ina da kuɗin karatu? a’a
Na shida:	ni zan ɗauki nauyin karatuna? e
Na bakwai:	karatu ko sana’a? ?
Na takwas:	ba ni da jari, ba ni da kuɗin karatu?
Na tara:	ina son karatu, ina son sana’a.
Na goma:	wanne ne zai yiwu daga cikinsu?
Na goma shadaya: karatu ba zai yiwu ba sai da kuɗi.
Na goma shabiyu: sana’a ba za ta yiwu ba sai da kuɗi.
Na goma sha’uku: shin in ciwo bashi?
Na goma shahudu: idan na ciwo bashin wanne zan yi?
Na goma shabiyar: idan na ciwo bashin zan biya a shekara ɗaya.
Na goma shashida: shin in biya kuɗin karatuna da kuɗin bashin?
Na goma shabakwai: ko kuma in yi sana’a?
Na goma shatakwas: idan na biya kuɗin karatu ai babu kuɗin da zan biya bashin.
Na goma shatara: idan na yi sana’a da kuɗin zan iya samun riba, kuɗin karatuna, kuma in biya kuɗin bashin.
Na ashirin:	zan yi sana’a da kuɗin.

Duk da abun ya ɗauki lokaci, amma haƙiƙa yanke shawarar ba ta zo a gurɓace ba. Haka nan an yi amfani da lissafi wajen warware wannan matsalar, kuma babu wani hangen nesa cewa za a iya samun matsala nan gaba. Idan kuma aka ci gaba da yin wannan lissafin a kowane lamari na rayuwar yau da kullum, to haƙiƙa za a dace.

3. Tsarin Rayuwa, da Lokaci, da Ƙididdiga, da Bincike

Rayuwa ba za ta yiwu babu tsare-tsare ba. Dole duk wanda ya fahimci duniyar yau zai san cewa tsarin rayuwa abu ne wanda zai yi matuƙar taimaka masa. Ya kamata duk wani lamari da za a yi a rinƙa duba yiwuwarsa, da sakamakon da zai haifar, da sanadinsa, da kuma hangen nesa a kanshi da dai makamantansu.

Har ila yau, babu yadda za a yi mutum ya iya tsara lamuran rayuwarsa yadda suka dace ba tare da tsara lokacin yin komai nasa ba; kamar lokacin karatu, ibada, mu’amala, kasuwanci da sauran al’amuran rayuwa na yau da kullum. Ke nan, mutum zai rinƙa tsara mene ne ya kamata yayi a wannan makon, ko watan ko shekara, wato ya rubuta ƙudirinsa da yake son cim ma wa.

Ko Za Ka Karanta?

Sannan sai ƙididdiga. Ana so duk wani lamari na rayuwar yau da kullum da mutum yake yi, ya kasance yana ƙididdigar abubuwan da suke faruwa da shi. Misali, ya kasance duk mako, a wata, ko shekara ana ƙididdigar abunda za a yi. Wato bayan an tsara ƙudirin da ake son cim ma wa, sai bayan wannan lokaci kuma a duba nasara ko faɗuwa da aka samu da kuma dalilan haka, sannan da darussa da aka ɗauka don nan gaba a kiyaye.

Misali, idan na rubuta wato na tsara cewa a wannan makon zan karanta littatafai guda uku (sannan na rubuta sunayensu), zan ziyarci abokaina biyu, sannan zan yi bincike kan wani kundi. To amma sai aka samu matsala ban karanta waɗannan littatafai duka ba, sai na samu damar karanta ɗaya, kuma ban yi bincike kan wannan kundi ba, haka nan abokaina uku da na ce zan ziyarta ban ziyarcesu duka ba. Yanzu abunda nake buƙata shi ne ƙididdiga da binciken gano mene ne yayi sanadin faruwar haka, sannan sai na gano ai rashin tsara lokutan waɗannan abubuwan da nace zan yi ne, kawai na shagalu da cewa zan yi amma ban tsara lokutan yinsu ba. To don haka yanzu na gano sanadin, kuma abunda zan yi nan gaba shi ne tsara lokaci saboda shi ne matsalar da na samu. Ke nan na ɗauki darasi, kuma zan kiyaye hakan na gaba.

Mohiddeen Ahmad

Mohiddeen Ahmad

I am Muhammad Auwal Ahmad, an inquisitive student, tech aficionado, science enthusiast and a writer. I am the founder and CEO of Flowdiary.

5 Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *