5

Muhimman Hanyoyi 5 Don Kare Wayar ‘Android’ Daga Annobar Na’ura Da Kutse

wayar android
Wayar Android

A duniyar zamani kuma a duniyar na’ura, babu wata na’ura mai ƙwaƙwalwa da za ta tsira daga kutse matuƙar tana kunne. Duk wani rukuni na na’ura mai ƙwaƙwalwa kama daga na’urorin tafi-da-gidanka, ko na’urorin kasuwanci, ko na aikin ofishi, ko na sadarwa, ko wayoyin hannu, da dai sauransu ba za su tsira daga tarkon madatsa ba, domin idan mai kariya ya na da hanyoyi goma na kare kanshi, madatsi ya na da hanyoyi dari da zai iya yin kutse.

Sai dai duk da haka masana suka ce yawancin waɗanda ake yi wa datsa suna ba da ƙofa ne ko ƙarama ce. Wasu lokutan kuma rashin ɗaukar matakan kariya, ko bayyana wasu sirruka na na’ura kan iya sa a musu datsa ba tare da saninsu ba, ya dai danganta ga wane irin datsa aka shirya musu da yadda za a samu nasara a kansu.

Ko Za Karanta?

Amma a lamarin manyan wayoyin zamani irinsu Android, mafi yawan hanyoyin da za a samu nasara a kan masu su shi ne ta hanyar ba su ƙofa, don a wannan zamanin an gano mafi yawan masu riƙe wayoyin ba su san abunda zai cutar da wayoyinsu da wanda ba zai cutar ba. A wannan rubutun za mu ga waɗanne hanyoyi ne ya kamata a bi don kare kai daga madatsa.

Yin kutse wa wayar Android kan iya zama da manufofi da dama, kamar yi don:

  • ƙeta
  • tallace-tallace
  • neman kuɗin fansa
  • leƙen asiri
  • rusa wani lamari ko kuma wayar gaba ɗaya

Da sauransu, ya dai danganta ga don wace manufa ne aka yi kutsen. Sannan wasu lokutan su kan iya yin kutsen cikin na’urar mutum kuma su gama abunda za su yi ba tare da saninshi ba. Amma kowanne daga cikin jerin nan ya kasance mai matuƙar hatsari ne, don haka ya kamata a ɗauki wasu matakai da zai hana yin kutse cikin wayoyi.

Ko Za Ka Karanta?

Hanyoyin Da Za A Kare Waya Daga Madatsa

1. A Rinƙa Kulle Waya

Abu na farko da za a yi kuma a rinƙa yi shi ne kulle waya ta hanyar sanya mata tsaro. Duk da sanya wa waya tsaro ya zama ruwan dare, amma game da kariyar waya ba wai sanya wa waya tsaro kamar yadda kowa yake yi shi ne abun nufi a nan ba. Sanya wa waya tsaro da kulle ta na nufin kulle duk wata manhaja da ke cikinta waɗanda ke da mu’amala da hanyar sadarwa, sirrikan waya da makamantansu. Don haka ya na da kyau a rinƙa kulle waya da sanya mata tsaro ta hanyoyin da suka dace.

2. A Yi Hankali Da Sanin Me Ake Sanyawa A Cikin Waya

Lokuta da dama mutane suna amfani da manhajoji da kala-kalan abubuwa ba tare da duba sahihanci da ingancinsu a cikin wayoyinsu ba. Wannan kuma ya kasance sakaci ne mai hatsari. Don haka ya na da kyau a rinƙa kula da duk wani abu da ke cikin waya; a kula da saƙonni, hotuna, bidiyoyi, fayil da makamantansu. A rinka sanin waɗanne abubuwa ne aka sanya a cikin waya kuma waye ya sanya su, sannan mene ne tabbacin wannan abun kasancewarsa sahihi. Misali a irin wayoyin Android da suke ɗauke da fayil da dama, kuma yawancin mutane ba su san amfaninsu ba saboda kasacewar sun danganta ne ga wata manhaja da aka sanya ko gundarin-tsarin-gudanarwa, ya sa wasu ba sa kulawa da duba waɗanne irin fayil ne a cikin wayoyin nasu. Amma duk da haka, akwai wasu fayil da suke kasantuwa a cikin wayoyi da suke saɓa layi; wato daga gani bai dace su kasance a inda suke ba. Don haka duk wani fayil da aka gani a cikin waya ya kamata a duba sahihancinsa da tabbacin kasantuwarsa a matsayinsa na fayil ɗin nan da kuma nau’insa.

Ko Za Ka Karanta?

3. A San Da Wa Ake Mu’amala

A wannan zamanin waɗanda suke kusa da mutum ma su kan iya cutar da shi  ballantana waɗanda bai sani ba. Don haka ya na da kyau a san da waye ake mu’amala a zahiri da kuma duniyar sadarwa ta yanar gizo. Wasu lokutan abokan mutum za su iya tura masa wasu fayil masu cutarwa ba tare da saninshi ba, kuma an fiye yawan yin hakan ne a dandulan sada zumunta kamar WhatsApp ko Telegram. Ko kuma a tura wa mutum a zahiri ta hanyoyin sadarwarshi. Haka nan a kan tura wa mutum likau ta waɗannan hanyoyin ana cewa ya bi don ya samu wani abu. Amma a zahiri, ko da an san mutumin da ke turo irin waɗannan likau ɗin ko manhajoji, bai kamata a kula da su ba domin yanzu madatsa suna yin kutse cikin asusan mutane su tura wa abokansu irin waɗannan saƙonnin na likau ko manhaja domin a ja ra’ayinsu kan wannan abu, don za su fi yarda idan suka ga abokinsu ne ya tura musu.

Ko Za Ka Karanta?

4. A Kula Da Manhajojin Da Ake Sanyawa A Cikin Waya

Mafi yawan waɗanda ake yi musu kutse a waya ta hanyar manhajoji ne saboda yawancin mutane ba sa duba sahihancin manhaja kafin sauƙe ta ko sanya ta a cikin wayoyinsu. Akwai manhajojin da ke ɗauke da annobar na’ura wacce da zaran manhaja ta fara aiki a cikin waya za ta nemi hanyar da za ta cutar da wannan wayar. Misali idan manhajar leƙen asiri ce, wataƙila daga sanya ta a cikin wayar ba za a ganta ba ballantana a cire ta, don haka sai ta yi ta neman bayanan sirrikan mutum tana tura wa masu ita. Sannan ana amfani da wannan dama a ƙirƙiri manhaja, wacce ko da ba ta kasance ta cutarwa ba tana ɗauke da likau na tallace-tallace wanda zai iya kai mutum faɗawa cikin hatsari. Yawancin irin waɗannan manhajojin kuma ana tallata su ga mutane ne kan cewa idan aka sanya su a cikin waya za a samu kudi, ko wata garabasa da sauransu. 

5. A Kula Da Sashin Sadarwa

Duk wani abu da zai shigo cikin waya sai ya kasance ta sashin sadarwa ne. Sashinan sadarwan suna da dama, misali sashin sadarwa na yanar gizo, na Wi-Fi ko Bluetooth, na tura fayil daga wata na’ura zuwa wata ta hanyar sanya igiyar caji da sauransu, amma duk waɗannan hanyoyi ba su kasance masu tsaro ba. Abunda ya kamata a yi shi ne a rinƙa kulle Wi-Fi, ko Bluetooth ko Hotspot a duk lokacin da ba a amfani da su, sannan a kula da sashin sadarwan yanar gizo a san ina aka shiga kuma ina ne bai kamata  shiga ba. Har ila yau a rinƙa kula da sashin sadarwan jona igiyar caji don sanya fayil a cikin waya ko wata na’ura –domin a irin wannan yanayin ana samun gurɓacewar annobar na’ura da za ta iya shiga wayar mutum ko na’ura ba tare da saninshi ba.

Ko Za Ka Karanta?

Don haka ya kamata a kula da duk waɗannan hanyoyin da madatsa kan bi don su samu nasarar yin kutsen asusan mutane. Ya na da kyau a san muhimmancin tsaro da boye bayanan sirri, domin idan lamarin kutse ya faru yana shafar mutane da dama.

Mohiddeen Ahmad

Mohiddeen Ahmad

I am Muhammad Auwal Ahmad, an inquisitive student, tech aficionado, science enthusiast and a writer. I am the founder and CEO of Flowdiary.

5 Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *