5

Datsa da Annobar Na’ura: Mene ne Virus, Malware, Spyware, Adware, da Ransomware?

virus

Duk wata daƙiƙa guda a yanar gizo ko a na’ura tana kasancewa mai hatsari, saboda yawaitar datsa da annobar na’ura da aka fi sani da virus. Sai dai duk da haka shi ma virus ɗin ya kasance kashi-kashi ne, kuma kowanne da aikinsa. Sau tari mu kan ci karo da waɗannan abubuwan wato ire-iren virus amma ba lallai ba ne in mun san ma’anoninsu. Sai dai sun kasance masu matuƙar cutarwa a cikin na’urorinmu da kuma yanar gizo. Sannan ana amfani da su wajen datsar na’ura da yanar gizo da leƙen asiri da sauransu.

Ko Za Ka Karanta?

Shin mene Virus, da Malware, da Spyware, da Adware, da Ransomware a duniyar datsa da na’ura?

1. Virus

annobar naura virus

Virus kan iya zama duk wani abu mai cutarwa da ke yawo a yanar gizo ko cikin na’urori. A kan yi amfani da shi wajen yin datsa domin cim ma wani buri na musamman, ta hanyar tura shi zuwa na’urar mutum ko sashin sadarwarsa. Madatsa da suka ƙware a kan tsare-tsaren na’ura su kan ƙirƙiri waɗansu irin tsare-tsare haɗe da haruffa da zai iya kasancewa wata manhaja ko wani salon cutar da na’ura. Na’urori da dama suna faɗawa wannan tarkon. Ya kan iya zuwa musu a matsayin wata manhaja ko wani abu, kuma yawanci suna gamuwa da shi ne a yanar gizo ko kuma ta hanyar sadarwa tsakaninsu da wata na’ura.

2. Malware

Kamar dai virus, shi ma malware dangin virus ne mai cutarwa, wanda ake ƙirƙira musamman don cutar da na’ura. Zai iya zama sanadin rushewar na’ura, hanyar sadarwa, ko kuma kawo dameji ga wani lamari da ake gudanarwa a yanar gizo ko a na’ura. Har wayoyin zamani da duk wata kalar na’ura mai ƙwaƙwalwa ba sa tsira daga sharrin malware. Sau tari mutane suna sauƙar da shi ne a cikin na’urarsu ba tare da sanin shi ɗin ne ba, saboda yana zuwa a salo kala-kala. Misali, mutum ya kan iya zuwa wani shafi don sauƙe wata manhaja, amma idan aka yi rashin sa’a sai ya sauƙe malware kuma ya saka shi a cikin na’urarsa ba tare da sanin shi manhaja ne mai cutarwa ba. Hanya mafi sauƙi da mutum zai iya kauce faɗawa tarkon malware ta hanyar sauƙe manhaja shi ne daina sauƙe manhajoji a shafukan da ba su kasance ingantattu kuma sahihai ba.   

3. Spyware

Haka nan kamar yadda sunan ya nuna, spyware dangin annobar na’ura ce da ke leƙen asiri a cikin na’urar mutum. Irin wannan manhajar madatsa da masu leƙen asiri ne suke ƙirƙirarta saboda ta yi musu leƙen asiri a cikin na’urar mutum. Suna tura wa mutane irin wannan manhajar ta hanyar sadarwa kamar ta imel, dandulan sada zumunta, shafukan yanar gizo da makamantansu. Ana tura wa mutum ne zuwa na’urarsa saboda akan shi aka yi shirin yin leƙen asiri, ita kuma manhajar za ta kutsa cikin na’urar mutum ne ta nemo duk wani abunda ya ajiye mai muhimmanci sa’annan ta tura wa waɗanda suka aiko ta.

Ko Za Ka Karanta?

4. Adware

Shi kuma wannan ba zai kasance mai cutarwa ba, kawai manhaja ne da ke zama a na’urar mutum ko shafin yanar gizo wanda ke nuna tallace-tallace ba tare da izinin mutum ba. Wannan manhajar aikinta kawai shi ne fito da tallace-tallace musamman a shafin yanar gizon mutum don cim ma ƙudirin samun maziyarta ko kwastomomi ga waɗanda suka ƙirƙire ta. Ana samun irin waɗannan manhajojin ne ta hanayr sauƙe wasu manhajoji na kayatar da shafi da makamantasu.

5. Ransomware  

Kamar yadda sunan ya nuna, irin wannan manhaja ta dangin virus ana ƙirƙirar ta ne don tura wa na’urorin da ke aiki a kamfani ko kuma mutum a karan-kansa, da za ta iya dakatar da wani sha’ani da ake gudanarwa ta hanyar yin yunƙurin kawo illa ga na’urorin ko hanyar sadarwa, wanda ƙudirin yin hakan ga maƙirƙiranta shi ne don biyan kuɗin fansa. Irin wannan manhaja za ta tsayar da wani lamari da ke gudana a cikin na’ura ko ƙoƙarin rusa wani abu ko gurbata bayanai a rumbunsu, har sai wannan kamfanin ko mai na’urar ya biya wasu kuɗaɗe don fanshe kansa.

Duk waɗannan manhajoji an yi su ne don cim ma buƙatun maƙirƙiransu. Suna amfani da su don ƙeta wajen rusa na’urar mutum, ko leƙen asiri, ko dakatar da na’urarsa daga aiki har sai ya biya kuɗin fansa da dai sauransu kamar yadda mu ka gani a sama.

Ko Za Ka Karanta?

Mohiddeen Ahmad

Mohiddeen Ahmad

I am Muhammad Auwal Ahmad, an inquisitive student, tech aficionado, science enthusiast and a writer. I am the founder and CEO of Flowdiary.