1

Bayani a kan Gundarin-Tsarin-Gudanarwar ‘Android’

Gundari-Tsarin-Gudanarwar Android

Android gundarin-tsarin-gudanarwa ne da aka samar don wayoyin tafi-da-gidanka na zamani. Duk da an samar da shi a shekarar 2005 ƙarƙashin jagorancin Andi Rubin tare da Chris White, da Rich Miner da Nick Sears, amma bai fara aiki da bunƙasuwa a duniya ba sai a shekarar 2008 lokacin da aka fara gabatar wa duniya farkon waya da aka ƙirƙira kan wannan gundari-tsarin-gudanarwar.

Andy Rubin, maƙirƙirin Android

Kamfanin Google ne ya ɗauki ragamar shigar da gundarin-tsarin-gudanarwar Android kasuwa, inda a yau ya zama shi ne na farko da mutane suke amfani da shi a duniya. Daga baya kuma kamfanin Google ya saye shi gaba ɗaya akan kuɗaɗe $50,000,000 kamfanin ya ce a yau sama da biliyan 2 na wayoyin tafi-da-gidanka na zamani ne ke amfani da wannan gundarin-tsarin-gudanarwar.  

Asalin tsarin Android an yi ta ne a matsayin saƙaguwar manhaja, wato wata na’ura da za ta iya yin wasu abubuwa da mutum zai yi, a matsayin ta zamani kuma tafi-da-gidanka. Don haka sai ta kasance wacce za ta iya taimakawa mutum wajen gudanar da wasu lamuransa, wacce kuma ta zo da sababbin tsaruka na zamani.

A kullum ma’aikata suna kan sabunta gundarin-tsarin-gudanarwar Android, don mafi sabon da aka fitar shine Android 11, wanda aka fitar a watan September na shekarar 2020. Don tabbatar da tafiya da zamani da daidaita amfani da manhajoji masu fasahohin zamani kamar su Artificial Intelligence, Machine Learning, Internet of Things da sauransu ya sa ake sabunta Android. Sai dai ba kowa ba ne yake amfani da sababbin tsare-tsare da salon, mafi yawan mutane a yanzu tsarin da suke amfani da shi a wayoyinsu ba ya wuce daga na 6 zuwa na 7.

Android na da tsare-tsare da dama kamar tsaro; an yi amfani da fasahohin zamani wajen tabbatar da tsaro, ba wa masana tsare-tsaren na’ura dama wajen kirkiro manyan manhajoji da taimaka musu don tafiyar da su, kyawun kyamara, tana da manyan ma’ajiyar bayanai, da sauri wajen gudanarwa da sauransu.

Masana tsare-tsaren na’ura a yau suna amfani da yaren na’ura kamar su Java, Kotlin ko C# wajen kirkirar manhajojin Android.

Mohiddeen Ahmad

Mohiddeen Ahmad

I am Muhammad Auwal Ahmad, an inquisitive student, tech aficionado, science enthusiast and a writer. I am the founder and CEO of Flowdiary.

One Comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *