0

A ina Ɓataccen Birnin Atlantis Yake?

Ɗaya daga cikin manyan masana falsafar Girka, Plato, wanda ya kasance ɗalibi ga shahararren masanin falsafar Girka, wato Socrates, ya ruwaito labarin birnin Atlantis da ya nutse a teku, a cikin wasu maƙalolinsa Timaeus da Critias.

Plato ya ce ya ji wannan labarin ne a wurin kakansa, wanda shi ma ya ji ne daga wurin ɗaya daga cikin masu-fada-a-ji na birnin Athens kuma babban masani wanda ya laƙanci sanin sha’anonin duniya; Salon, wanda shi ma ya ji ne daga wurin wani babban malami a Egypt, cewa wannan lamari ya faru ne shekaru 9,500 kafin zamanin Plato.

Ko Za Ka Karanta?

To ko ma dai mene ne, walau lamarin ya faru a zahiri ko kuma dai almara ne, masana da dama a duniya sun ɗauki wannan labarin a matsayin zarar-bunu ko labarun hikima da Plato ya saba bayarwa a rayuwarsa, ciki har da labarin kogo.

Sai dai duk da haka Plato ya nuna lallai labarin gaskiya ne, inda yake nuna cewa birnin Atlantis wata babbar daula ce. Imani da wannan ya sa masana bincike kan ababen tarihi kutsawa don nemo wata shaida da za ta tabbatar da kasantuwar wannan lamari.

Wasu masana suka ce lallai birnin Santorini ne Atlantis, wani tsibir da bala’in aman wutan dutse ya afka masa a ƙarni na 16 B.C, wato yau shekaru 3,500 da suka shuɗe.

Ko Za Ka Karanta?

Wasu kuwa suka nuna cewa ai tekun Atlantika ne Atlantis, saboda kasantuwar sunayensu na kamanceceniya, a inda suka ce wataƙila a tekun Allantikan ne birnin Atlantis ya nutse. Sai dai har yanzu babu wata shaida ƙwaƙƙwara da za ta tabbatar da hakan a zahiri kuma a bayyane.

Idan har lamarin ɓacewar birnin Atlantis ya faru da gaske, a yau lamarin zai iya kai wa shekaru 11,500 da suka gabata ke nan.

Ko Za Ka Karanta?

Madogara:

History.com

Wikipedia.org

AlienNationCorporation.com

Mohiddeen Ahmad

Mohiddeen Ahmad

I am Muhammad Auwal Ahmad, an inquisitive student, tech aficionado, science enthusiast and a writer. I am the founder and CEO of Flowdiary.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *