4

Kwatancen Girman ƙwaƙwalwa da ƙaunu

Mutane da dama, musamman masana suna yawan tunanin yanayin girman ƙwaƙwalwa, da kuma yanayin girman ƙaunu. Duk waɗannan abubuwa masanansu sun ce ba su da iyaka, duk da sun sha bamban ta fuskar halitta da yanayi da kuma nau’i.

Masana asalin ƙaunu da tarihinta da wanzuwarta, suka ce ƙaunu ba ta da iyaka; don ganin bangonta abu ne wanda tunanin mai tunani ba zai iya zuwa wurin ba. Suka ce a kowace daƙiƙa guda ƙaunu tana ƙara faɗaɗa, don haka la’akari da duba girmanta abu ne wanda ba zai yiwu ba.

Ko Za ka Karanta?

A ɗaya ɓangaren kuma, masana da masu karantar ƙwaƙwalwa da abunda ta ƙunsa suka ce girman bincikensu bai iya kai wa inda za su gane waɗanne irin bayanai ƙwaƙwalwa ta ƙunsa ba, ko kuma gane yanayin girmanta da abubuwan da za ta iya ƙunsa. Wato dai su ma suna ƙara jaddada cewa ƙwaƙwalwa ba ta da iyaka.

Abu na farko da ke ƙara faɗaɗa girman ƙwaƙwalwar ɗan Adam shi ne tadawwuri; wato yanayin canjin halittu na ci gaba, wanda ya ɗauko asali tun daga samuwar rayuwa. Misali daga nau’in mutanen Homo Habilis zuwa Homo Sapiens an samu canji na tazarar kusan 850 a yanayin girman ƙwaƙwalensu, inda Homo Habilis suke da 550cm^3 zuwa 687cm^3, su kuwa Homo Sapiens ke da 1400cm^3. Wannan ya nuna yanayin yadda girman ƙwaƙwalwa yake ƙoƙarin daidaita don dacewa da zama ƙwaƙwalwar mutum.

Har ila yau, bincike ya ƙara nuna wani banbancin da ke tsakanin girman ƙwaƙwalwar mace da namiji; inda namiji ke da 1370g mace kuma 1200g, amma sai dai wannan yanayin girman duk ba ya nuna kaifin basira ko fiƙira. Haka nan yanayin girman ƙwaƙwalwar mutum ya sha bamban da na sauran halittu kamar dabbobi, tsuntsaye, da sauransu.

Ko Za Ka Karanta?

To amma ba yanayin girman ƙwaƙwalwa a zahiri shi ne girman da za a iya kwantancen shi da girman ƙaunu, girman da za a iya kwatancen shi da girman ƙaunu shi ne wanda  ido ba ya iya gani; wato girman ma’ajiyar bayanai. Misali, ma’ajiyar bayanai na kati ko wayoyin zamani ko na’ura ba su kasance masu girma ba a wannan zamanin, amma suna ɗaukar bayanai masu yawan gaske. Sannan suna bambanta ne kawai a yanayin girman ma’ajiyar bayanai, ba a yanayin girmansu na zahiri ba.

Ko Za Karanta?

Wannan na nuna cewa yanayin girman ƙwaƙwalwar da ake magana a nan shi ne na ma’ajiyar bayanai. Masana a wannan fage suka ce duk abunda mutum zai haddace a ma’ajiyar bayanansa, a duk iya tsawon rayuwarsa bai wuce yayi amfani da kaso 10% cikin 100% na girman ma’ajiyar bayanansa ba. Ke nan duk iya tsawon rayuwar mutum ba zai iya mamaye ko da rabin-rabin ma’ajiyar bayanansa ba. Wannan hasashe kaɗai na nuna yanayin girman kwakwalwar mutum ya wuce inda mutum ɗin yake tunaninsa.

Haka nan su kuma masana ƙaunu suka ce girman ƙaunu ya wuce duk inda mutum zai yi tunani, domin ko da amfani da ma’aunin haske bai iya kai wa rabin-rabin inda ake tunaninsa ba. Iyakar nisan ma’aunin haske a yau shi ne gudun haske na shekaru biliyan 13.39, inda wani gungun taurari mai suna GN-z11 yake, wanda shi ne abu mafi nisa a ƙaunu (a binciken 2016 – zuwa yau).

Ko Za Ka Karanta?

Abunda za a yi la’akari da shi a nan shi ne; shekaru biliyan 13.39 na gudun haske ba daidai suke da shekaru biliyan 13.8 na shekarun kasantuwar ƙaunu ba, duk da shekarun ƙaunu ba daidai suke da yanayin tafiyar lokaci a duniyar earth ba, sai ma dai yin ƙasa da haka. Cikin sauki, da jirgin sama zai shafe shekaru tiriliyon 100 yana tafiya ba zai iya zuwa gungun taurari GN-z11 ba.

Ko Za Ka Karanta?

Madogara:

  • Wikipedia.org
  • ScientificAmerican.com

Mohiddeen Ahmad

Mohiddeen Ahmad

I am Muhammad Auwal Ahmad, an inquisitive student, tech aficionado, science enthusiast and a writer. I am the founder and CEO of Flowdiary.

4 Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *