4

Shawarwari 11 Ga Ma’abota ‘Programming’– Tsare-tsaren Na’ura

maabota programming language yaren naura HTML javascript PHP sql

Masana tsare-tsaren na’ura da ake ƙira programmers suna shirya wasu haruffa ne da ke zama a matsayin tsarukan da ke ba wa na’ura damar gudanar da lamuranta. Waɗannan tsaruka na haruffa da ake kira programming da suka haɗa da lambobin, haruffa, alamu da sauransu, ana shigar da su ne cikin na’ura don biyan buƙatar matsaransu a gudanar da ayyuka da dama.

Mutane da dama suna son koyon wannan harkar ta tsare-tsraren na’ura, amma wasu suna sarewa don wahalarsa, wasu kuwa su ja da baya saboda rashin samun madafun aiki. Haƙiƙa rashin sanin madafun aiki yana kar mutane, kuma ya kasance abu na farko da yake sa su yi ƙasa a gwiwa.

Ga wasu shawarwari da duk wani ma’abocin wannan harkar yake buƙatar sani:

1. Zaɓin Ɓangare

Duk wani ma’abocin wannan harkar ya kamata ya zaɓi ɓangaren da zai riƙe domin akwai bangarori da dama. Rashin sanin wannan kuma yana shigar da mutum daji, domin ba zai san wane ɓangare ne ya dace da shi ba. Ɓangarorin da ya kamata duk wanda ke son wannan harkar ya mayar da hankali a kansu sune kamar web development; ƙirƙirar shafukan yanar gizo, software development; ƙirƙirar manhajoji, system development; ƙirƙirar na’urori. Waɗannan su ne jiga-jigan tsare-tsaren na’ura da muhimmiyar rawar da suke takawa a duniyarta.

Ko za ka karanta?

2. Tsara Lokacin Koyo

Masana wannan harkar suna tsara lokacin koyonsu, wato lokutan da ya kamata  su rinƙa yin bita da kuma gwaje-gwajensu. Zai fi kyau mutum ya tsara yadda zai rinƙa koyo, da yarukan da ya kamata ya fara da su kafin ya wuce gaba. Babbar matsalar da sababbi a wannan harkar suke fuskanta ita ce rashin sanin matakan da ya kamata su bi daki-daki don ginuwa a kan harkar tsare-tsaren na’ura. Don haka yanada kyau a tsara yadda duk za a fara koyo, da lokutan da ya kamata a bata a kan kowanne yare da sauransu.

3. Tadanar Kayan Aiki

Abu na gaba da ake buƙata a harkar tsare-tsaren na’ura shi ne kayan aiki. Dole za a tanadi kayan aikin da suka dace da kowanne yaren na’ura, don kowanne yaren na’ura yanada nashi tsarukan da kayan aikin da ake buƙata wajen gudanar da shi.

4. Tambayar Ƙwararru da Ma’abota Sani

Tambayar ƙwararru da ma’abota sani yana taka muhimmiyar rawa wajen ba wa wani damar sanin hanyoyin da ya kamata ya bi wajen warware wata matsala, ko sanin wasu abubuwa da za su iya wahalar da shi. Amma idan aka tambayi masana harkar sai su ƙara wa mutum haske don sanin yadda zai warware matsalarsa da kuma sanin yadda zai tunkari ta gaba.

5. Juriya da Naci

Daga cikin ɗabi’un masana tsare-tsaren na’ura akwai juriya, haƙuri da naci. Wasu lokutan a kan shafe kwanaki ko makonni aka ƙoƙarin warware wata matsala ko ƙirƙirar waani abu amma bai yiwu ba. Don haka dole ne ma’aboci wannan harkar ya kasance mai haƙuri da juriya, ba wai mai saurin sarewa ba.

Ko za ka karanta?

6. Faɗaɗa Bincike

Dole ne ma’abocin harkar tsare-tsaren na’ura ya faɗaɗa bincikensa a karance-karance littatafai da bibiyar shafukan masana don sanin halin da ake ciki a wannan harkar.

7. Fara Aiki

Da zaran an koyi wasu yaruka kamar biyu, misali HTML da CSS da sai a fara ƙoƙarin gina wani shafi da su. Fara yin aiki yana sa mutum ya san wasu naƙasunsa da yadda zai warware wata matsala, sannan zai zo matakin da zai buƙaci wani abu ko ƙarin haske a wajen masana ne.  

8. Laƙantar Yadda Lamarin Yake

Dole mutum zai laƙanci yadda wannan harkar take tun daga tushe. A nan, ana buƙatar sanin yadda manhaja take gudanar da ayyukanta, da na’ura, da yanar gizo da sauransu. Wasu ba wai a iya rubuta tsare-tsaren na’ura suka tsaya ba, sun ƙware ne a sanin yadda wannan lamarin yake. Don haka akwai buƙatar mutum ya san yadda abubuwa suke wakana a cikin na’ura da haɗakayyarta.

9. Koyon Warware Wata Matsala

Dalili na farko da ya sa ake koya wa mutane lissafi shi ne don laƙantar warware wata matsala da kan iya tasowa. A ilimin lissafi ana ba wa mutum sarƙaƙiya lissafi, shi kuma sai ya nemo wata hikima da zai yi amfani da ita wajen warware wannan sarƙaƙiya. Don haka a nan ana buƙatar sanin yadda mutum zai warware matsala da wannan harkar. Warware matsala ba wai sai sanin yadda ake kula da harkokin na’ura ba, yana nufin fito da wata hanya don ƙirkƙrar wasu abubuwa da zai taimakawa al’umma.

Ko za ka karanta?

10. Aiki da Lisafin Algorithm

Algorithm na nufin bin hanyoyi daki-daki don warware wata matsala, ko kuwa ƙirƙirar wata fiƙira ko wani lamari daban. Dole mutum zai koyi sauƙaƙa wani lamari ta hanyar zana shi a gundarin tsarin algorithm.

Ko za ka karanta?

11. Bibiyar Ayyukan Wasu

Sababbi a wannan harkar, har ma da masananta suna bibiyar ayyukan wasu don sanin yadda suka gudanar da nasu lamarin don su ma su koya. Idan wani masani ya warware wata matsala ko ya ƙirƙiri wani abu to yana bayyanar da hanyoyin da ya bi, har ma da ayyukan da yayi don ba wa wasu su ma su koya. A nan, ma’abota wannan harkar suna buƙatar bibiyar ayyukan wasu masana don fa’idantuwa.

Mohiddeen Ahmad

Mohiddeen Ahmad

I am Muhammad Auwal Ahmad, an inquisitive student, tech aficionado, science enthusiast and a writer. I am the founder and CEO of Flowdiary.

4 Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *