4

Ko Kasan Yadda Za Ka Laƙanci Zama Masanin Na’ura?

Mutane da dama a duniya, musamman matasa suna son koyon harkar na’ura ko zama shahararren masaninta, don dalilai da dama. Cikin dalilan akwai burgewa; wasu kawai sha’anin na’urar ne yake matuƙar burge su, son abun; wasu kuwa ba wani muhimmin dalili face son na’urar da kuma son amfani da ita, don zamanantar da duniya; a haƙiƙanin gaskiya ko da ni marubucin wannan maƙala a wannan matakin nake – wato mun shigo harkar na’ura ne saboda yadda duniya ta koma ta zamani, domin mu koyi harkar don bayar da tamu gudummawar musamman don cigaban al’ummarmu.

To amma duk da haka, koyon na’ura bai kasance kamar sauran kwasa-kwasai ba, wato shi lamari ne da yake buƙatar nazarinka, lokacinka, juriyarka da kuma ƙwazonka. Lamarin na’ura abu ne wanda ya shafi warware duk wata matsala da kan iya tasowa, ko tunanin sabunta wani lamari, ko ƙirƙiro wata fiƙira ko fasaha don cigaba da sauransu. Don haka, lamari ne da ke buƙatar lokaci da kuma ƙwazo, da sauransu abubuwan da na lissafo a sama, saboda wasu lokutan kai da kanka ake son kayi tunanin ƙirƙiro wata fasaha da ba a taɓa ganinta a duniya ba.

Fannonin na’ura sunada matuƙar yawa, don haka ba kowanne ba ne mutum zai iya ƙwarancewa a kai sai dai ya ɗauki wani ɓangare guda musamman wanda ya fi amanna da shi. Misali, akwai ɓangaren:

 1. tsare-tsaren na’ura wanda ake ce masa “programming”, wato fanni ne da ya shafi laƙantar yaren na’ura, koyonsu da kuma sanin yadda ake amfani da su kafin kai wa matakin sanya su a cikin na’ura don wani keɓaɓɓen aiki da ake so ta yi.
 2. zane da ƙayata wato “graphics design”, shi ma fanni ne wanda masanansa suka ƙware a haɗa hotuna ko gyara su, ko kuma wasu da suka shafi na barkwanci da makamantansu.

Da sauransu. Akwai ɗaruruwan fannonin na’ura da mutum zai iya laƙanta a yau don biyan buƙatunsa na dalilin shigowarsa harkar na’ura ko makamancin haka.

Ko za ka karanta?

Amma me kake bukata wajen laƙantar na’ura?

 1. Ka Fahimci Sashinan Na’ura Da Amfaninsu
  Dole za ka fahimci waɗanne sashinan na’ura ne masu amfani da kuma laƙantar sirrinsu. Waɗannan sashinan na’ura sun haɗa da Mouse, Keyboard, CPU, RAM, ROM da sauransu. Waɗannan su ake ƙira hardware components.
 2. Ka Fahimci Manhajar Na’ura Da Yadda Take Aiki
  Duk wani lamari da ke gudana a cikin na’ura to babu shakka manhaja ce take gudanar da shi. Dole za ka fahimci wane mataki ko wace irin rawa manhaja take takawa a cikin na’ura. Misali, Operating System a matsayin zuciyar na’ura wacce ake ƙira gundarin-tsarin-na’ura; Software a matsayin manhaja da take taka rawa a wani aiki na musamman a cikin na’ura da sauransu.
 3. Ka San Yadda Za Ka Warware Wata Matsala
  Dole za ka laƙanci yadda za ka rinƙa warware duk wata matsala da kan iya tasowa a cikin na’urarka. Ba kullum ba ne za ka rinƙa kai wa wajen wasu don su rinƙa warware matsalolin na’urarka ba. Ka rinƙa yawan tambaya da sanin matakan duk wani lamari da yadda yake gudana.
 4. Ka Koyi Tsare-Tsaren Na’ura
  Ka yi ƙoƙarin koyon tsare-tsaren na’ura ko kaɗan ne domin zai taimaka maka wajen fahimtar mece ce manhaja da yadda na’ura dungurungum take gudanar da ayyukanta.
 5. Ka Faɗaɗa Bincike
  Ka faɗaɗa bincikenka a harkar na’ura ta hanyar tambayar masana da kuma bibiyar shafukansu. Ka rinƙa shiga dandulan warware matsaloloin na’ura da sanin yadda ma’abota harkar suke gudanar da lamuransu, da kuma hanyoyin da ake bi wajen shawo kan wani lamari da kan iya tasowa.

Ko za ka karanta?

Mohiddeen Ahmad

Mohiddeen Ahmad

I am Muhammad Auwal Ahmad, an inquisitive student, tech aficionado, science enthusiast and a writer. I am the founder and CEO of Flowdiary.

4 Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *