5

Shawarwari 5 Don Laƙantar Tsaron Na’ura da Asusai

Duk wata daƙiƙa da ka ɓata a yanar gizo, to ba za a rasa wasu da suke haƙonka ba. Ko da ba za su samu komai a wurinka ba, burinsu bai wuce lalata maka tsaruka ba. Don haka a yau tsaron na’ura da yanar gizo ya kasance mai muhimmanci, amma wasu suna masa riƙon sakainar kashi.

Idan aka ƙwace maka asusu ba kai kaɗai matsalar za ta shafa ba, idan kai ba ka damu da kanka ba to ka yi tunanin wasu da matsalar za ta shafa. Sanin kanmu ne cewa kwanakin nan an faye yawan datse asusan mutane musamman na Facebook, har da na banki da sauran shafuka.

An yi ƙiyasin cewa a kullum ana datse dubunnan asusan mutane, tare da shafuka da manhajoji. To amma matsalar ta kafu ne kan cewa, amfani da tarin hikimomi ne ga madatsan ya janyo haka. Sai dai duk da haka, su ma masu asusan sunada hanyoyin da za su bi wajen ganin sun kaucewa kutse da ma’abotansa.

Ga shawarwari guda biyar kacal da na tanada ga wadanda suke ƙoƙarin kare asusansu, don jarraba su da fatan a samu dacewa.

  1. Kada ka rinƙa amfani da lambobin sirri masu sauki, ka yi amfani da masu tsauri wato kamar yadda masana suka umarta. Kada ka sa kwanan watan haihuwa, lambar waya ko wani sunanka ko sunan budurwarka. Akwai dalili mai ƙarfi da ya sa masana suka ce hakan, kai dai ka kiyaye kawai.
    Misali na lambobin tsaro masu tsauri:
    MoH&i)D(deEn%20+20*jp.J&a
  2. Kada ka ajiye lambar wayar da aka san ka da ita a matsayin lambar da ka saita asusunka da ita. Idan so samu ne kada ka bari wani ya taɓa sanin lambar ma ballantana ka yi rajista da ita a wani wuri.
  3. Ka da ka kasance mai amfani da lambobin tsaro iri ɗaya a ko ina, misali lambobin tsaron asusunka na Facebook ya kasance daban da na NPOWER, SMEDAN, Gmail da sauransu, sannan ka daina yawan rajista da shafuka ko manhajojin da ba ka san sahihancinsu ba, kuma ka yi hattara da bin likau!
  4. Ka saita two-factor authentication da logging notification, sannan kayi verifying identity naka.
  5. Ka da ka sake ka ba wa wani bayanan asusunka, kuma kayi hankali da adireshin email naka sosai.

Ko Za Ka Karanta?

Ka turawa abokanka da ‘yan uwanka don su ma su ankara.

Allah ya tsare mu, ameen.

Mohiddeen Ahmad

Mohiddeen Ahmad

I am Muhammad Auwal Ahmad, an inquisitive student, tech aficionado, science enthusiast and a writer. I am the founder and CEO of Flowdiary.