1

Me Ya Sa Kimiyya da Fasaha Suka Ci Gaba a Ƙasashen Yamma?

Idan ka kwantar da ranka kayi tunani da kyau za ka fahimci cewa akwai wasu dalilai da yasa kimiyya da fasaha suka ci gaba a duniya musamman a ƙasashen yamma. Sai dai dalilan a bayyane suke kuma kusan kowa ya san su, abun nunawa guda a nan shi ne “menene madogarar cigaban bunƙasa ilimi da binciken kimiyya da fasaha” bayan kuma mutane ne masanansu.

A yau duniyar kimiyya da fasaha sun yi ci-gaban da ya haura gaban mamaki domin wasu abubuwan da za ka ji ana samarwa da binciken da ake yi wajen gano wani abu dole sai dai kayi shiru don mamaki.

Amma menene dalilin haka?

A takaice kuma dalili guda daya shine “bincike.” Da bincike ake juya duniya, da shi ake canja duniya kuma da shi ake bunkasa komai.

Shekaru dari da suka wuce a baya babu ilimin yanar gizo, yau ga shi ta dalilinsa ka kan iya ganin mutumin da yake wata nahiyar kai tsaye, kawai taba jikinsa ne ba za ka iya ba. Shekaru dubu da suka wuce kafin ka kai wata kasa sai ka shafe tafiyar watanni, a yau za ka iya daga murya kayi magana kowa ya ji ka a fadin duniya; wannan shine manufar bature “making the world a global village” – saboda a ƙaramin kauye ne ko ihu kayi kowa sai ya ji.

A takaice, wato bincike a yau yayi sanadiyyar samuwar komai kuma yayi sanadiyyar gano wasu abubuwan da da Ɗan-Adam bai isa ya gano su ba.

Amma wane irin bincike tukunna?

Bincike ya rabu kashi-kashi kamar yadda masana suka kasabta, sai dai a takaicen-takaicewa za mu iya raba shi kasha biyu kacal:

  1. Binciken Kimiyya – wato a nan bincike ne ake yi domin gano wani abu. Misali ƙirƙirar wata mawarwarar sarƙaƙiyar lissafi daga tunani, gina nazariyya, fahimtar ko gano sabon wani abu da sauransu. Wannan ya jingina ne ga masana kimiyya da fasaha da duk wasu muƙarrabansu. A wannan bincike yau duniya ta ci gaba. Da wannan bincike aka iya samun ababen tafiye-tafiye, na’urori, aikin likitanci da sauransu. Irin wannan ilimin bincike shi ne wanda turawa suka duƙufa akai har suka zarcewa duniya.
    Amma me kake buƙata wajen yin irin wannan bincike?
    Lokaci, dama, tunani, karatu… shikenan!
  2. Binciken Nazari – wannan kuma bincike ne da ya shafi wurare da dama kamar binciken gano adadin yawan al’ummar Nigeria ko duniya, binciken gano wane irin taimako talaka yake buƙata, binciken gano yadda za a taimaki al’umma da cigaban su da dai sauransu. Irin wannan bincike masana harkokin siyasa, albarkatun ƙasa, falsafa, ƙididdiga, zamantakewa da sauransu suke yi. Kafin ka kai ga irin wannan bincike kana buƙatar karantar yadda lamarin yake da kuma yadda abubuwa zasu kasance.

Duk waɗannan nau’i na binciken yana bukatar ƙwarewa ko kaɗan ne domin aiwatar da shi. Kuma ina mai tabbatar maka da cewa da waɗannan irin binciken ne duniya take samun cigaba domin kuwa kullum masana suna boye suna gudanar da su.

Misali a binciken kimiyya wani mashahurin mutum ya kan iya ɗaukar nauyin masana ya zuba su a ɗakin binciken kimiyya domin duƙufa wajen binciko wani abu, kamar yadda marigayi Paul Allen yayi a cibiyar bincikensa ta Paul Allen Institute of Artificial Intelligence da kuma Paul Allen Institute of Brain Science, haka Elon Musk a Neuralink da sauransu. Da zaran an zuba waɗannan masana a ɗakunan bincike to za su duƙufa ne wajen tunani domin binciko yadda za su iya gudanar da wani abu.

Nayi bayani a cikin nazariyyata ta theory of the cosmic phenomena yadda idan mutum ya duƙufa a tunani to zai iya gano abubuwa da dama, bugu da ƙari kuma na ƙarfafa cewa duk wanda yayi tunani ya gano wani abu to daman can abun ya kasantu kawai lokacin gano shi ne bai yi ba. Sannan sai kuma yadda sabon wani abu yake zuwa wa mutum a cikin tunaninsa.

Mohiddeen Ahmad

I am Muhammad Auwal Ahmad, an inquisitive student, tech aficionado, science enthusiast and a writer. I am the founder and CEO of Flowdiary.

One Comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *