6

Yaya Yanayin Girman Ƙaunu Yake?

Duk wani abu mai girma, komin girmansa ko nauyi da mutum zai iya tunaninsa, to bai kai ko daya bisa dari daga cikin girman ƙaunu ba. Yanayin girman ƙaunu ya wuce duk wani tunanin mai tunani. Babu wani Ɗan-Adam da ya taɓa kimanta yadda girman ƙaunu yake walau a tunani ko a zahirance.

Har yau masana binciken lamuran ƙaunu, da duk wasu masana kimiyyar sararin samaniya da makamantansu, basu iya bada yadda girman ƙaunu yake ba, sai dai ƙiyascewa ta hanyar nazartar yadda girman abubuwan da ta ƙunsa suke.

Duk wani abunda mutum yake iya gani, da duk wasu duniyoyi da taurari da biliyoyin gungunansu, da girman sararin samaniya, da ƙasa da duk wani abunda ta ƙunsa duk suna cikin wani ƙaramin sashe ne na ƙaunu. A ƙalla dai ƙaunu ta kasance kamar wani teku ne inda mutum zai ɗebi ruwa a tafin hannunsa ya bar sauran, to haka ƙaunu take – duk wani abunda mu kan iya tunanin kasantuwarsa, ko ganinsa yana wani ƙaramin sashe ne na cikinta.

Masana sun haƙaito cewa ƙaunu ta samu ne sanadiyyar fashewar wata ƙwayar zarra da ba a san asalinta ba, shekaru a ƙalla biliyan 13 da ‘yan kai. Tun daga wannan lokaci, shi kanshi lokaci ya samu, haɗe da abubuwa, da kuzari. Wannan nazariyya ita ce ake ƙira Big Bang Theory.

Sannan ta ci gaba da cewa daga wannan lokaci komai ya rika samuwa a hankali a hankali daga ƙura ko tiriri, wanda shi ma ya samu ne ta dalilin tsananin zafin wannan fashewar ƙwayar zarrar. Har ila yau, nazariyyar Hubble ta ƙara nuna yadda ƙaunu ta ci gaba da faɗaɗa tun daga wannan lokacin.

Daga nan Ɗan-Adam ya fahimci cewa matukar ƙaunu tana ci gaba da faɗaɗa to babu ranar gano ƙarshenta, babu ranar gano wani abu da ke kusa da bangonta ko makamancinsa. Wannan yake ƙara nuna girman ƙaunu ya wuce misalin mai misali ko tunanin mai tunani.

Haka nan, masu hasashe sun haƙaito cewa wataƙila bayan wannan ƙaunun akwai wasu ƙaunuka, da kuma kasantuwar wasu halittu da suke rayuwa a cikinsu, wannan shi ake ƙira parallel universe da multiverse.

Ko da a hasashe ko tunani mutum ya kan iya kwatanta yadda girma da nauyin duniyar earth yake, ta wannnan hanyar kuma zai ƙara sanin ya yanayin girman tsarin hasken rana yake ballantana wani tauraro ko gungunsa.

  • Idan ka dauki yanayin girman duniyar earth za ka fahimci yadda ta kasance kamar wata ƙwayar zarra a cikin ƙaunu,
  • Haka nan girman tsarin hasken rana wanda ya dauki duniyoyi 8 da abubuwan da ke cikinsu, tare da basu damar zagaye rana da juyawa ba tare da samun tangarɗar bauɗewa daga matafiyarsu ba,
  • Sannan sai gungunan taurari waɗanda suka kasance biliyoyi a cikin ƙaunu,
  • Ga sauran abubuwan da suke a sararin samaniya masu matuƙar girma da nauyin gaske kamar blackhole, asteroid, comet, meteorite, da sauransu.

Rana, wacce ta kasance duniyoyi 8 ke zagayawa, ta ninka duniyar earth a girma sau 109, a nauyi kuma sau 333,000. Game da rayuwar taurari kuwa, suna shafe a ƙalla shekaru biliyan 10 suna rayuwa. Wanda ya kasance ƙarami daga cikinsu kuma shine wanda ya ninka rana sau 10 a girma. Cikin bincike aka iya gano mafi girman tauraro a ƙaunu shi ne UY Scuti, wanda ya ninka rana sau 1,700 a girma.

A gungun taurari ɗaya a kan samu biliyoyin taurari, kamar yadda ya kasance akwai taurari a ƙalla biliyan 100 a gungun taurari Milky Way. Haka nan local group ya kasance matattarar gungunan taurari, domin a local group daya a kan samu gungunan taurari kamar 50. Local group shine matattarar gungunan taurarin da ke kusa da juna, a inda akwai biliyoyin local group a ƙaunu, wanda mutum ya iya ganowa.

Ko da a iya nan muka tsaya, zamu iya fahimtar yadda girman ƙaunu yake ya wuce misali, sannan ya wuce duk inda muke tunani ko hasashe. Haƙiƙa sanin ƙaunu da abunda ta ƙunsa sai wanda ya halicce ta.

Madogara
Space.com
Livescience.com
Wikipedia.com
NASA

Mohiddeen Ahmad

Mohiddeen Ahmad

I am Muhammad Auwal Ahmad, an inquisitive student, tech aficionado, science enthusiast and a writer. I am the founder and CEO of Flowdiary.

6 Comments

  1. MashaAllah, gaskiya wannan rubutun an zuba ilmi sosai, na samu karuwa. Kuma ga zubin rubutun a bisa tsarin adabin Hausa daki-daki. Allah ya kara maka basira kuma ya karo mana irinsu a duniyar Hausawa. Mun gode sosai.

  2. INA FATAN WANNAN BINCIKE ANYISHI A MUSULUNCE saboda binciken turawa duk karya ne

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *