4

Me Solar System ta Ƙunsa?

Jerin duniyoyi a solar system

Solar System ita ce tsarin hasken rana, wacce ta ƙunshi duniyoyi 8 da sauran abubuwan da ke shawagi a sararin samaniya ciki har da duniyarmu earth. Ba cikakkun duniyoyi 8 da sauran ƙananan duniyoyi kawai ba ne a solar system, haƙiƙa akwai sauran abubuwan da ke shawagi a sararin samaniya da solar system ta ƙunsa.

A Solar System akwai duniyoyi, duwatsun da ke shawagi a sararin samaniya, watanni da sauransu. Solar System tana nan a tsakiyar gungun taurarinmu Milky Way, inda take iya zagaye shi duk bayan shekaru miliyan 230.

Me Solar System ta Ƙunsa?

Na farko: Duniyoyi

Inner Planets: Waɗannan sune duniyoyin da suke kusa da rana, sannan suke kusanci da juna.

  1. Mercury: duniyar mercury ita ce ta fi kusanci da rana, dan haka ita ce ta ɗaya a jerin duniyoyin solar system.
  2. Venus: duniyar venus kuma ita ce ta biyu bayan mercury. Tanada zafi sosai kasancewarta kusa da rana.
  3. Earth: duniya ta uku ita ce duniyarmu ta earth. Ita ce zafi da sanyi suke daidaita, ita ce duniyar da halittu masu rai suke rayuwa. Watanmu guda ɗaya da ke zagaye duniyarmu shine Moon.
  4. Mars: duniya ta gaba bayan Mercury, Venus, earth, sai Mars. Ita ce duniyar da masana kimiyya suke hasashen yiwuwar rayuwa a cikinta. Phobos ya kasance watan da masana kimiyya suke ji da shi sosai a duniyar Mars.

Outer Planets: Waɗannan kuma yawancinsu duniyoyi ne waɗanda suka samu kuma suka ginu akan sinadarin gas.

  1. Jupiter: duniya mafi girma a solar system. Jupiter tanada watanni kamar su Europa da Callisto.
  2. Saturn: duniyar da take ba wa mutane mamaki kasancewar wani zobenta da yayi mata ƙawanya. Tanada watanni irinsu Mimas, Dione, Titan da sauransu.
  3. Uranus: Haka nan duniyar Uranus ma tanada zobuna 11. Watannin da ke duniyar Uranus sun haɗa da Miranda, Titania da sauransu
  4. Neptune: duniya mafi nisa daga rana. Haka nan Neptune ma tanada watanni irinsu Triton da Proteus.

Wasu duniyoyin da ba a tabbatar da sahihancin zamansu a matsayin duniyoyi ba sun haɗa da Pluto, Phaeton da kuma Planet Nine. Sannan sai ƙananan duniyoyi da ake ƙira Dwarf Planets

Na biyu: Sauran abubuwan sararin


Sauran abubuwan da ke shawagi a sararin samaniya sun haɗa da asteroid, comet, meteorite, tauraron Ɗan-Adam da sauransu
  • Akwai dubunnai asteroid da ke shawagi a solar system
  • Haka nan masana sun ƙara tabbatar cewa akwai biliyoyin comet da meteor a solar system

Madogara
NASA
Space.com

Mohiddeen Ahmad

Mohiddeen Ahmad

I am Muhammad Auwal Ahmad, an inquisitive student, tech aficionado, science enthusiast and a writer. I am the founder and CEO of Flowdiary.

4 Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *