1

Me Za Ka Iya Sani Game da ‘Biometric’?

Biometric shine amfani da wasu sashina na jikin mutum don tabbatarwa; kamar yatsa, fuska, gashi, jini, murya, ƙwayoyin halitta da sauransu. Ana amfani da waɗannan sashinan don tabbatar cewa wannan mutumin shi ne wanda ake nema, ko kuwa don gujewa harkar bayan-fage da wasu mutane kan iya yi da sunan wani.

A wannan zamanin ana amfani da waɗannan sashinan na jikin mutum a fannin tsaro. Misali don tabbatar da cewa wanda ake nema ne ko wanda ya cancanta ne ya kamata ya shiga wani wuri, kamar buɗe manhaja, shiga wani wuri da sauransu.

Masanan da suka shahara a bangaren gano laifuka da kama masu shi, suna amfani da jini ko ƙwayoyin halitta ko wani sashe na jikin mutum don gano waye shi ɗin musamman idan har ya kasance ba a iya gane shi (watakila ko tashin bam ne ya tarwatsa shi, ko an cire wasu sassa a jikinshi) da dai makamantansu. Sannan suna amfani da waɗannan sashinan don gano wanda yayi kisan musamman idan ya kasance ya bar wani abu da za a iya gane shi.

Duk da wannan ƙoƙari da masana suke yi, sai ya kasance ana samun ƙwayoyin halittar wasu sukan iya zuwa ɗaya, musamman ‘yan tagwaye, ko kuma nau’in jininsu. Amma binciken masani Francis Galcon ya nuna cewa, a binciken shekaru ɗari na baya, babu wasu mutane biyu a faɗin duniya da zanen hannunsu ya zama ɗaya, ko da kuwa sun kasance ‘yan tagwaye ne. Wannan ya nuna cewa kowanne mutum a duniya da nashi irin zanen hannun wanda ba ya zama iri daya da na wani.

Saboda wannan dalili ya kasance a yau ake amfani da zanen hannu wajen tabbatarwa, musamman a bangaren da ya shafi tsaro da danginsa. Sannan na biyu ake amfani da murya, ko kuwa fuskar mutum ta hanyar nazartar ƙwayar idon mutum da na’ura za tayi.

Mohiddeen Ahmad

I am Muhammad Auwal Ahmad, an inquisitive student, tech aficionado, science enthusiast and a writer. I am the founder and CEO of Flowdiary.

One Comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *