
Kamar yadda ka san yarukan na’ura a matsayin programming languages, su suke ba wa na’ura mai ƙwaƙwalwa damar gudanar da ayyukanta bayan masana sun shigar mata da waɗannan tsare-tsaren mai cike da lissafi da haɗe-haɗen haruffa.
Masana yarukan na’ura a kullum suna kan ƙirƙirar manhajoji, shafuka, har ma da na’urori ta hanyar shigar wa na’ura tsare-tsaren. Dan haka a duk yawan waɗannan yarukan na’ura akwai wasu muhimmai da ya kamata ka koya a duk bayan wasu lokuta.
Ga wasu yarukan na’ura guda 6 da ya kamata ka koya a samuwar shekarar 2021:
Na farko: Python

A wannan zamanin, Python shine yaren na’uran da ya fi shahara a duniya saboda muhimmancinsa a wurare da dama da kuma taimakonsa wajen sarrafa fiƙirorin fasahohin zamani. Za ka iya amfani da Python don ƙirƙirar manhajoji, shafukan yanar gizo, bugu-da-kari kuma amfani da shi wajen sarrafa fiƙirorin fasahohin zamani kamar Artificial Intelligence, Machine Learning da Data Science da sauransu.
Za ka iya koyon Python a shafin LearnPython.org
Na biyu: R

R shine na biyu bayan Python a yarukan na’ura da aka fi bukatar amfani da su a sarrafa manyan fasahohin zamani irinsu Machine Learning da bangaren Data Science. Yanada saukin koyo da sarrafawa, yanada tsaro kuma yana aiki musamman wajen sarrafa bayanai da haduwa da rumbun bayanai. Za ka iya amfani da shi a na’urarka da ke kan gundarin-tsarin Windows, Ubuntu, Mac OS da sauransu.
Za ka iya koyon R a shafin TutorialsPoint.com
Na uku: PHP

PHP yaren na’ura ne da ake amfani da shi wajen ƙirƙirar shafukan yanar gizo. Yanada sauri sosai, saukin koyo da amfani, tsaro, sannan ba ya bayar da wahala wajen gudanarwa. PHP yana sahun gaba a jerin manyan yarukan da aka fi amfani da su wajen ƙirƙirar shafukan yanar gizo a duniya baki-daya. Sannan a watan da ya gabata na October 2020 ne aka sake sabunta shi (PHP 8), don tabbatar da tafiya da zamani da kuma biya wa masu amfani da shi bukata yadda ya dace.
Za ka iya koyon PHP a shafin W3Schools.com
Na hudu: JavaScript

A yanzu haka kasuwar masana yaren JavaScript ƙara ruruwa take a duniya, saboda yadda yakeda tsare-tsare da kuma ba wa mai amfani da shi damar sarrafa shi yadda yake so. Masana suna matukar kula da wannan yaren saboda bada gudummawa wajen kutse da bayar da tsaro da sauransu.
Za ka iya koyon JS a shafin JavaScript.info
Na biyar: Swift

Yaren na’ura Swift, duk da ma bai jima a duniya ba, mallakar kamfanin Apple, ya kasance yare mafi kyau da tsari da ake amfani da shi wajen ƙirƙirar manhajojin fasahohin ko ƙirƙirar kamfanin Apple kamar su iOS, Mac OS, tvOS da sauransu. An ƙaddamar da yaren a shekarar 2014, kuma ya zo da tsaruka na zamani da tsaro sannan bashida wahala wajen koyo ko sarrafawa.
Za ka iya koyon Swift a shafin CodeAcademy.com
Na shida: C#

Duk da mutane musamman sabbin ‘yan koyo ba su cika kula da yaren C# ba, amma yanada kyau ka daura damarar koyonshi saboda yanada tsare-tsare da wasu yarukan basuda shi. Za ka iya amfani da wannan yaren wajen ƙirƙirar shafi, manhajar na’ura da wayar hannu. Za ka iya amfani da shi wajen sarrafa fiƙirorin fasahohin zamani kamar su Virtual Reality da sauransu. Yanada sauri da tsaro, sannan ba a cika samun matsala da shi ba.
Za ka iya koyon C# a shafin: TutorialsTeacher.com
Thanks Oga… But naga babu JAVA haka na nufin Muyi Avoid dinsa? 😃