2

Asteroid ɗin Psyche 16 zai iya azurta kowa a duniyar Earth

Psyche 16

Garin dadi na nesa, ungulu ta leka masai…

Masana kimiyyar sararin samaniya suka ce akwai wani asteroid mai suna Psyche 16 da aka gano da jimawa, sai dai wani abun burgewa a tattare da wannan asteroid shine arzikin da ke tattare da shi.

Masana suka ce akwai zallar baƙin karfe da kwal da wasu sinadarai masu muhimmancin gaske a jikin wannan asteroid ɗin. Sannan aka ce yana tsakanin duniyar Mars da Jupiter.

An yi ƙiyasin cewa Psyche 16 zai kai dala tiriliyan dubu sau dubu dari, a kalla kusan $10,000 quardrillion. Masana sun haƙaito cewa da za a iya kawo shi duniyar earth, da kowane mutum daya a duniya sai ya zama biloniya.

Masana kimiyyar sararin samaniya da ke hukumar NASA suna shirin aika wa wannan asteroid Pysche 16 sako nan da shekarar 2022, sannan akwai yiwuwar ya isa a shekarar 2026. Wannan saƙo ne irin na masana wanda na’ura ce za ta binciki wannan asteroid sannan ta rinƙa aiko da saƙo.

Mohiddeen Ahmad

Mohiddeen Ahmad

I am Muhammad Auwal Ahmad, an inquisitive student, tech aficionado, science enthusiast and a writer. I am the founder and CEO of Flowdiary.

2 Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *