12

Ina ne Bangon Duniya?

Kasantuwar kaunu a tunani

Yawancin mutanen da suke riskar kimiyya cewa duniya daban, haka ma kaunu; suna shiga cikin tunanin yadda hakan kan iya faruwa, kuma ina ne karshen duniyar ko kuma kaunun.

Babban masanin kimiyya, Stephen Hawking, a cikin littafinsa “A Brief History of Time”, ya ce bayan wani masanin kimiyya ya gama bayar da darasi a wani babban taro, sai wata budurwa ta tashi ta ce, “duk abubuwan nan da ka fada karya ne, tayaya za ka ce wai duniya kamar kwallo take? Mu abunda muka sani shine duniyar a shimfide take kamar tabarma akan wani babban kunkuru.”

Farfesa Hawking ya ce, “masanin kimiyyar nan yayi murmushi ya tambaye ta, to idan akan kunkuru duniya take, shi kuma kunkurun akan me yake?” Wannan tambaya tasa duk mutanen da ke wurin suka shiga nazarin yadda wannan abu zai kasance.

Da kyau! Wato kamar haka lamarin yake; duk inda aka yi tunanin cewa duniya a shimfide take kamar tabarma to gano bangonta ba zai yi wuya ba, amma kimiyya ta iya gano wani abu guda:

A shekarar 1929 wani masanin kimiyya mai suna Edwin Hubble ya gabatar da wani kundinsa mai dauke da nazariyyar yadda duniya take fadada. Wannan ya samo asali ne tun samuwar kaunu, inda nazariyyar Big Bang ta ruwaito cewa kaunu ta samu ne ta hanyar fashewar wata ‘yan karamar kwaya.

Wannan nazariyyar masani Hubble ta nuna cewa tun daga samuwar kaunu shekaru biliyan 13 da suka shude kaunu ta ci gaba da fadada har zuwa wannan lokaci, kuma kullum tana ci gaba da fadada.

Kenan matukar kaunu tana ci gaba da fadada to babu lokacin da za a iya gano karshenta, musamman idan aka yi duba da yadda sararin samaniya take da fadi da kuma nisa. Wannan ya sa ko da biliyoyin gungunan taurarin da suke a sararin samaniya ba sa kusanci da juna, wannan ke nuna yanayin girman kaunu da Dan-Adam ba zai iya gano karshenta ba.

Mohiddeen Ahmad

Mohiddeen Ahmad

I am Muhammad Auwal Ahmad, an inquisitive student, tech aficionado, science enthusiast and a writer. I am the founder and CEO of Flowdiary.

12 Comments

 1. Amma kuma ance akwai bangon duniya a china?
  .
  Shin ko karya ne?

  • Idan kana magana a kan Great Wall of China ne, to wannan garu ne ba bangon duniya ba. An yi wannan garun/bangon ne saboda ya zama garkuwa ga mutanen yankin saboda farmakin makiya.

 2. Masha Allah, To amma Qur’ani ya nuna cewa Sama tamkar dai Rumfa ce,wacce zata iya kekkecewa saboda ma wani dalili misali:Inda Allah SWT yake cewa “Sama ta kusa kekkecewa saboda abin da suke fadi,kasa ma ta tsatssage….” a Suratul Kahfi. Tambaya ta a nan ita ce,Shin a kimiyyance ne ko har addinanance Universe bata da iyaka?

  Allah ya kara basira.

  • To Malam Habibu ingantacciyar amsa ita ce: a kimiyyance ne sama/kaunu ba ta da iyaka.

   Kasancewar abunda Dan-Adam ya iya ganowa ne, ka ga kenan iya ilimin mutum ya tsaya kan cewa kaunu ba ta da iyaka, saboda wadannan dalilaibda na kawo a sama. Amma shi fadin addini, musamman kamar yadda ka kawo madogarar inda ubangiji yake magana, na nuna yadda lamarin yake sai dai mu mutane mu iya samun sabanin fahimta a kai.

 3. Masha Allah, To amma Qur’ani ya nuna cewa Sama tamkar dai Rumfa ce,wacce zata iya kekkecewa saboda ma wani dalili misali:Inda Allah SWT yake cewa “Sama ta kusa kekkecewa saboda abin da suke fadi,kasa ma ta tsatssage….” a Suratul Maryam.
  Tambaya ta a nan ita ce,Shin a kimiyyance ne ko har addinanance Universe bata da iyaka?

  Allah ya kara basira.

 4. Alhamdu lillhi! Na gamsu sosai Malam,Allah ya kara hazaka. Muna godiya da ilmantar da mu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *