4

Ko Kasan Asalin Karfe ba a Duniyar Earth Yake ba?

A duk kwanan duniya binciken kimiyya yana kara fadada kuma masana suna kara kuzari kan binciko wani sabon lamari da Dan-Adam bai sanshi ba. A irin wadannan binciken muka iya sanin daga ina muka zo, yaya duniyar tamu ta samu da kuma hasashen abubuwan da zamu iya riska a nan gaba.

A yau binciken kimiyya ya iya gano cewa asalin karfe ba a wannan duniyar yake ba, ya zo ne daga sararin samaniya miliyoyin shekaru da suka gabata. A cikin wani rubutu, Me Yasa Muke Rayuwa a Duniyar Earth; mun fahimci yadda wannan duniyar tamu ta samu daga atisayen wasu sinadarai. Kawo yanzu, duk wani abu da muke iya ganinsa a wannan duniyar wadannan sinadarai ne suka samar da shi.

Imam Ja’afar al-Sadiq, malamin Jabir bin Haiyan (uban kimiyyar kyamistare) ya fadawa abokin muhawararsa, Abu Shakir, cewa asalin karfe ya zo ne daga sararin samaniya. A yau binciken kimiyya ya iya tabbatar da wannan lamari.

Haka nan ma’abota addinin musulunci sun yi imani cewa Allah ne da kanshi ya fadi wannan a cikin littafi mai tsarki, Al-Qur’ani.

Wasu lamura da Dan-Adam zai fahimta a wannan bincike shine: masana sun tabbatar cewa fashewar wani bijimin tauraro mai dauke da sinadarin karfe shi yayi sanadiyyar faruwar hakan bayan fadowa da yayi duniyar earth.

Shin idan irin wannan bijimin tauraro ya kara amai ya fashe nan gaba, zai iya fadowa wannan duniyar? Abun tambayar da ya ragewa masana kimiyya kenan.

Mohiddeen Ahmad

Mohiddeen Ahmad

I am Muhammad Auwal Ahmad, an inquisitive student, tech aficionado, science enthusiast and a writer. I am the founder and CEO of Flowdiary.

4 Comments

  1. Lallai na taba Karo da wannan ruwayar ta Imam Jafar Al-sadiq (As). Ba Qarya bane jikan Annabi (S) imam (As) Shine Uban Cemistry. Kakansa Imam Ali (As) kuwa shine Uban Technology din kanta.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *