4

Quantum Mechanics: Maganin Warware Duk Wani Hasashen Kimiyya (2)

ko quantum mechanics zai iya zama maganin warware duk wani hasashen kimiyya

Game da lamarin hada kwakwalwar mutum da na’ura kuma, har masana kimiyyar kwakwalwa basu san yadda nau’in bayanan da suke cikin kwakwalwa suke ba, basu san yanayin kankantar bayanan ba, haka basu san yanayin ganuwarsu a zahirance ba.

Sai dai masana bincike a cibiyar binciken da ke kokarin hada kwakwalwar mutum da na’ura wato Neuralink, suna matukar kokari wajen ganin sun samu damar fahimtar wadannan bayanan da kuma yadda zasu sarrafa su.

Ban sani ba ko wadannan masana bincike suna amfani da na’urorin wannan zamani, idan kuwa hakan ya tabbata da gaske to hakika hakan zai kasance babban kuskurensu. Na’urorinmu na yanzu da lambobin 1 da 0 kadai suke adana bayanai, amma sai dai bayanan da suke cikin kwakwalwar mutum ba da lambobin 1 da 0 aka adana su ba, haka ba da haruffan A ko B ba ne; watakila a nau’in ziri suke, ko kuma sun kasance mafi kankanta da ido ba zai iya ganinsu a zahirance ba. Don haka, na’urorinmu na yanzu ba zasu iya adana bayanan kwakwalwa a rumbun bayanansu ba, sai dai a nemo na’urorin da aka gina bisa gundarin kimiyyar quantum mechanics wato quantum computers.

Da kyau! Na hasasho cewa duk lokacin da wadannan masana bincike suka yi nasarar cimma wannan kudiri nasu, to hakika abu mai yiwuwa ne a iya binciko shaida daga idon mamaci kan wanda ya kashe shi. Wato da wannan dama za a iya gano wanda ya kashe wani ta hanyar nazartar idon mamacin, domin watakila mutumin da ya kalla a karshen rayuwarsa zai iya zama makashinsa.

Amma tayaya za mu iya binciko hakan?

Wannan lamarin ma na jingine shi ga maganin warware duk wani hasashen kimiyya wato quantum nechanics, idan aka yi duba da abunda na rubuta a sama cewa muna bukatar quantum computers don fahimtar bayanan da suke cikin kwakwalwa.

Wato da zaran an samu nasarar sauke bayanan kwakwalwar mamacin to za a iya ganin har wasu abubuwa da yayi kamar tattaunawa, ganin wani abu, a inda kuma za a iya ganin bayani da ya ta’allaka ko yake nuna cewa mamacin yana hakaita, “abokina yana kashe ni”, a inda za a iya fahimtar cewa abokinshi ne ya kashe shi.

Idan wannan hikimar za ta iya cin karo da hankali, to ayi tunanin yadda masana binciken kayan tarihi suke nazartar abubuwa, har da kwarangwal din mutum domin gano adadin shekarun da suka yi a doron kasa. Haka masana bincike kan gano makasa da aikinsu suke sabunta kwarangwal ta hanyar sake gina jinkinshi da turbaya da wasu sinadarai a matsayin naman jikinshi domin gano asalinsa.

Duk wadannan hanyoyin fa ana kirkiro su ne domin saukaka wani lamari mai sarkakiya ko wanda ba a san kansa ba

Mohiddeen Ahmad

I am Muhammad Auwal Ahmad, an inquisitive student, tech aficionado, science enthusiast and a writer. I am the founder and CEO of Flowdiary.

4 Comments

  1. MashaAllah gaskiya rubutunka akwai burgewan gaske cikinsu saboda dimbin ilmin da suka ƙunsa da kuma zurfin su. Ina gani dai Yakamata mu zama ɗalibanka a wata makaranta ko manazarta ta musamman da zai dinga sauƙaƙe mana abubuwan da muka karanta don mu fahimcesu. Sa’annan kuma ya amsa tambayoyin da muke dasu masu zurfi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *