3

Quantum Mechanics: Maganin Warware Duk Wani Hasashen Kimiyya (1)

kimiyyar quantum mechanics

A duniyar yau, duk lokacin da masana kimiyya suka gagara warware wani hasashen kimiyya sai a jingina lamarin ga kimiyyar quantum mechanics a matsayin maganin warware duk wani hasashen kimiyya. Hakan ya kasance ne saboda wasu lamura da har yanzu Dan-Adam bai iya ganowa ba.

A yanzu haka da manyan masana’antun fasaha suke kara kaimi wajen gina na’urorin zamani wadanda samfurinsu zai kasance a gundarin kimiyyar quantum mechanics, masana hangen nesa sun hasasho cewa nan da shekaru 50 masu zuwa wadannan na’urori zasu mamaye duniya, a inda kuma za a kusan daina amfani da na’urorinmu na yanzu.

Wato saboda wadannan na’urorin da aka gina a bisa gundarin kimiyyar quantum mechanics ne da kuma wasu fasahohin zamani kamar su Artificial Intelligence, Internet of Things da Robotics ya sa sabuwar fasahar sadarwa ta 5G ta kasantu. Hakika wannan ya kasance babban ci-gaba da duniyar zamani ta samu.

Game da lamarin time travel kuwa, wato hasashen kimiyya na tafiya don tsallaka wani karni ko zamani zuwa gaba ko baya, an yi imanin cewa quantum mechanics ne maganin da zai warware wannan hasashe a inda zai taimaka wajen kirkirar masarrafin wannan tafiyar wato time machine, wanda ake tunanin zai iya gudu kamar na haske. Ko da yake masani Albert Einstein ya ce babu wani abunda zai iya gudu kamar haske sai dai shi hasken kansa. Toh, mu dai ba mu san yiwuwarsa ko rashinta ba, watakila zirin haske ne zai dauki abu ya luluka da shi kamar saurin haske.

Wani hasashen kimiyya da ke bukatar ilimin quantum mechanics mai zurfi shine teleportation, wanda hasashe ne aka yi cewa mutum zai iya tafiya daga wani wuri zuwa wani ba tare da amfani da injinan tafiye-tafiye ba, ba kuma tare da bayyana a zahiri ko yin wani abu da zai nuna mutum yayi tafiya a zahirance ba. Misalin wannan tafiyar shine kamar musayar kayayyakin na’ura kamar su hoto, fayil, bidiyo daga wata na’urar zuwa wata cikin ‘yan dakiku.

A wannan matakin ma an ce ilimin quantum mechanics ne zai iya zahirantar da wannan hasashe. Sai dai ba mu sani ba ko wannan hasashe, ko kuma idan ma ya yiwu zahirance na nufin salwantar da rayuwar mutum ba ne, haka ba mu san yadda za a iya yin irin wannan tafiyar ba. Abunda muka nemi sani shine boyayyun lamuran cikinsa idan aka bayyanar da su.

To, yanzu mun gane cewa kusan duk wani hasashe na kimiyya ana jingina yiwuwarsa a zahirance ne ga wannan kimiyya ta quantum mechanics a matsayin mawarwara. Sannan dalilin anan guda daya ne, wato binciken masana tushen kaunu, wanzuwarta da kuma lamuranta, kan gano makasudin fashewar wannan matattarar-komai da fashewarta ya faru shekaru biliyan 13 da suka gabata kamar yadda nazariyyar Big Bang ta zayyana.

Manyan masanan suka ce quantum mechanics zai iya taka muhimmiyar rawa kan samuwar kaunu ko kuma dai ita kanta matattarar-komai din. Sai dai Farfesa Hawking ma shiru yayi; quantum mechanics ba zai iya samar da wani abu daga babu ba! Toh! Wannan babban lamari ne, abunda muke son sani kawai shine rawar da quantum mechanics yake takawa wajen warware kusan duk wani hasashen kimiyya.

Mohiddeen Ahmad

Mohiddeen Ahmad

I am Muhammad Auwal Ahmad, an inquisitive student, tech aficionado, science enthusiast and a writer. I am the founder and CEO of Flowdiary.

3 Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *