1

Abubuwa 5 Da Ya Kamata Ka Sani Game Da Kwakwalwa

Kwakwalwar mutum

Kwakwalwa ta kasance wani sashe ne na jikin halitta mai rai da ke ba ta damar tunani, ajiye bayanai da sarrafa duk wani sashi na jikin halittar cikin rabin-rabin dakika. Abu ne mai sauki ka iya fahimtar yadda halittu suke tafiyar da tsare-tsarensu bisa hikima, wannan na nuna yadda kwakwalwa take taka muhimmiyar rawa wajen duk wani lamari da halittar za ta yi.

Idan ka dauki misali da mutum, a nan manyan sashina na jikinsa guda biyu sune: zuciya da kwakwalwa; wadanda suka kasance manyan sashina ne da suka yi ruwa da tsaki wajen ganin mutum ya siffantu da surarsa ta mutum. Wato wadannan sashina sune sinadaran tafiyar da duk wani lamari na zahiri na Dan-Adam. Mutum ba ya iya yin komai face yayi tunaninda, haka zuciyarsa ta raya masa. Don haka kwakwalwa ba wai bayanai kadai take ajiye ba; akwai kai sakonni daga duk wani sashen jikin mutum zuwa gare ta – wadannan sakonnin kuwa sun hada da ji, dandano, gani, sauraro da sauransu.

Duk da haka akwai wadansu abubuwa masu ban al’ajabi game da kwakwalwa wanda ba kowa ya san da su ba. Wadannan abubuwa guda 5 ba kowa ba ne ya san su game da kwakwalwa musamman ma na lamba 3. Wadannan abubuwa sun ta’allaka ne kan kwakwalwar Dan-Adam a cikin halittu, kamar:

 1. Girma
  ko kasan yanayin girman kwakwalwar mutum? Ko kasan ma’ajiyar bayanan kwakwalwarka bashida iyaka? Ko kasan nauyin kwakwalwar mutum ya kai 1.5kg?
 2. Banbanci
  Kwakwalwar wani tana banbanta da ta wani a lokuta da dama. Misali kwakwalwar mace ta banbanta da ta namiji ta fuskar tazarar nauyi, amma hakan ba ya nuna fifikon fikira ko basira. Bayan wannan akwai banbancin girma tsakanin kwakwalwar mutum da ta dabba.
 3. Ziri
  Ko kasan kwakwalwa ma tanada ziri? Misali kamar yadda babu yadda mutum zai iya gani da idonsa face da zirin haske, wato zirin haske da ake kira “photons” ko “particles of light” su ke da alhakin nuna abu daga ido zuwa ga abun. Wannan ya nuna cewa matukar babu su a ido to hakika ba zai iya gani ba ko da ya kasance a bude. Haka ita ma kwakwalwa tana da nata zirin da ake cewa “brain waves”, sai dai wannan sun ta’allaka ne ga nemo bayanai kamar yadda nazariyyar lamuran kaunu (theory of cosmic phenomena) ta nuna.
 4. Taimako
  Hakika mun san cewa kwakwalwa tana taimakawa halittu sosai. To amma ita kwakwalwar wa yake taimaka mata ta fuskar gudanarwa? Misali zuciya ta kasance mai taimakawa kwakwalwa domin adana bayanai kamar yadda nazari da bincike ya nuna, sai dai ba kowanne masanin kimiyya ba ne ya yarda da hakan.
 5. Sauri
  Kwakwalwa tanada sauri matuka. Tana iya sarrafa bayanai a saurin da tafi kowace irin na’ura a duniya. Tana warware duk wata matsala a saurin da tafi kowace irin na’ura a duniya. Ko kasan kwakwalwa tana tunanin abubuwa sama da 70,000 a kullum?

Mohiddeen Ahmad

I am Muhammad Auwal Ahmad, an inquisitive student, tech aficionado, science enthusiast and a writer. I am the founder and CEO of Flowdiary.

One Comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *