2

Gungume Uku Gagara Dauri: Menene Blackhole, Whitehole da Wormhole?

Kai da ka ji an fadi wannan kalmar ka san karin magana ce wacce amsarta shine: kwai, saboda duba da cewa kwai uku ba su dauruwa ko da da igiyar zamani ballantana ta gargajiya. Amma fa duk da haka anan lamarin ya sha ban-ban saboda kai tsaye ba wannan amsar ko bayanin wannan rubutu ya kunsa ba.

Yanayin yadda suka wakana a cikin tunani su uku, kuma wasu lokutan suke kama da juna ko sabanin haka amma dai suna kamanni da juna ta fuskar suna ya sa na zaba musu wannan kirari: gungume uku gagara dauri. Shin yaya suke, menene su din kuma a ina suke?

Tuntuni mun jima da yin bayani kan menene blackhole da tsarinsa cikin rubuta na: mu leka blackhole, a nan muka gano menene shi din kuma a ina yake. Amma whitehole kuwa da wormhole wani ma bai taba jin sunayensu ba, watakila dan haka ya kan iya dauka ‘yan uwan blackhole ne amma bai san yadda zai fara tunanin yadda zasu kasance ba, dan haka ni kuma na dauki kudurin kawo bayaninsu su a takaice.

  1. Blackhole
    Blackhole ba komai ba ne illa wani sarari a cikin sararin samaniya da yake da tsananin karfin maganadiso da ba ya barin komai ya wuce ta kusa da shi har sai ya janyo shi, har haske ma bai tsira ba. Ana iya samun blackhole a gungun taurari kamar yadda mafi girma daga cikin wanda a yanzu aka gano shine wanda ya kai nauyin rana sau biliyan 40.

Karanta:
Mu leka blackhole 1
Mu leka blackhole 2

  1. Whitehole
    Shi kuma whitehole sabanin blackhole yake. Ya banbanta da blackhole saboda shi babu ma yadda za a iya shigarsa sabanin blackhole – duk da ma shi shiga cikinsa na nufin salwantar da rayuwa. A whitehole zirin haske kan iya ratsawa. Masana suka ce watakila duk abunda blackhole ya lakume to whitehole ya kan iya dawo da shi.
  2. Wormhole
    A cikin nazariyyar dangantaka ta masani Albert Einstein, ya so ace za a iya tafiya daga wani wuri zuwa wani wuri komin nisan da ake tsakani ba tare da gazawa ba, kawai kamar tsalle mutum zai yi sai dai ya ganshi a wurin da yake so. Wannan hasashe yana kama da hasashen kimiyya na time travel da kuma teleportation – inda aka ce ana so mutum ya kasance mai yin tafiya ne kamar yadda zirin haske yake yi.

Masana sun hadu kan cewa kusurwowin kaunu kan iya zama uku ne, idan aka hada da lokaci sun zama hudu: gaba ko baya, hagu ko dama, sama ko kasa. A nan sai aka ce to matukar wadannan sun hadu, lokaci ma ya kan iya zama na hudunsu bisa ga fahimtar nazariyyar Einstein, dan haka sai aka samu wuri da lokaci a matsayin kalma daya (space-time).

To domin sarrafa wadannan kusurwowi hade da lokaci, sai aka hakaito cewa watakila akwai wani abu wai shi wormhole da ya ta’allaka da wadannan abubuwa kuma ya wanzu bisa kaunun kanta, kamar dai yadda idan aka dora fallen littafi bisa kasa to zirin fallen kan iya zama wormhole dan haka nade shi kan iya zama hade wasu wurare biyu ko matso da su kusa.

Misali idan hakan ya yiwu to abu ne mai sauki ka iya tashi daga gidanka zuwa duniyar Mars cikin kankanin lokaci kamar wanda ka tashi daga dakinka zuwa kofar gidanka. Tirkashe! To hakan kuma ya kan iya yiwuwa? Masana suka ce babu wata shaida har yanzu da ke nuna tabbacin kasantuwar wormhole a fadin kaunu, ido bai taba ganinshi ba kuma haka hujjoji ba su tabbatar da shi ba. Kamar dai haka shi ma whitehole. Watakila binciken masana na gaba ya iya tabbatar da hakan ko kuma rashinsa.

Mohiddeen Ahmad

Mohiddeen Ahmad

I am Muhammad Auwal Ahmad, an inquisitive student, tech aficionado, science enthusiast and a writer. I am the founder and CEO of Flowdiary.

2 Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *