1

Yadda Za Ka Lissafa Sa’o’in da Suka yi Saura Rana ta Fadi

Idan ka fuskanci rana ta kusan faduwa kuma kana so ka lissafa sa’o’in da suka yi saura ta fadi, sai ka fuskance ta da kyau (ya kasance za ka iya hango mafadarta ko kadan ne, wato kada wani abu ya maka katanga tsakaninka da ganinta). A wannan lokaci sai ka mikar da tafin hannunka ya kasance yana fuskantar ka, a yayinda kuma bayan tafin hannun naka yana fuskantar inda ranar take. A wannan yanayi tafin hannun naka ba kare ranar zai yi ba, sai dai ka daidaita shi da saitin kasan inda ranar take.

Daga nan sai ka kara jona tafin hannunka na biyu kasa da inda hannunka na farko ya kasance (ka ga kenan hannunka na farko da na biyu suna jone da juna, ranar kuwa tana samansu). Idan hannunka na biyu ya yi saiti da mafadar rana wato daga kasa to shikenan za ka iya saukewa, sannan ka lissafa. Yadda abun yake shine: duk wani yatsanka guda da ya fuskanci rana yana nufin mintuna 15, idan ka hada yatsu hudu ka ga sa’a guda kenan. Idan hannuwa biyu ne kaga yatsu 8 a inda ka samu sa’o’i biyu kenan.

Za ka iya yi har da tafin hannuwa sama da biyu, ya dai danganta da inda ka saita tafin hannun naka daga inda ranar take zuwa mafadarta. Abunda za ka fahimta anan shine duk wani yatsanka guda daya (a cikin guda hudu da zasu fuskanci rana don ba a lissafawa da babban yatsa) to yana nufin mintuna 15 ne, ka ga yawan yatsun da ka sa sune adadin yawan mintunan da ya rage rana ta fadin.

Ana yin wannan lissafin ne lokacin da yamma ta yi misali bayan karfe 3 na yamma lokacin da rana ta doshi mafadarta.

Mohiddeen Ahmad

I am Muhammad Auwal Ahmad, an inquisitive student, tech aficionado, science enthusiast and a writer. I am the founder and CEO of Flowdiary.

One Comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *