0

Da Gaske Za Ka iya Hango Duniyar Venus?

Idan kuma ka ga rana tana faduwa ko bayan ta fadi da kamar mintuna 10 haka, a lokacin ne za ka iya ganin mafadarta tayi ja sosai. Sannan da sassafe lokacin da rana ke kokarin fitowa wato ta dillo kai tana fitowa haka za ka kara ganin mafitarta tayi ja sosai. Ko kasan a wadannan lokutan ne za ka iya ganin duniyar Venus da idanunka?

Wannan ja da kake gani lokacin faduwar rana ko fitowarta bangon duniyar Venus ne. Duniyar Venus tana daukan kwanaki 243 ne kafin ta gama juyawarta na kwana daya, ita kuma duniyarmu sa’o’i 24 ne jiyawarta, wato shine muke cewa kwana daya. A lokacin da duniyarmu ta kai tsakiyan juyawa wato misali karfe 6 na safe, to a lokacin ne ta dan gota ta yadda zamu iya hango duniyar Venus wacce daman a kusa da ita take.

Idan kuma ka taba tambayar kanka me yasa mafitar rana da mafadarta suke canjawa a lokuta da dama kamar damina, rani, bazara, kaka da sauransu. A duk wannan lokuta za ka fuskanci mafitar rana da mafadarta suna canjawa misali kamar gabas-maso-arewa, zuwa gabas sak, da kuma zuwa gabas-maso-kudu, haka nan ma mafadarta. Wannan ba komai ba ne face zagayen duniyarmu. Wato duniyarmu tana murginawa ko juyawa (rotation) a majuyinta kuma tana zagaya rana (revolution) a matafiyarta. Haka duk duniyoyin da suke a tsarin hasken ranarmu suke.

A duk lokacin da ka fuskanci canjin mafitar rana to hakan na nuna kara kusanci na duniyarmu a zagayenta ga rana, tunda tana zagaye rana a kwanaki 365 ne shine shekara guda.

Mohiddeen Ahmad

I am Muhammad Auwal Ahmad, an inquisitive student, tech aficionado, science enthusiast and a writer. I am the founder and CEO of Flowdiary.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *