5

Genetic Engineering: Kimiyyar Juya Kwayoyin Halitta

Wannan kimiyya ta juyin halitta mai suna “genetic engineering” ta na kokari ne wajen juya halittu ko sabunta su daga asalin yadda kwayoyin halittarsu suka kasance zuwa wasu daban, ko kuwa hada su da wasu daban don samar da wata halittar.

Anan halittu masu rai kan iya zama mutane, dabbobi ko tsirrai. Wannan kimiyya kuwa tana kokari ne wajen juya asalin kwayoyin halittar wadannan halittu domin samar da wata halitta a cikinsu ko daidaita wata.

Da wannan kimiyyar za a iya juya jinsin jariri kafin ya zama mutum, wato a lokacin da yake ciki bai fara chanja halittarsa zuwa kamannin Dan-Adam ba, sai a iya chanja jinsinsa daga namiji ya koma mace ko kuma daga mace ya koma namiji.

Har ila yau da wannan kimiyyar dai a kan iya hada kwayoyin halittar mutum da na wata dabba tare da rainonsu daga bisani kuwa a samu cikakkiyar halittar jinsi biyu, mutum da dabba – kenan mutum-dabba.

Mohiddeen Ahmad

I am Muhammad Auwal Ahmad, an inquisitive student, tech aficionado, science enthusiast and a writer. I am the founder and CEO of Flowdiary.

5 Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *