5

Rayuwa a Wata Duniya

Kamar yadda muke rayuwa a wannan duniyar tamu ya kasance wata ni’ima ce ta musamman da ba za mu iya ba wa kanmu ba face tsintar kanmu da muka yi a cikinta. Rayuwar da muke yi a wannan duniyar ta ba mu damar yin bincike game da wasu duniyoyin bayan tamu da kuma gano wasu halittu da abubuwan da suke samanmu da gefenmu. Hakika ilimin da muka samu ya tabbatar mana da cewa akwai wasu duniyoyi irin namu, sai dai babu wata hujja da take nuna cewa akwai wasu halittu makamantanmu da ke rayuwa a cikinsu.

Bayan gano wadannan duniyoyi sai Dan-Adam ya kudiri daura damarar yin bincike game da yiwuwar yin rayuwa a cikinsu; shin abu ne wanda zai iya yiwuwa ko kuwa ba zai yiwu ba? Idan har zai yiwu to kuwa zai shirya ne kwansa-da-kwarkwatarsa ya koma can ya ci gaba da rayuwa, watakila hakan zai iya zama babban ci-gaban da Dan-Adam ya samu a matsayinsa na masanin kimiyya kuma mai bincike.

Sai dai kuma wannan tunani har yanzu na zama mai narkewa ne a inda yiwuwar rayuwa a wasu duniyoyin kan iya zama barazana mai karfi, domin ba lallai bane Dan-Adam ya iya sanin duk abunda yake cikin wannan duniyar mai cutarwa da marar cutarwa ba tare da daukar lokaci wajen gudanar da binciken kwakwaf ba.

Har ila yau Dan-Adam ya iya gano cewa rayuwa a wasu duniyoyin ba ma barazana kawai za su kawo ba, har da duba yiwuwar kasantuwar mutum a cikinsu; shin hakan mai yiwuwa ne kuma zai iya dacewa da abunda mutum ya saba da shi a wannan duniyar ko a’a? A wanann hali Dan-Adam ya iya gano cewa wasu duniyoyin kamar Mercury da Venus ba za su zaunu ba, kuma ko da kusantarsu babu wani mahaluki da ya isa yayi saboda tsananin zafin da suke da shi kasancewarsu a kusa da rana.

Farkon duniyar da take kusa da rana ita ce Mercury, sai Venus, sai kuma ta uku ita ce duniyarmu wato Earth. Tazarar da take tsakanin kowace duniya ya haura kilomita miliyan 30 a inda tazarar da ke tsakanin rana da duniyar Mercury ya kai kilomita miliyan 57, haka tsakanin Mercury da Venus ya kai kilomita miliyan 49 kuma tsakanin Venus da Earth ya kai kilomita miliyan 40

Duniyoyi

Wannan al’amari ya sa Dan-Adam kara la’akari da cewa rayuwa a wadannan duniyoyi biyu da suke kusa da rana ba zai yiwu ba, dan haka sai masana suka kudiri niyyar nemo wata duniyar mafi kusa domin rayuwa a cikinta bayan wannan duniyar tamu da muke rayuwa a cikinta.

Fadada wannan bincike yasa masana suka gano cewa duniyar Mars wacce take kusa da mu ita ce mafi dacewar duniya da ta dace da rayuwa bayan duniyar Earth saboda wani bincike ya tabbatar sa samuwar danshin ruwa a duniyar, wanda hakan ke nuna cewa rayuwa za ta iya kasantuwa a duniyar.

Na’urorin hukumar NASA a duniyar Mars

Tambayar anan ita ce: shin tabbas duniyar Mars za ta dace da rayuwa dari-bisa-dari?

Eh, watakila. Wato binciken masana ya tabbatar cewa duniyar tana bukatar gyara sosai saboda wasu sinadarai masu cutarwa da kuma yanayin iskar da take duniyar ta sha banban da tamu.

Har ila yau, karfin maganadison duniyar bai kai namu ba saboda bincike ya nuna karfin maganadison duniyar Mars daidai yake da karfin maganadison da yake a duniyar Mercury. Sannan karfin maganadison da yake a duniyar wata kuma bai kai ka kowacce duniya ba, wato mutum ba zai iya tafiya a can ba sai dai da taimakon wasu sinadarai na daidaita karfin maganadiso.

Misali idan za a jefo abu daga saman benen da ke da tsawon mita 30 a duniyar earth, to abun zai shafe tsawon dakiku 3 ne kacal kafin ya iso kasa saboda lissafin maganadison da ke duniyar earth na 9.8m/s. Haka nan idan a duniyar Mars ne za a jefo abun to sai ya shafe dakiku 8 kafin ya iso kasa saboda lissafin maganadison da ke duniyar shi ne 3.7m/s. Haka nan idan a duniyar wata ne kuwa akwai yiwuwar abun ya shafe kimanin dakiku 18 kafin ya dira a kai.

Wannan dalilin ne yasa tauraron Dan-Adam ba ya samun damar fadowa, sai dai yayi ta shawagi kawai a sararin samaniya. Haka mutum ma idan ya je wannan wuri ba zai smau damar fadowa ba sai dai yayi ta shawagi a sararin samaniya.

Masana suka ce in dai akwai irin wannan matsalar a duniyar mars, abu ne mawuyaci a iya samun damar rayuwa a wannan wuri. Wasu suka ce da taimakon kimiyya da fasaha hakan zai iya yiwuwa ta yadda za a iya daidaita karfin maganadison wurin da kuma bincike kan sinadaran da suke wannan duniya da yanayin yadda mu’amalarsu da mutum za ta kasance.

Har yanzu dai masana suna ci gaba da bincike akan wannan kudiri na rayuwa a wata duniya.

Mohiddeen Ahmad

Mohiddeen Ahmad

I am Muhammad Auwal Ahmad, an inquisitive student, tech aficionado, science enthusiast and a writer. I am the founder and CEO of Flowdiary.

5 Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *