1

Da Gaske Akwai “Aliens”?

Hasashen siffar Aliens

Mutane da dama suna yawan tambayar shin ko da gaske akwai “aliens” kuma yaya suke da makamantansu saboda sun jima suna jin labaru game da su, dan haka wasu suka shiga shakkun shin da gaske akwai wadannan halittu; a ina suke kuma yaya suke?

Wato “aliens” wasu halittu ne da aka fara tunanin kasantuwarsu a kirkirarrun labarun kimiyya. Ta wannan hanyar ne ma’abota wannan rubutu suka ankarar da masana kimiyya domin a duba yiwuwar kasantuwar wadannan halittu. To daman ita kimiyya haka take; wato sai an yi tunanin wani abu kafin a gudanar da bincike a kansa. A cikin tunanin sai aka ce yanzu mutane da suke rayuwa a wannan duniyar ta earth wacce ta kasance ta uku tsarin hasken rana, shin mutum ba ya tunanin cewa watakila akwai wata duniya da wasu halittu suke rayuwa?

Wato yadda abun yake shine samuwar ruwa a wannan duniyar shi ya ba wa duk wata halitta damar rayuwa a cikinta sabanin yadda sauran duniyoyin da suke a tsarin hasken rana suka kasance.
Karanta: Meyasa muke rayuwa a duniyar earth?

Sannan a lamarin kimiyya kuma shine duk abunda ya faru a wani wuri to ya ta’allaka da faruwar wani abu a wani wuri da suke mabanbantan wuri da lokaci. Wannan shine abunda masanin kimiyya Einstein yake yiwa lakabi da “spooky action at a distance”, wanda shine dai abunda sauran masana suka kira da “quantum entanglement.” Har ila yau nima haka na gina nazariyya wacce take nuna hakan har ma take nuna cewar ilimi (ko wane irin bayani na duniya) ya kasantu ne tun bayan wanzuwar wannan duniyar kamar yadda lokaci, abu da kuzari suka kasantu. Na kira wannan nazariyyar tawa da suna “Cosmic Phenomena.” Har yanzu nazariyyar tana nuna cewa duk abunda wani zaiyi a wani wuri to sai dai ya kasance maimaici ne kawai.

To indai akwai wadannan nazariyyoyin a kimiyya to hakan yana kara nuna cewa ba zai yiwu ace mu kadai ne muke rayuwa a kaunu ba. Watakila akwai wasu a wata kaunun da suke rayuwa (parallel universe) – ko da ace ba kamar mu suke ba to zasu kasance wasu halittu ne daban. Sai wadannan marubutan suka samar da kalmar “aliens” tare da wasu kalmomi wadanda suka danganci juna.

Bayan duk wadannan sai masana kimiyya suka kara kaimi wajen bincike kan sanin hakikanin kasantuwar wadannan halittu da aka yi hasashen kasantuwarsu –shin a ina suke? kuma yaya suke?

Wadannan tambayoyi har yanzu babu wanda zai bayar da amsarsu domin babu wata hujja karara da ta nuna cewa wani masani ya taba cin karo da wadannan halittu a yayin bincike a sararin samaniya. Har tauraron Dan-Adam aka kirkira aka harba sararin samaniya domin farauto da nemo wata hujja ta bayani dangane da kasantuwar “aliens” a sararin samaniya.

Sai dai akwai wasu bayanai da suke nuna cewa “aliens” sun taba zuwa wannan duniyar har ma sun taba zuwa kauyen Dulali na karamar hukumar Darazo a jihar Bauchi tare da jirginsu. Haka wani bincike ma ya kara nuna cewa an taba ganin wani abu da ake kyautata zaton jirgin wadannan halittun ne a garin New Jersey na kasar Amurka a shekarar 1952. Wasu sun yarda da haka wasu kuwa ba su yarda ba.

Wannan bidiyon gidan jaridar Inquisitr.com ne suke da alhakin daura shi a tashar YouTube.

Mohiddeen Ahmad

I am Muhammad Auwal Ahmad, an inquisitive student, tech aficionado, science enthusiast and a writer. I am the founder and CEO of Flowdiary.

One Comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *