5

Dacewar Nazariyyar “Relativity” da Wannan Duniyar

Nazariyyar dangantaka

A shekarar 1905 fitaccen masanin kimiyyar nan Albert Einstein ya fara gabatar da shahararriyar nazariyyarsa ta “relativity” cikin wani aikinsa na kimiyya, kana daga bisani a shekarar 1915 ya ci gaba.

Farfesa Einstein a matsayinsa na shahararren masanin kimiyya da ya rayu a karni na 20 ya kirkiri wannan nazariyyar ne cikin tunani, kamar yadda wasu majiya suka ruwaito cewa farfesan yayi tunanin nazariyyar ne kamar a mafarki, da ya farka kuwa sai ya fadada bincike a kai a inda ya tabbatar da gaskiya ne.

Mececce nazariyyar “relativity”? Me take nuna mana kuma tayaya za ta taimake mu? Shin ta dace da mu a wannan duniyar?

Nazariyyar “relativity” wato dangantaka a takaice a ilimin kimiyya na nufin dangantakar wuri da lokaci. Nazariyyar ta nuna cewa wuri yana dacewa ne da lokaci, haka lokaci ma ba ya samun daidaito har sai ya dace da wuri. Wannan na nuna cewa ba ko ina ba ne a fadin kaunu inda lokaci yake tafiya kai-daya, wato ko wane wuri a fadin kaunu yanada nashi yanayin lokacin da yadda yake tafiya.

Farfesa Einstein a cikin wannan nazariyyar tasa ya samar da lissafin E = mc^2 wanda ya shahara matuka a duniya. Wannan lissafi na nuna daidaiton abu (matter) da kuzari (energy) idan har suna iya tafiya da saurin gudun haske (speed of light).

Lokacin da wannan masanin kimiyya ya gabatar da wannan nazariyya hakika ba ko wane masani ba ne ya yarda da ita. Amma farfesa Einstein ya kafa hujjoji da dama wajen gabatar da wannan nazariyya kamar nazariyyar Isaac Newton ta “gravitational force” wacce ke nuna karfin maganadiso yana ta’allaka da wuri. Misali, karfin maganadison wurin da kake daban yake da wanda yake a tsibirin Bermuda. Haka karfin maganadison wannan duniyar daban yake da na wata duniya. Sannan karfin maganadison ko ina a fadin kaunu shi ya ta’allaka yanayin tafiyar lokacin wurin.

Misali ka dauki karfin maganadison duniyarmu ta earth cewa 9.8m/s ne (ta yadda idan ka jefo abu daga kan benen da ke da tsawon mita 30, to abun zai shafe tsawon dakiku 3 ne kafin ya fado kasa). To amma fa ba a ko ina ba ne a fadin kaunu irin wannan zai faru. Watakila a wata duniyar sai abun ya shafe kimanin dakiku 20 kafin ya kai kasa, wani lokaci kuma ba zai kai haka ba.

Haka-zalika nazariyyar “relativity” ta ke nuna cewa wuri da lokaci sun ta’allaka da juna ne, dan haka kowane wuri akwai yanayin tafiyar lokacinsa.

Bayan mutuwar Albert Einstein masanin kimiyya Edward Teller a cikin bayaninsa na yiwuwar tafiya sararin samaniya ya ce, “watakila zuwan ‘Dan-Adam wata duniya a sararin samaniya kan iya daukarsa shafe shekaru a inda kuma lokacin kan iya banbanta a inda yake da kuma duniyar da ya bari” wannan ya nuna amintar masani Teller da nazariyyar “relativity” da kuma yadda za ta kawo sauki ga rayuwarmu a wata duniya.

A yau, da taimakon nazariyyar “relativity” mun iya gano cewa tafiya sararin samaniya sai da kyakkyawan shiri kan lissafin lokaci da yanayin wuri, haka a wannan duniyar tamu kuma banbancin lokaci da wuri kan faru ne sakamakon zagayen rana da kuma wanda duniyarmu ta ke yi.

Mohiddeen Ahmad

I am Muhammad Auwal Ahmad, an inquisitive student, tech aficionado, science enthusiast and a writer. I am the founder and CEO of Flowdiary.

5 Comments

  1. Tafiya zuwa sararin samaniya akwai sauki matuka idan har mutum zai ta cikin mafarkin Mohidden (My journey to centre of my milky way galaxy) Lol!!

    Allah ya saka da alkhairi

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *