10

Tarihin Duniya: Menene Babban Cigaba a Duniyar Kimiyya da Fasaha? (1)

Fasahohi

Duniyar kimiyya da ta kasance daban a cikin duniyoyi bisa ga la’akari da fannonin da take jagoranta, da kuma irin cigaban da ta kawo wa duniya tun farkon kasantuwarta ya sa har yanzu mutum ya ke tambayar shin wane babban cigaba ne duniyar kimiyya a samar zuwa yau a fadin duniya?

Hakika wannan babbar tambaya ce da ba kowa ba ne zai iya amsa ta kai tsaye komin shaharar mutum ko iliminsa, domin tambaya ce da ta shafi la’akari da tunani mai zurfi tun daga kasantuwar kimiyya har zuwa yau, tare da ta’arifin gano wane cigaba ne ya taimaki mutane, ko kuwa wane cigaba ne duniyar kimiyya ta samar da shi wanda da ana iya ganin ba zai yiwu ba. Tabbas sai masana sun yi zama tare da tunanin gano wadannan abubuwa da kan iya amsawa mutum wannan tambaya da yayi na cewa wane babban cigaba ne duniyar kimiyya da fasaha suka samar wanda har suke alfahari da shi.

Duk da haka, wato duk da wannan tambaya ta rataya ne a wuyan manyan masana, amma mu kanmu da muke kokarin koyi da wadannan duniyoyi na illimin kimiyya da fasaha hakika za mu iya zakulo wasu fannoni da cigaban da suka kawo wa duniya wadanda da mutumin da ya rayu shekaru dubu da suka gabata zai dawo duniya, da ba zai yarda da abunda yake gani a tattare da mu na cigaba ba.

A yanzu mu kan iya komawa tarihi domin mu nemo ilimin da ya samar da kimiyya da fasaha da kuma yadda aka yi suka wanzu har izuwa wannan lokaci. A zahirin gaskiya duk wani ilimi ko cigaba da ake nema wanda ya shafi duk wani fanni to fa sai an binciko tarihi da salsalarsa, matakansa da kuma wasu muhimman abubuwa a tattare da shi tun daga karnukan baya har zuwa lokacin da ake son yin amfani da shi. Dan haka komawa asalin tarihin kimiyya ko kadan (wato ko a takaice ne) zai ba mu damar gano ci-gaban da duniyoyin kimiyya da fasaha suka samar har zuwa yau.

Wato da farko masana tarihi da kimiyya sun nuna cewa wata ‘yar karamar kwaya ce kamar kwayar zarra ta samar da dukkanin kaunu. Wannan karamar aba da ta kumbura ta fashe ita ta yi sanadiyyar samuwar kaunu, a inda kuma har yanzun nan take ci gaba da fadada kanta; wato a takaice dai har yanzu kaunu tana kara fadadawa. Wannan ita ake kira da nazariyyar Big Bang wacce Georges Lamaitre ya gina ta a karni na 20.

Big Bang ta nuna yadda kaunu ta fara kasantuwa

Wasu masana kimiyya sun yarda da wannan nazariyya a inda wasu kuma ba su yarda ba, har sai da zamani ya zo bincike ya kara tabbatar da cewa hakika wannan shine abunda ya faru. Nazariyyar Big Bang ta ci gaba da cewa wannan abu ya faru ne kimanin shekaru biliyan 13 da suka shude. A tunaninka gano abunda ya faru shekaru biliyan 13 da suka shude tun kafin wata halitta ta wanzu a doron kasa zai iya zama babban cigaba a duniyar kimiyya? Biyo ni ka sha labari.

Bayan samuwar kaunu a inda ta kasance mai zafin gaske, sai kura ta fara wanzuwa tana yawo a ko ina, a nan lokaci (time), karfi (energy) da komai (matter) suka fara wanzuwa. Wadannan abubuwa da suka kasance jiga-jigan ginuwar kaunu sun ci gaba da fadada da kuma daidaita kansu a inda suka da ce da dokokin halitta ko dabi’a (laws of nature).

Daga wannan lokaci gungun taurari na farko ya samu da sauran abubuwan sararin samaniya (spatial objects), har suka yi sanadiyyar samuwar tsarin hasken rana (solar system) shekaru biliyan 4 da suka gabata.

Gungun taurari

Wannan tsarin hasken rana ya kasance mai daidaita kansa cikin fikira babu kuma kuskure ko daya a inda rana ta kasance a tsakiyar duniyoyi takwas zuwa tara ciki har da duniyar da muke rayuwa a cikinta wato earth, wacce a cikinta ne kawai halittu masu rai za su iya rayuwa.

Tsarin hasken rana

Na rubuta a shafin nan cikin wani rubutu “Nazariyyar Darwinism” cewa:
Samuwar mutum kuwa a wannan duniya a kalla kan iya kaiwa shekaru dubu 250 da suka gabata bayan wuce wasu matakan halittar mutum da suka hada daga homo habilis, homo erectus, homo sapiens da sauransu. A salsalar tarihi kuwa a kalla mutanen da sukayi rayuwa kamar mu sun shude ne shekaru dubu 100 ne baya.

Wadannan mutane suna iya yin farautar abinci da kansu sai dai basuda wasu kuzari da muke da shi yanzu kamar na yin magana da juna, fikira da kuma zunzurutun basira ko ilimi, sun dai kasance kawai suna rayuwa da namun daji ne a cikin dajin. Basuda basirar yin daki ko gida domin gudun dukan ruwa ko rana, sai dai su zauna a karkashin bishiya. Basuda tsoro domin komin girman naman dawa haka za su tare shi su kar shi ko kuma ya kar su, sannan basuda basirar dafa abinci haka suke cin shi danye.

Nazariyyar Darwinism kan halittar mutum

Bayan wani lokaci da suka fara chanja halitta tana komawa irin ta mutane, wato gashin jikkunansu ya fara zubewa, halittarsu ta fara juyawa tana komawa mai dan kyau, sai suka fara tunani da samarwa kansu mafita. Tarihi ya nuna cewa bayan wadannan sun shude sai aka fara samun wasu wadanda suka fisu haske da kuma kyau. Haka dai halittarsu ta ci gaba da juyawa tana kara chanja musu salon da zai dace da yanayinsu da kuma yankinsu.

Tarihi ya kara nuna cewa farkon wadannan halittu sun rayu ne a nahiyar Afirka kafin daga bisani su wanzu zuwa sauran nahiyoyin duniya domin dacewa da halittarsu da kuma yanayinsu, ciki har da sauran dabbobi da tsuntsaye. Wannan ita ce nazariyyar Darwinism ko kuma evolution wacce masanin kimiyyar halittu Charles Darwin ya gina a shekarar 1859.

Mohiddeen Ahmad

Mohiddeen Ahmad

I am Muhammad Auwal Ahmad, an inquisitive student, tech aficionado, science enthusiast and a writer. I am the founder and CEO of Flowdiary.

10 Comments

 1. Aduk time Dana karanta rubutunka Ina shiga matukar nazarin tayaya kasamu wasu ilmuka alhalin ka kasance Mai matsakaitan shekuru, tabbas mohiddeen akwai abubuwan Al ajabi a tattare dakai

  Ina maka fatan dacewa da Karin ilmuka masu albarka, wadanda zasu tallafi Al Uman musulmi baki daya.

 2. Salamu Alaikum, sannu da kokari, ina da yan tambayoyi game da nazariyyar Darwinism.

  1. Kaman yadda yazo a rubutun, nazariyyar Darwin ya nuna cewa karamar kwaya, kamar kwayar zarra ita ce ta samar da dukkanin kaunu a sanadiyyar fashewa, shin akwai wata nazariyyar kuma da zata iya bayyana abinda ya samar da wannan halitta ta kwayar zarra? Kuma a ina ita wannan halitta ta wanzu kafin ta fashe?

  2. Idan na fahimci karatun, lissafin lokaci ya fara ne bayan kwayar zarra ta fashe, wace irin fasaha aka yi amfani da ita da ta zama madogarar Darwin da sauran masana kimiyya akan lissafin Biliyoyin shekaru?

  3. Tarihi ya nuna cewa farkon halittu sun rayu ne a nahiyar Afirka kafin daga bisani su wanzu zuwa sauran nahiyoyin duniya domin dacewa da halittarsu da kuma yanayinsu, idan na fahimci wannan ma, hijira suka rika yi?

  • Madallah da wannan tambaya Malam Kabiru Muhammad.

   Wato amsar tambayarka ta farko har yanzu da nake wannan rubutun kimiyya ba ta iya gano makasudin wannan kwayar zarra ba. Babban masanin tarihin kaunu, halittarta da wanzuwarta (cosmology) wato Prof. Stephen Hawking har ya mutu amsar tambayar da bashida ita kenan, haka Richard Dawkins da aka yi musu irin wannan tambaya a gidan talabijin.

   Na biyu, kwarai lissafin lokaci (time), karfi (energy) da kuma komai (matter) ya fara ne daga wannan lokaci bayan fashewar wannan kwayar zarra.

   Tambaya ta farko da ta biyu ba nazariyyar Darwinism ba ce, nazariyyoyin halittae kaunu ce da makasudinta (cosmology) a inda na lissafo nazariyyar Big Bang a matsayin wanda ke da alhakin wannan bincike na fashewae kwayar zarra.

   Na uku, eh hijira suka yi daga domin dacewa da yanayi da kuma halittarsu kamar yadda tarihi ya nuna, kuma haka ma nazariyyar Darwinism din ta ce.

   Idan kanada karin tambayoyi za ka iya, kuma ina fatan ka ji dadin ziyartar wannan shafi. Na gode

 3. Yaune Rana na na farko na ziyarar wannan shafi Mai albarka, Kuma abinda nazo na tarar ya kayatar Dani, Ina fatan khairi ga marubucin, Allah Kara shiga lamuranka amin

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *