10

Me Za Ka Iya Sani Game da Tsibirin Shaidan?

Tekun Bermuda

Shekaru da dama tun daga yammacin turai, Amurka, Afirka da sauran sassan duniya wannan suna na tsibirin shaidan ya jima a bakunan mutane, kuma ba wai don gargajiya kawai ba, a’a sai dai don wani al’amari mai ban mamaki da ya faru a wannan lokaci. Bermuda Triangle wanda aka fi sani da tsibirin shaidan a gargajiyance wani tsibiri ne a kusa da kasar Mexico tsakanin Bermuda, Miami da Puerto Rico, inda wani teku ya kasance mai matukar abun al’ajabi da yake lakume jiragen sama idan sun zo giftawa ta samansa.

Jirage da dama sun jima suna bata a wannan yanki ba tare da sanin dalili ba sai daga bisani aka gano cewa akwai wani abunda yake da alhakin lakume wadannan jirage a wannan yanki. A wannan lokacin ne turawan wurin da kansu suka tsorata da lamarin a inda suka sanya masa suna da devil’s triangle wato tsibirin shaidan. Daga wannan lokaci kuwa masana suka dukufa wajen binciken kwakwaf kan gano abunda yake lakume wadannan jiragen; shin wata halitta ce wacce ba a san da ita ba, shaidanu ne ko kuwa menene a wanann wuri.

Bayan an gudanar da bincike na tsawon shekaru wanda fitattun masana kimiyya suna gudanar, sai aka gano cewa ba wata halitta ba ce a cikin wannan da take lakume wadannan jirage, ba kuma shaidanu ba ne suka kafa daula a wurin, binciken ya tabbatar da cewa kawai karfin maganadison tekun (gravitational force) shi ya ke janyo duk abunda ya so ketawa ta samansa. Bayan wasu lokuta kuwa sai aka kara tabbatar da cewa hakika wannan bincike bai ci karo da duk wasu ingantattun nazariyyoyin kimiyya ba sai ma kara tabbatar da su yayi kamar nazariyyar Albert Einstein ta Theory of Relativity da kuma ta Sir Isaac Newton ta Gravitational Force.

Hakika wannan bincike ya tabbatar da cewa tsananin karfin maganadison da ke tekun ne yake jangyo duk wani abunda ya so giftawa da samansa a inda kuma wadannan jiragen suke salwanta. Har ila yau, binciken ya kara gano wadannan jiragen da suka nutse a karkashin tekun shekaru sama da 20 a baya.

Mohiddeen Ahmad

Mohiddeen Ahmad

I am Muhammad Auwal Ahmad, an inquisitive student, tech aficionado, science enthusiast and a writer. I am the founder and CEO of Flowdiary.

10 Comments

  1. Abun burgewa!!!
    Wannan rubutun ya karamin basiran kan tsibirin shaidan
    Godia megida Muhideen

    • A’a ba ya iya tafiya, haka masana suka ce. Wasu kuwa suka ce ai zai iya saboda jirgin sama ne kawai wanda tsakaninsa da tekun akwai iska wacce ta ta’allaka ga karfin maganadison wajen

  2. Mun karu sosai,to amma ta yaya suke shiga karkashin gurin bayan karfin maganadiso dake gurin?

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *